← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 127

Sashe 94

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai hannunsa na ji a fuska ya juyo da fuskar tawa yana kurawa bakina ido kamar idon nasa za su yi magana.

“Miya faru?”

Hannu na saka na dauke hannunsa kan fuskata.

“Jamila ce tace mu bar mata gidanta”

“Saboda me?”

Daki-daki na tsara masa abun da ya faru, kallona ya sake yi da murmushi a fuskarsa.

“Mijinta yake sonki ne?”

“Ina fa, kawai tana da karamin kai ne bata gane komai idonta rufewa yake”

“Idan ba sonki yake ba mi zai saka yayi haka a gabanta”

Na kalleshi.

“To ko so na yake?”

“Ke baki sani ba ya za'ayi wani ya sani? Amman ina ji miki tsoron ranar da zai gane gaskiya bana tunanin zai kyale ki, abun da nake ganin ya fi tun a yanzu ki yi aure inuwar aure zata baki kima da martaba, kuma kin ga ita kanta Jamila hankalinta zai kwanta dake kuma mijinta ma dole ya kyaleki”

Magana yayi min mai halshen damo, kamar ya idan ya gane gaskiya? Gaskiyar me?

“Ni ban shirya aure yanzu ba, yaushe aurena ya mutu da zan ce na yi wani, kuma ba ni da wani da zan iya aure a yanzu”

“Baki san musulunci ya yarda aurenki ya mutu da safe idan kin cika idda da rana a daura miki aure da dare ba? Musamman irin aurenki da haihuwa ce iddarki, karki damu da abun da mutane za su fada karki haramtawa kanki abun da Allah ya halal ta miki”

Shiru na yi ina kallonshi har yanzu mamakin furucinsa na dazun nake.

“Me kike tunanin ina zuwa yi gurinki? Me yake kawo ni? Kula dake right?”

Na daga kai.

“Bayan wannan zuciyarki bata raya miki wani abun ba? Miyasa yake kula da ni, wannan kulawar ta yi yawa”

“Ka ce saboda na rage damuwa”

“Yeah saboda ki rage damuwa amman ai ba kekai kike cikin damuwa ba, miyasa ban kula wasu ba sai ke? Akwai wadanda suka fiki shiga matsala”

“Miyasa ni kake kula ni?”

“Saboda ina sonki...”

Ya fada min kai tsaye murya kasa kasa yana matso da fuskarsa kusa da tawa.

“Sauban ni ce fa”

“Na sani, na dade ina jiran zuwan wannan ranar ranar da zan fada miki gaskiyar abun da yake zuciyata, Zahra na dade da kaunarki a cikin zuciyata, sai dai ba ni da wata damar nuna miki saboda hankali yana gurin Abiey a da na hakura dake saboda abokina, sai dai kaddara ba barku kun zauna da juna ba, na san Abiey zai iya yin sakarcin hakura dake ya barwa Deen da ban bari soyayyarku ta yi karfi ba, and now Deen ya mutu Ammy da Mai Martaba sun shiga tsakaninki da Abiey, and now ga wannan matsalar ta taso kina tunanin kina da wanda zaki aura sama da ni”

“Sauban ko wani abu ka sha? Kai fa abokin Abiey ne?”

“Idan ni abokin Abiey ne dai na haramtawa kaina abun da Allah ya halatta? Karki damu da idon da zan kalli abokina da su ko ya mu'amalarmu zata kasance, kamin na fara zuwa gurinki sai da na sanar da Abiey, after mun fara shakuwa da juna na sanar masa kudina saboda bama boyewa juna sirri ni da shi, kuma ya nuna min ya jidadin haka, har ya fada min zai fi kowa farinciki idan Zahra ta yarda da aureka, ko ba komai kusancimu zai karu kuma na san zaka rika ta tsakani da Allah”

“Wata kila ya fada maka haka ne, saboda yana kaunarka a matsayinsa na abokinka, baya son ya nuna maka damuwarsa ranka ya bace, amman na tabbatar Abiey yana so na, kuma dole zai ji kishi idan aka ce muna soyayya ma balle kuma ace na aure ka, ba zan iya haddasa masa bacikin ba, ba zan iya cin amanarsa ba”

Na fada hawaye na rige rigen sauko min, lallai na yarda dan'adam butulu ne yanzu duk amincin dake tsakanin Abiey da Sauban ace Sauban zai iya tunkarata kai tsaye ya fada min cewar yana kaunata wane irin so ne wannan da zai saka ka manta aminci da abotar dake tsakaninka da amininka ka murje ido ka aure budurwarsa.

“Ki tsaya ki yi tunani Zahra karki yanke hukunci cikin bacin rai, kuma ki duba halin da zan shiga idan kika amsa min da a'a”

“Babu wani hali da zaka shiga domin babu komai a zuciyarka sai tsantsar budulci, karka sake ganinka a kusa da ni, kuma kar ka sake kiran wayata ko ka bi a gurin da na bi, idan ka sake min wata maganar sai na sami Abiey da kaina na sanar da shi abun da kake shiryawa”

Na bude motar na fice a fusace, sai ya bude bangarensa ya fito.

“Kamin ki sanar da ni abun da kika shirya zan riga ki sanar da Mr Bashir abun da kika shirya ke da matarsa, sannan na sanar da Mahaifan Deen abun da kika boye musu”

Cak na tsaya gabana yayi dukan shida shida, na juyo a matukar firgice na kalleshi.

“Kin siyar da ďan cikinki saboda ki ceto rayuwar Deen, kin hada kai da matarsa da yayan matarsa kin mallaka masa ďanki a matsayin nasa, ya kike tunanin zai ji idan ya gane gaskiyar dan da yake alfahari da tutiya ba nasa ba ne? Wane irin hukunci kike tunanin zai yanke miki? Idan ma ya kyale ki yan jaridu da Mahaifan Deen za su saka miki ido ne? Kin ga daga lokacin kin bata sunanki da sunan danki kuma kin yankawa kanki tikitin zuwa gidan yari, wata kila ma zuciyar Mr Bashir ta buga ya mutu a daureki”

Na tako na dawo a inda yake tsaye hawaye na sauko min kamar ba gobe.

“A ina ka ji wannan?”

“A gurin wanda kuka nemi ta rufa muku asiri ta boye sirrin, wannan abun da kika aikata ya saka Abiey da Ammy da ita kanta Dr Zainab suna murna da yi ma Allah godiya da baki auri ďansu ba, idan kika san yadda Abiey ya tsane ki a yanzu saboda abun da kika aikata sai kin gode Allah da ya saka ba ku ganin juna a yanzu”

“Ba da son raina na aikata hakan ba, talauci ne ya saka ni haka”

“Yan jarida zaki yi ma wannan bayanin, rai ya fi rai ne da zaki da zaki siyar da ran da be miki komai ba, tun kamin ya zo duniya? An fada miki talauci hauka ne? Talauci ke saka rai fita daga jiki ne? Ko kuma kina tunanin arziki zai hana mutuwa aiwatar da aikinta ne? Da kika samu kudin kika biya ya tsaya ne? Sai kika yi biyu babu da ace kin yi tawakkali ki bar wa Allah komai da yanzu ba ki shiga wannan halin ba”

Ba ni da wata dabara sai ta kuka har numfashina yana kokarin fin karfina, cikin saldewar halshe na ce.

“Sauban baka da wannan kusanci da zaka nemi wargaza rayuwata ko da Mr Bashir akan abun da be kamata ya shafe ka”

“Da gaske? Baki san ina da kusanci da mutanen gidan ba? Ranar da na shiga cikin gidan na zauna a falo har na aika aka kiraki ba ki yi mamaki? Jamila yaya ce a gurin matar da nake aure a yanzu, ko Matata kadai na sanarwa zata iya ruguza komai naki, saboda haka ina baki shawarar ki yi tunanin abun da zai zame miki mafita tun wuri wanda zai fitar da dake daga taskon dana sani, kwana biyu na baki ki yi shawara”

“Ba zan aikata abun da kake bukata ba, ba zan yarda na yi butulci ba”

Na bashi amsa da kakkausar murya sannan na juya na nufi kofar gidan na shiga na bar shi a tsaye. Ina shiga daki sai an samu yancin yin kuka yadda raina yake so, ina nadamar abun da na aikata, gashi sanadin haka na jefa mahaifiyata cikin tashin hankali ni ma kuma na jefa kaina, har ana min bazarana da shi, a cikin kalaman da ya fada min ba wanda ta fi daga min hankali da saka ni bakinciki kamar cewar da yayi Abiey ya tsane ni saboda abun da na aikata.
Na yi zaton Sauban zai sauya shawara ya kyale ni amman sakon karta kwana na gani ya shigo a wayata da sunansa.

“Ki yi shawara da zuciyarki, karki yarda ko Mama ta san da wannan maganar, Wallahi Zahra kin ji na rantse miki da Allah ko? Son da nake miki zai iya sakawa na aikata komai a yanzu, fiye da abun da Deen ya aikata ya shiga tsakaninku da Abiey, kuma ina mai kara tabbatar miki kwana biyu na baki karki yarda ki bijirewa umarnina, idan ba haka ba zaki jefa kanki a babbar matsala”
Chapter 94 · 0% Book details