Sashe 9
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka na koma kan achaban muka sake wata tafiyar ta minti ashirin sannan muka iso kofar gidan, na sauka na biya mai achaban na doshi gidan ina kallon yadda yanayinsa ya canja domin a can da gidan kasa ne gaba daya yanzu kuma na ga gaban gidan da wani bangare ginin bulo ne na zamani, sai dai ba ayi filista ba balle fenti. Na shiga cike da tsoro irin na bakunta waya sani ma mahaifiyarta tana nan ko ta rasu ko zan iya gane bangaren da take ba, wani gidan na fada na fada musu wanda nake nema.
“Inno Mamansu Hafsat wanda ta yi zama a Kano”
“Oh ga bangarensu can”
Matar mai goyon ta nuna min, sai na juya na nufi bangaren, na shiga da sallamata ina ta karewa bangaren Kallo.
“Wa'alaikissalam”
Muryar Hafsa na ji ta amsa ta juyo daga wankan da take yi ma yaro ta kalleni mamakin ganinta ya saka na tsaya cak domin a iya sanina ta yi aure irin auren da ake yi ma yarinyar tun bata gama makaranta ba a lokacin muma ss1 aka cireta aka mata aure, ita ma mamakin ganina ya saka ta tsaya a gurin kamar hoto.
“Uwani...”
Ta furta haka take kirana tun ina complain har na gaji na rika amsawa kasancewar ina da sunan mahaifiyarta ne. Da gudu ta iso gareni sai kuma ta ja ta tsaya tana kallon cikina.
“Allahu Akbar Uwani rai kan ga rai? Ashe Allah be kare ganawarmu ba”
Kallona take irin na canjawa da nayi nima ina mata kallon yadda ta yi rama ta kara baki kamar ba ita ba, a take hawaye ya cika idonta ta rungume ni tana murna tana kwalawa mahaifiyarta kira.
“Inna fito ga takwararki”
Inna ta fito da sauri tana kallona irin kallon nan na baka wayanci mutum ba, har sai da Hafsat ta yi mata bayani.
“Allahu Akbar yar nan? Allah sarki sannu da zuwa sannu da zuwa”
Kamar su hade haka suka rika murnar ganina.
A take aka yi min shimfida aka bani ruwa da filo ta cire kudi tace a siyo mata taliya da kifi ta daba min, abun ka da mutanen kauye masu karamci da kara kamin azahar har gidan ya cika da kwanon abinci, domin duk mutanen gidan da suka dafa abinci sai da suka kawo min suna ta min marhabun, har na rasa wane zan fara ci, Hafsat kam sai tambaya take idan akwai wani da nake so ta siyo min, mun sha hira duk da bana jin sakewa sosai amman a dole na washe damuwata ta ragu sai dai faduwar gabana be daina ba na halin da Hajiya da Mama za su shiga.
Can da hira ta yi dadi take fada min aurenta ya mutu, sam ban jidadi ba ganin tana da kurciyarta gashi har sun haihu biyu.
“Ni kam yi mamakin ganinki gida, amman ban dauka mutuwar aure ba ne, Hafsat miya faru?”
“Mi ya faru kuwa Uwani mazan yanzu mutunci ne da su, auren zamani ya zama abun da ya zama aure zai kara saboda arziki ya fara samuwa yana zuwa onisha kai kayan masarufi yana samun kudi sai maganar aure ya shirya ma Amarya daki ciki da falo a kusa da nawa ni kuma kin san daki daya da ni ko da yake baki taba zuwa ba, nawa dakin dai daya ne kuma indai har ga mutunci da adalci kamata yayi ya gyara min nawa ko kuma ni da ita duk ya gina mana sabon daki, daga na yi magana sai ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, daman gaba daya ya canja sai rawar kafa yake zai yi amarya, yan'uwansa suka hau zuga shi wai na cika mugun kishi daman mahaifiyarsa ce take so na domin ita ta hada auren yanzu kuma bata raye, daga yar magana nan sai ga saki abun haushi kuma ba saki daya ba har biyu ya karbi yaron sa babban wannan karamin ya kai wa yayarsa kawai ya bar min”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un wannan mutuwar auren har da ku?”
Na furta cike da bakin ciki.
“Hmmm ai auren yanzu idan kin yi dace ki gode Allah, ba kafi ba na dara ko'ina fama ake mazan ne kamar an kwashe na kwarai, yanzu kuma baka san inda zaka fada ba”
“Hafsat ba za a shirya ba? Tun da har ga yara?”
“Tun da ya sake ni har yau be tako kafarsa gidan nan ba, Baba Halilo har aikawa yayi nemansa amman bai zo ba, kuma yana zuwa cikin garin nan tun da yan'uwansa ai duk suna nan kalilan ne a Zaria, ďan da ya karbe ma yana nan garin hannun yayarsa, mazan yanzu ba su da mutunci Uwani, Allah yasa dai ke kin dace”
“Na dace sosai domin mijina irin mazan nan ne masu wuyar masu kuma na san har abada ba zan taba samun irinsa ba, amman na rasa Hafsa saboda ya rasu”
Ta daki kirji da karfi ta dora hannun saman kai.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Uwani Deen ya rasu?”
Na daga mata kai ina hawaye.
“Ashe kin san shi na aura”
“Eh Anty Samira ta fada min tace Zaharadeen kika aura”
Ta karasa ita ma hawaye na sauko mata.
“Wayyo Allah Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Sannu Uwani Allah ya masa Rahama”
“Ameen”
“Yaushe ya rasu?”
“Yau kwana goma sha uku”
Ta share hawayenta tana min kallon mamaki sai ta waiga ko'ina ta matso kusa da ni.
“Uwani? Takaba kika yi kika zo?”
Na daga mata kai sai ta rufe baki da sauri.
“Lafiya?”
“Ba lafiya ba ke ma kin san lafiya ba zata saka na bar gida na dawo nan a cikin yanayin da nake ba”
“Miya faru”
“Zan fada miki amman ba anan ba, kuma ba yanzu ba, dan Allah karki ba Inna ta san ina takaba kuma karki fadawa kowa abun da zan fada miki”
“Inshallah na miki alkawari babu wanda zai ji”
Ta yi shiru tana kallona can kuma ta ce.
“Yanzu babu wanda ya san kin zo nan?”
Na daga mata kai
“Amman hankalinsu ba zai tashi ba Uwani?”
Na yi masa da kai ina hawayen da su kadai suke iya fadar halin da nake ciki.
“Idan ban gudu ba, ba ni da wata mafita”
“Saboda me?”
“Saboda za a raba ni da abun da yake cikina”
“Kamar ya? Ban gane ba”
“Siyar na yi saboda rashin lafiyar Deen...”
Ban karasa ba ta saka hannunta ta rufe min baki tana kallon kofar dakin Inna.
“Bar maganar nan Uwani ba ri sai gobe mu yi ta, idan zan je mu je aikin gona sai mu tafi tare ai zaki iya ko?”
“Ba nisa bana iya tafiya mai nisa yanzu ban san miyasa ba”
“Cikin da kike da shi ne hala kin shiga watan haihuwarki ne?”
“Aa wata takwas ne da kwana sha shida yanzu”
“Kina kusa Allah ya sauke ki lafiya.”
“Ameen”
Na amsa ita kuma tana ta kallona cike da tausayawa.
ABIEY POV.
Kwanansa takwas a England suna buga wasa sannan ya dawo gida, a karo na hudu kenan da ya sauka a Masarautar be sauka gurin Ammy ba, daman ya kan kwatanta yin haka lokaci lokaci saboda Anty Amarya da kuma Mai Martaba da Ammy ta nuna masa yin hakan zai kara gyara alakar dake tsakaninsu.
Anty ta san da zancen dawowarsa hakan ya saka ta shirya masa abinci mai kyau ita da yayanta duk kuwa da ta san ba lallai ne ya ci ba, idan ma ya ci wani ba zai ci wani ba, but ta saba a duk lokacin da yayi tafiya kuma ta san da zancen dawowarsa tana shirya masa abinci da kayan tabawa, already yana da direban dake dauko shi daga airport hakan yasa be kira Anty ya fada mata ya sauka airport ba, sai ganinsa ta yi cikin falon Narjis tana tsaye daga gafensa tana murnar ganinsa shi kuma waya makkale a kunnensa yana fadawa Ammy isowarsa.
“Barka da zuwa mutanen turawa”
Ya yi murmushi yana sauke wayar.
“Anty”
“Na'am ďana ya hanya?”
“Alhamdulillah”
Sai ka fara wanka ko abinci zaka fara da shi.
“Food first”
Ya fada yana cire jacket din dake jikinsa kana ganinsa kasan damuwarsa ta dan ragu domin fuskarsa a sake take. Anty ta yi mamakin ganinsa a haka rabon da ta ganshi haka an dade, sai dai bata ce masa komai ba sai kallonsa take har ya iaa dinning din tare da kanwarsa ta fara bude masa abinci.
“Wannan ni na yi maka ni kadai”
“Bari na dandana hmmmmm hmmmm dadi”
Ya fada yana kara kai yayinda ya kai cake din a bakinsa. A dinning ya baje hajarsa ya ci ya koshi yayi nas sannan ya tashi yana jin cikinsa kamar zai fashe ya nufi dakinsa, kamin ya shiga ya ja ya tsaya jin kamar muryar Aisha tana dagawa saman ta Anty da alama wata gardamar suke, fasa shiga yayi dakinsa ya nufi kofar dakinsu su Aisha ya tura ya kofar ya tsaya daga bakin kofar yana kallonsu, Anty na tsaye Aisha na zaune fuskansu babu annuri a fuskokinsu.
“Lafiya....”
Ya tambaya har Aisha ta yunkuro zata fada masa sai Anty ta yi saurin dakatarta ita.
“Babu ruwanki a ciki, idan ke ba a isa da ke ba shi an isa da shi”
“What's going on here?”
“Aure za a mana ni da Narjis sun gaji da ganinmu a cikin gidan nan”
This time around abun dariya ya bashi domin murmushi yake mai sauti.
“As how”
“As ni an min miji”
“Ke ko Narjis”
“Ni din dai, wai be kamata ace za'ayi auren Narjis ni a bar ni ba, saboda haka ta hada ni da kanenta kamar ance mata na rasa miji ne, babu ranar da zan fita wani be gan ni yace yana so ba, ba za a min magana ace na fito da miji ba sai kawai ace ta hada ni wani kanenta kamar na yi kwantai yana da mata fa, ni a tsarina auren mai mata baya ciki, kuma na yi magana Anty tace zata ga laifi? Na rasa gane wane irin mulkin mallaka ake mana a gidan nan domin ba a banbanta mu da bayin cikin gidan nan ba”
“Anty you can't force her idan bata ra'ayi”
Abiey ya fada, sai Anty ta juyo ta kalleshi.