Sashe 50
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana da safa da marwa da a dakin hawaye na mata zirya sai aikin jijjiga Amir take dake kafadarta yana rusar kuka kamar zai mutu, tun kamin suna rabon shi da shan nonon Zahra, ranar da aka yi sunan ma ya wuni a wahale da ciwon ciki ga daukar da ya sha a gurin mutane, domin an yi taron da har bata iya gane wasu mutanen, an kashe dokiya kamar domin ranar aka tanade ta, ga kyaututuka da ta samu daga manyan mutane da matansu, kawayenta yan'uwan mijinta da kuma makota da abokan kasuwanci, Sunan mahaifin Mr Bashir yaron ya ci wato Ibrahim sai aka yi masa lakani da Amir, yaro ya samu soyayya ta ko'ina a gurin danginta ba ba a gurin dangin mahaifinshi ba sai ka rantse da Allah akan ta aka fara haihuwa kuma sai bne ďa na karshe da za a sake haihuwa a duniya. Sai dai da haka hankalinta ba a kwance yake ba saboda kukan da Amir na ciwon ciki, har yanzu cikinshi ka ki ya saba da noninta, balle kuma madara da ake kadawa na ba shi, duk wani abu da take ganin mafita ne ta gwada be yi ba, har nonon wasu matan an gwada bashi amman abun be karbe shi ba, yaron sai rama yake yana yawan kuka saboda ciwon ciki, ita kuma har ga Allah bata son sake waiwayar Zahra, duk kuwa da irin damun ta da Mr Bashir yake da tambayar Zahra, tun bayan da ta yi mashi karya cewar mahaifiyarta bata yarda ta yi aikin ba, da ya nemi sanin inda take kuma sai ta nuna mishi ita ba bata san inda Zahra take rayuwa ba, kuma matar da ta kawo mata ita ma bata sake zuwa ba, gashi ba su da number juna, sam bata yarda ta nuna mishi cewar Yayanta Dr Hamid ne ya kawo ta ba, hakan kuma be yi ma Mr Bashir dadi ba domin yayi niyar kyautata mata iya kar kyautatawa.
A razane ta juyo ta kalli kofar dakin da aka turo, wani mugun faduwa gabanta yayi a lokacin da ta yi arba da wata likitar dake tare da mijinta.
“Bismillah Dr Zainab”
Ta aje Amir a gadon da aka tanadar mashi na yara tana kallon mijinta kamar idonta zai fado.
“Sannu”
Dr Zainab ta ce da Jamila tsabar hankalinta baya gurin bata iya amsawa ba sai kallon mijinta take.
“Baka fada min zaka zo da likita ba”
“Wata kila idan na fada miki zaki kawo wata shawarar ne, idan na ce ki je asibiti ba zaki je ba yaro sai cutuwa yake, baki yarda kowa ya duba shi ba sai dan'uwanki kuma be zama lallai ya san komai ba domin komai da muhalinshi”
Ta hade yawun bakinta tana jin yadda makoshinta ya bushe kamar bata taba jika shi da yawu ba.
“Duk likita likita ne Hubby, bana son a matsawa yaron nan ne, ni kadai na san wahalar da na sha kamin na same shi ni kadai na san yadda nake jin yaron nan a raina, amman tun da ka matsa zan kai shi asibiti yanzu nan”
Ya kai hannunshi ya dafa ta domin ya lura da damuwar da matarshi take ciki ga hawaye har yanzu basu daina mata zuba ba, dazun na tausayin Amir ne yanzu kuma na tashin hankali ne da faduwar gaba wato tsoro.
“Ki kwantar da hankali wannan kwarariyar likita ce, Alhaji Habibu ne ya hada ni da ita kawai ki yi fatan Allah ya ba shi lafiya”
“Ameen Allah”
Ta fada tana kallon yadda Dr Zainab ta dago shi tana dubawa.
“Wannan ba abu ne da za'ayi a cikin gida ba, na san ku manya ba ku son kwantawa asibiti amman dole ne wannan saboda ayi wasu gwaje gwaje kuma mu gano daga ina matsalar take, domin mu bincike abun da yake yawan saka shi ciwon cikin kuma miyasa nonon mahaifiyarshi ma yake saka shi yin haka? Duk muna bukatar sani idan ta kama har nono zamu gwada”
“Ba matsala mu dai batan mu ya samu lafiya”
Dr Zainab ta maida yaron a inda yake kwance ta nufo Jamila dake tsaye.
“Idan ya sha nono yana amai? Kuma kina daukar awa nawa kamin ki bashi nonon?”
Amaimakon ta amsa sai kawai ta fashe da kuka ta fice daga dakin, Mr Bashir ya kalli Dr Zainab yana murmushin karfin hali ya ce.
“I'm sorry hankalinta duk ya tashi akan ciwon yaron nan, kuma ban fada mata zan zo da ke ba, domin bata son a taba yaron nan ko kadan lemme talk to her”
Dr ta mayar mashi da murmushin da ya bata sannan ya juya ya fice ita koma ta maida hankalinta gurin yaron.
[11/3, 7:43 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣6️⃣
Ya nufi kujera ya zauna ya aje wayar a gefe.
“Yaushe ka lalace har haka Aliyu? Akan me zaka saka a dauke tsohon mutane? Wannan abun ya zama hauka, baka san yana da ikon a kan Zahra a matsayinshi na aminin mahaifinta? Ko ka manta da mahaifiyarta yake aure? Wannan abun da ka aikata ya gyara abun ne ko kuma ya kara bata shi?”
“Ban yi da nufin komai ba, sai dan bata min rai da yayi, Ammy wannan abun yayi yawa ďan shi yayi shi kuma yanzu yace zai dora?”
“Kasan ba zaka iya ba ka fara? Akan me zaka dauki halin da ba naka ba ka ratayawa wuyanka? Wannan abun ya tashi daga soyayya kuma ya zama wani abun na dabam, domin gashi ya taba Martaba gidan nan ya taba kimarka ya taba kimar Mai Martaba domin dole za a ce ďanshi ne, da wans idon zaka kalleshi ma? Daman can ba jutuwa kuke samu ba balle kuma yanzu? Miyasa idan zaka yi abu baka tsayawa ka yi tunani?”
Ya tashi daga inda take zaune ya karso kusa da ita ya tsaya.
“Ammy ki saurareni dan Allah, ban saka a rushe gidansu yarinyar nan ba, me zai saka ma na yi mata haka, ni kawai na ce a dauki mutumen nan a yi masa horo so that ya san ba a bata mutane irin a zauna lafiya”
Ammy ta nuna shi da yatsa.
“Kai ka karya mashi dokar gida, saboda haka yana da ikon ya hukunta ko yace ka daina zuwa kofar gidanshi, arziki da sarauta da daukaka ba hauka ba ne, maganin kar ayi kar fara idan da baka je kofar gidanshi ba da be ganka ya wulakanta kaba”
“Ammy ba gurinta naje ba gurin Zahra...”
“Ya isa haka wai Zahra ce kadai mace a duniya da idan baka same ta ba zaka mutu a gwaro? Ina ce Mai Martaba ya tambaya maka Yasmin? Ko ka manta? Yanzu me zaka fadawa duniya? Zargin da aka fara yi a kanka zai iya fin haka ma, daman mutane kadan suke jira, ka kyale yarinya Aliyu bana son na sake jin sunanta a bakinka na gaji”
Kanshi ya sauke kasa yana jin wani yanayi marar dadi.
“Na ji na yi kuskure amman ba ni na saka a rusa gidan da suke ciki ba”
“To waya saka? Waya san ka dauke shi? Dole akwai mai bibiyarka, yanzu kuma an samu damar tun da ka bada kofa, daman be kamata kana zuwa gidansu yarinyar nan ba yaushe mijinta ya mutu? Da har zata fara kula wasu? Kuma macen da ta yi haihuwa? Allah kadai ya san abun da wasu jaridun za su buga nan gaba”
“Ammy ina son na yi magana da ita”
“Na fada maka ka dauke kafarka daga gurinta? Yanzu ba matsalar da ta faru nake kokarin solving ba? Shi zaka taka kafa kaje gidan? Mutanen unguwar su saks ganinka?”
“Ammy idan an rusa gidan da suke zaune ai dole na nema mata wani da za su zauna”
“Ba yanzu ba, ka bari mu gama da wannan matsalar tukuna”
Ammy na fadar haka ta kalli wayarta dake ringing.
“Mai Martaba...”
Abiey ya kalleta da sauri cikin matukar tashin hankali, sai da Ammya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa kiran ta kai kunnenta gabanta na faduwa.
“Assalamu Alaikum”
Tarar dakiku goma ya bada sannan ya amsa mata.
“Wa'alaikissalam ďanki yana kusa?”
“Eh yana kusa Mai Martaba”
“Ki turo min shi yanzu nan”
“Toh”
Ta amsa sannan ta sauke wayar idonta na duban Abiey.
“Mai Martaba yana nemanka, sai ka tanadi irin amsar da za ka ba bashi”
Kanshi ya daga sama ya sauke ajiyar zuciya.
“Karka yarda da amsa cewar ka saka a kama shi, amman ka fada mashi ka je kofar gidan idan ya tambaye ka dalili ka fada mishi cewar yarinyar da aka fasa aurenka da ita ce, ai ya san lokacin sai dai ace be santa ba”
“Amman Ammy mi zai saka na ce ba ni na sa aka kama Baban ba bayan kuma ni ne?”
“Idan ka amsa cewar kai ne, zai iya yarda kai ne ka rusa gidan, amman idan kofar gidan kawai ka je babu wata hujja dake nuna haka, kuma karka nuna mashi ka yi sa'insa da shi”
Ya daga mata kai alamar gamsuwa, kana ya cira kafa ya taka zuwa kofa, kamin ya fice kira ya sake shigowa wayarshi, da mamakin shigowar kiran ya janyo kofar falon ya rufe yana picking call din. Daga shi har ita aka rasa wanda zai ce fara magana, sai da ta kira shi take jin nauyin yi mashi magana, shi kuma ya gagara cewa komai jira yake ya ji abun da zai fara fitowa bakinta.
“Idan baki da abun fada zan kashe wayar i have something important to do”
“Na kira ne kawai na ji lafiyarka”