Sashe 55
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta hannu yayi mata nuna da kujera sai ta nufi kujerar ta zauna, Mai Martaba ya tattara dukan hankalinshi ya mika mata, daman haka yake indai Ammy na a guri Mai Martaba baya sauraren kowa sai ita.
“So nake ka duba, a cikin hukunci da ka saka ma Aliyu ka sausauta ma shi wasu, na san kana da iko akanshi na aiwatar da duk wani abu, amman akan duba masalahar abu”
“Maslahar ce na duba shiyasa na yanke wannan hukunci”
“Ranka ya dade a dai duba dai, Aliyu baya son yawo da kowa, ka san kuma babu ruwanshi da sarauta kuma kace zaka nada shi ina ganin haka kamar tawaya ne a gurinshi, sannan tun tasowar shi ya tashi da sha'awar kallon hakan yasa na bashi duk wani goyon baya har ya kai inda yake a yanzu, rana tsaka sai kace ya daina?”
Tana maganar Mai Martaba yana kallonta har ta kai aya sannan ya dora kafa daya kan daya.
“Na yi hakan ne saboda bana so, abun kunya ne ace ďan sarki ya taso yana buga kwallon wannan ba al'adarmu bace zamani ne ya canja mana wasu abubuwa kuma dole ta saka muka karbe su, yanzu kuma ina son ya daina umarni ne wannan”
Yayi shiru yana cigaba da kallonta damuwar dake tare da tsohuwar matarshi yake ta karanta.
“Nada shi a matsayin Galadima zai taimaka masa gurin shiga cikin harkokin Masarautar nan, zai canja mu'amalar shi da jama'a ko dan ya kiyaye janyo mana abun magana, sannan ina son ďana a kusa da ni...”
Ammy ta duba shi duba irin na mamaki.
“Yau kai da kanka kake fadar haka Mai Martaba?”
“Umaima ko na ki ko na so Abiey jini na ne, ko da ba jini na ba ne ba zan ki abun da ya fito a cikinki ba, balle kuma ace jinina ďana”
Idon Ammy ya cika da hawaye.
“Ka san da wannan amman kake kokarin hako abun da na dade da binnewa? Miyasa zaka ce na gurbata maka zuri'a a gaban shi? Har ka zo ya zo yana tambayar dalili? Kasan zafin da make ji? Ka san irin zuriyar da na yi kamin na gina rayuwar ďana? Na jure na jajirce kamin ya kai yanzu, saboda na san bashi da laifi, na raini ďana saboda kar ya tashi ace mashi shege...”
“Abiey ba shege ba ne yana da uba”
Ammy ta mike tsaye hawaye na zuba a idonta.
“Karka cilasta mashi abun da be saba ba, domin be girma a tare da kai ba, ba san abun da yake so da wanda baya so ba, kar neman kusancin ka da shi ya bata tsakanina da ďana...”
Tana kai wa nan ta juya ta nufi kofa.
“Babu wata dokar da zan canja, idan har Abiey be yarda da bin umarnina ba to sai dai ki canja mashi wani uban”
Juyowa ta yi ta kalleshi tana share hawaye ba tare da tace da shi komai ba ta fice, kamar yadda bata shiga bangaren Anty Amarya ba lokacin da zata shigo haka ta fita ba tare da leka apartment dinta ba, domin tana cikin damuwar da bata bukatar kowa ya ga fuskarta. Sai dai bata tsira ba domin ta tararda gidanta da wasu yan'uwa da suka ji abun da ya faru suka kira wayarta bata daga ba, musamman mukusanta sai dai zuwansu ya saka ta dan ji sakewar zuciya saboda hirar da aka sha, sai dai bata fada musu Abiey yana cikin gidan ba shi ma kuma be fito ba har dare azahar la'asar da magariba duk a cikin dakin yayi idan ya gama sai ya hau gadonshi ya kwanta.
After ya gama sallah isha'i ya hau saman gadonshi ya dauki wayarshi yayi trying number Mama, dazun ya samu number a bude amman ba a daga kiran ba daga baya aka kashe wayar sai ya aika mata da sako, a yanzu din ma wayar a akashe take, ajiyar zuciya ya sauke gaba daya bashi cikin natsuwa domin be san halin da Zahra take ciki ba, kuma be san inda take ba, zancen da Mai Martaba yayi mashi ba ya hana shi samun natsuwa, so yake ya san abun da Ammy ta aikata sai dai be san ta ina zai fara ba, baya son ya tambayeta ko ya matsa mata
Ammy ce ta turo kofar dakin ta shigo sai ya dan dago ya kalleta ya koma ya kwanta.
“Me za a hada maka? Baka ci komai ba tun safe”
“Bana jin yunwa”
Ya amsa, kusa da shi Ammy ta zauna tana kallonshi cikin damuwa.
“Aliyu kana cikin damuwa”
Ya tashi zaune.
“Ammy ai dole na damu kin san yadda na ke son Zahra, a yanzu da nake ganin na samu dama sai kuma Mai Martaba ya bullo min da wannan? Sannan yace ya saka date din aurena da Yasmin? Ammy bana son Yasmin ko kadan Wallahi”
“Amman baka tsanar ta ai”
“Eh bana tsanarta amman ba zan iya zaman aure da ita ba”
“Kuma kasan Mai Martaba ba zai canja kudinshi ba, tun farko kai ka daure kanka da kanka, dazun naje na yi magana da shi ko zai sauko sai ya nuna min idan har ba zaka iya bin umarninshi ba sai dai na nema maka wani uban, ni kuma bana son abun da zai shiga tsakaninka da Mai Martaba Aliyu bana son ku samu matsala”
“Kema kin goyi bayanshi kenan? Na hakura da Zahra kike nuna min”
“Aliyu Zahra ba numfashi ba ce da zaka ce idan ka rabu da ita mutuwa zaka yi, ba addini ba ce balle ka ce idan ka barta kafirta ka yi, ni din nan da na haife ka zan iya mutuwa kuma ka cigaba da rayuwarka balle Zahra da ta hadu da kai daga baya”
Ta yi shiru kamin ta sake kallonshi tace.
“Idan ka yi mata bayani ai zata fahimta, ta san kana son ta yanzu ma abubuwa ne suka zo ta hanyar da ba ayi zato ba you can talk to her, Sauban ya zo yana falo”
Ya mike tsaye ta nufi kofa sai ya daga kai ya kalleta.
“Yeah i did... Amman ba akan wannan maganar ba akan abun da kike boye min Zahra told me everything”
Cak Ammy ta tsaya ta juyo cikin matukar tashin hankali ya bugun gaba ta kalleshi, gaba daya sai jikinta ya dauki rawa a take mokoshinta ya bushe idanuwanta suka fiffito suka cika da kwalla kamar marar gaskiya Abiey kuma karantar abun da ta aikata yake a fuskarta daga zaunen da yake yana zuciyarshi na raya mishi abun da Ammy ta aikata ba karami ba ne. Kwakwaso kofar ďakin aka yi Sauban ya murda kofar ya leko Ammy ta juyo ta kalleshi hawaye na sauko mata sai kuma ya kalli Abiey dake zaune.
“I'm sorry... Ban san magana kuke ba daman Zahra ce ta zo”
Abiey ya mike tsaye da sauri.
“Zahra? Ina take?”
“Tana falo”
Sauban ya saki kofar ganin Ammy ta doso kofar da zimmar ficewa, sai ya kauce ta fito daga dakin tana share hawaye, Abiey yaje ya fito Sauban ya maida shi ciki ya shiga ya turo kofar ďakin.
“Taya zaka saka mahaifiyarka kuka Abiey? Kana da hankali?”
“Ba akan Zahra ba ne”
Abiey ya fada yana kokarin bude kofar ya fito, da saurinshi ya nufo downstairs zuciyarshi har wani fisga take ta hango masoyiyarta.
ZAHRA POV.
Bayan sallah la'asar Mama ta dawo daga gidan Hajiya tare da Yaya Maryam da Matar Kawu dukansu fuska babu annuri, Mama da Yaya Maryam ina kallonsu na san kuka suka yi musamman ma Mama da idonta har kumbura yayi, ina ta tambayar abun da ya faru kowa ya kasa amsa min sai hankalina ya tashi.
“Ko dai Baba ya mutu ne?”
Na tambaya ina kokarin fashewa da kuka domin hankalina a matukar tashe yake.
“Be mutu ba yana nan da ranshi, amman auren dake tsakanina da shi ya mutu”
Mama ta amsa min, hannu na do saman kai na rufe ido sai hawaye suka fara min sallama a saman fuska, auren mahaifiyata ya mutu saboda ni, bayan mutanen da na zan za su magana ita kanta mahaifiyar tawa ya zata ji? Idan ta kalleni ai ba zata iya mantawa ba, a ina zamu zauna yanzu? Gidan gadon su Mama da yan'uwanta suka maye suka zauna zamu raba ko kuma gidan gadon mahaifinmu da na aka siyar saboda neman kudin maganin aikin Deen? Ko kuma haya zamu kama mu zauna?
“Wannan abu dai be yi dadi ba, dukansu ba su yi tunani ba kamin aikatawa musamman shi mai son Zahra saboda Malam kamar uba ne a gurin ta komai yayi mashi ya kamata ya hakura, shi ma Malam be kamata yayi masshi cin mutunci ba ko dan kasancewar shi babban mutum, amman ya biye zuciya yana taya ďanshi kishi”
Matar Kawu ta fada, Mama dai bata ce komai ba, Yaya Maryam ta ce.
“Ni gani nake sila yake nema saboda ya fara canjawa tun daga lokacin da aka ce Deen ya aikata ba daidai ba kuma Zahra ta ga laifinshi, kenan goyon bayan ďanshi yake yana ganin kamar abun da ya aikata ba laifi ba ne kuma be kamata a ga laifinshi ba, Wallahi Abiey ma yana da hakuri da wani tuni ya aikata musu rashin mutunci”
Ni dai shiru nake bana iya cewa komai, domin a dalilina komai ya faru duk wanda za a ga laifinshi a bayana yake.
[11/5, 11:41 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣9️⃣
Muna zaune a gurin Surukar Mama Sa'adatu ta kawo min wayarta da na saka line na wai an turo min sako. Mama kallona kawai ta yi ta dauke kai na mika hannu na karba, ban san ta cire line a airplane mode ba domin na yi haka ne saboda kar ya sake kirana kamar yadda ya kira dazun.
“Zahra idan kin ga sakona ki kirani dan Allah ina son magana dake, Zahra idan ya wuce yau ban saka ki a ido ban yi magana da ke ba, zan saka a gano min inda kike”