Sashe 22
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ban masa komai, dan Allah ka fada min miya same shi? Me zai saka na yi ma masa wani abu?”
Na tambaya wani kuka mai karfi na zo mini, gaba daya jikina yayi sanyi gabana kuma sai faduwa yake.
“Babu.. Abun da ya same shi... da farko mun dauka ko matsalar daga rashin kyau nonon Jamila ne... Amman an gwada ba shi nonon wata wasu matan har biyu shi ma ya saka su ciwon ciki, kuma ana bashi madara ita ma tana ba shi matsala”
“Ban masa komai ba ka bincika nononta wata kila ba shi da kyau”
“Nononta lafiya kalau yake, kuma ba nononta kadai ke saka shi ciwon ciki ba, so ki fada tun wuri idan kin san da wata matsalar”
“Ban san da matsalar komai ba, da na sani da fada ko dan a ceto rayuwarsa”
Ya sauke ajiyar zuciya ina jin kamar akwai abun da yake boye min, sai ya sauke wayar ba tare da yace min komai ba, ni kam tuni hawaye suka wanke min fuska ina jin kamar ďana mutuwa zai yi a hannun wata wanda ba mahaifiyarsa ba. Fitowa na yi dakin na ajewa Mama wayarta na nufi dakin da nake kwana tana tambayar na gama waya da Hameeda kai kawai na iya daga mata na shige, ina shiga na maida kofar na rufe na kife saman katifa sai kuka, shi na kwana yi har safe daman ni da kuka mun dade da kullo abota tun a lokacin da Deen ya fara yin bakwana da duniya ban san wata rana sa zan ce farinciki ya rabe ni ba.
Ana gama sallah asuba Mama ta dora min ruwan zafi, daman can da zarar ta gama sallah azuba take dora min ruwa idan ya tafasa sai ta dama min kunu sannan ta zuba min na wanka. Sai da na fito daga wankan na sha nunu sannan na fito waje na aje kofin da na sha da shi da zimmar na hada sauran kayan na wanke.
“A a ban saka ki ba, tashi ki je ki kwanta jiya ba ki samu bachi ba”
Ya daga kai na kalleta mahaifiyata ce ko ban fada ba zata iya fahimtar halin da nake ciki domin idanuwa da fuskata sun nuna haka, sai dai na san bata son ta yi min maganar saboda Baba yana cikin gidan. Tashi na yi na koma dakina na kwanta sai kuma na ji katifar bata min dadi, na tashi zaune na ranka tagumi ina tunanin anya ban zalinci ďana ba? Da kuma ni kaina? Sai dai wata zuciyar kokarin nuna min take ba ni da laifi na aikata abun da na aikata ne saboda neman mafita, tashi na yi na fito waje na karbi wayar Mama na dawo dakin na kira number Dr Hamid be daga ba sai na ji wani zazzabi ya sauko min, gaba daya na rasa abun da ke min dadi. Na sake kira be daga ba sai na yanke shawarar kira Jamila kai tsaye domin zuciyata ta kwadaitu da son sanin halin da ďana yake ciki, kowane ringing daya tare da bugun zuciyata yake shiga, tsoro nake kar ta ki dauka ta dayan bangaren kuma ina fargabar abun da zan fada mata idan ta daga kiran.
“Ya aka yi?”
Jikina ya hau rawa na tsoronta can kuma sai na samu kaina da murmushi hawaye na sauko min sakamakon jin sautin kukan ďana da na yi yana fitowa daga cikin wayar.
“Ina jinki?”
Na kasa magana sai hannu na saka na dafe kirjina.
“Mtssssss”
Taja guntun tsaki zata yanke wayar sai na yi saurin dakatar da ita.
“Daman tambayar jikinsa zan yi”
“Shi wa?”
“Dana.....”
“Danki babu ko kunya babu tsoron Allah? Wato Dr fada miki abun da ya ke ko? To bari na gargade ki idan baki da hankali zan miki shi, daga yau sai yau karki kuskura kiran ďana da sunan ďanki, and daga karki sake kiran wayata sannan idan wani abu kika masa dake saka shi ciwon ciki idan ya kama nono to ki fada tun wuri, domin Wallahi zan iya shari'a dake akan ďana, idan wani abu ya same shi ba zan barwa Allah ba”
“Ban masa komai ba, ina rokon alfarmar ki dan Allah ki taimaka min ki rufa min asiri ki bari na ganshi ko sau daya ne”
“Baki da hankali Zahra”
“Ki kira ni da ko wane kalar suna, ki wulakanta ni yadda ranki yake so zan dauka saboda na ga....”
Na kasa karasawa saboda kar na furta kalmar ďana ranta ya bace.
“Danki... Dan Allah ki min wannan lamanin dan alfarmar da Allah yayi miki, ki taimaka ki cece rayuwata wata kila ba zan yi tsawon ran da zan sake saka shi a idona ba, waya sani ko nonon mahaifiyarsa yake so?”
“Dana ba shi da wata uwa sai ni, ki daina yin abu kamar kin fini sonsa kuma na fada miki tun wuri idan kin san wani abu kika masa ki fada tun wuri, daman can zuciyata bata natsu da baki shi da aka yi kika gani ba har na tsawon lokaci, Allah ya saukewa ďana ya sha nononki ko zai mutu ba zai taba shan nononki har abada...!”
Sai da na zabura a lokacin da ta yanke kiran, sai ya rumgume wayar ya runtse ido ina kuka marar sauti saboda kar Baba ya ji ni.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un.... ”
Na furta ina jin ina ma ban aikata ba, ashe haka ko wace uwa ke ji idan ďanta yana kuka hankali ya tashi matuka da jin kukan ďana da na yi, ina jin kamar na ruga naje agareshi a guje na bashi abun da yake bukata.
“Na cutar da kaina na cutar da jaririn da be san komai ba.... Na saka Hajiya ta yi zaton bata da jika... Na yi dalilin fitar jinin Deen a hannuna, na rasa Deen na rasa ďana wayyo Allah”
Wannan karon da da ihu ya ambaci Mahallincina ina jin kamar na yi hauka kuka na zo ta ko'ina Mama ta shigo ďakin da sauri.
“Lafiya?”
Sai na tashi da sauri na rumgume ta ina jin kamar ita ce zata min maganin matsalolina na fashe da wani sabon kuka wanda ya saka Baba shigowa yana tambayar ba'asi.
[10/10, 2:55 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2⃣4️⃣
*Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*
“Yarinyar nan tana cikin damuwa”
Shi ne abun da ya fito daga bakin Baba a tunanin Baba ina kuka ne saboda rashin Deen da baby kawai, Mama dai bata ce komai ba ta yi ta rarrashina har sai da na samu sukuni sannan ta fita ta bar ni a dakin ina ta faman sauke ajiyar zuciya, sai na yi kamar na dauki wayar na kira Dr Hamid sai kuma wata zuciyarta ta hana ni wata kila shi ma idan na kira ya fada min magana marar dadi ko ma ya rufe ni da fada kamar Jamila. Sai da Mama ta sallami Baba sannan ta shigo dakin ta tambaye ni abun da ya faru tun jiya har kawowa yau. Damuwa na gani karara a fuskarta wanda hakan ya saka hankali ya kara tashi.
“Mama mutuwa zai yi ko?”
Ta sauke ajiyar zuciya ta kalleni.
“Babu wanda ya san mutuwar wani sai Allah, ina tunanin na ce ki cire yaron nan a ranki, karki sake kiran wani daga cikinsu da sunan tambayar lafiyarsa, indai na isa na baki shawara ki ji”
Na daga mata kaina da ke min wani mugun ciwo sannan na lumshe idona na kwanta. Nan da nan bachi ya dauke ni ban farka ba sai da na ji muryar Yaya Maryam da kuma hayaniyar yaranta ita ta farkar da ni, na taso na fito waje na zauna kusa da ita sai ta kalleni tana murmushi.
“Ya jikin Zahra?”
“Alhamdulillah”
Na amsa da muryarta da bata fita sosai.
“Kin ci abinci?”
“Eh na sha koko da safe”
“Ga danwake na miki na san kina son shi”
Ban ce mata komai ba na kwantar da kaina jikin kafadarta sai na ji wani sanyi.
“Mama ta fada min abun da ya faru ki barwa Allah komai kin ji Zahra ki saka ma ikonsa da sarautarsa ido, yadda Allah ya so haka yake kasancewa”
Na daga mata kai, ina kallon yaranta dake wasa a tsakar gida gwanin sha'awa, sai gani ina murmushi a da can mi ba gwanar son yara bace amman daga daukar cikin nan da na yi zuwa haihuwa Allah ya saka min son Yaya sosai. Ban daga jikinta ba sai da aka kira sallah azahar sannan na daga ta tashi ta yi alwala ta dawo kusa da ni ta yi sallah ta dauko plate ta zuba min danwaken Husna ta dauko min spoon amman sai na samu kaina da kasa ci.
“Ki daure ko ci mana, idan kina zama da yunwa zaki jefa kanki cikin wani hali ne kawai sannan hakan yana nuna baki yardar da kaddarar da Allah ya dora miki ba”
“Ina jin tausayin yaron nan, ina jin tsoron hakkinsa da Allah zai tambaye ni”
Na dauki spoon na na debi ďan waken na kai bakina.
“Yau da safe Abiey ya zo gidanmu”
Kasa tauna ďan waken na yi na kalleta.
“Gurin me? Cewa yayi yana son magana da ni amman kamin yayi magana da ni sai da ya fara yi da Abban Husna”
“Maganar me?”
“Kawai dai ya tambaye ni ne damuwarki, yace ya gan ki asibiti jiya tare da wani likita, yana son ya san ko akwai wani abu da kike bukata ne”
Kamin na ce komai Mama dake daki ta ja tsaki ta ce.
“Abiey dai be san kunya ba, ni abun da yake a yanzu shi da yan'uwanshi har mamaki yake ba ni, kawai dai bana nuna musu komai ne saboda hali da tunani ba daya ba, kuma tun da har abun ya wuce kara a bar shi ya wuce kawai”