← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 127

Sashe 107

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na numfasa bayan na dire a linen da na yi masa karyar cewar na haifi cikin da Deen ya mutu ya bar ni da shi babu rai, sai dai ban boye masa cewar yana da ciwon hanta ba da kuma zancen aikin da aka yi masa haka ma na gano cewar shi ya shirya duk abun da ya faru tsakanina da Abiey ba da irin tsabanin da muka samu da Hajiya da Baba ta dalilin haka, har zuwa hana Abiey aurena da Ammy da Mai Martaba suka yi.
Na saka hannuna na share hawayena, ina jin wani abun kamar a lokacin yake faruwa. Sai ya koma jikin kujera ya zauna yana kallona.

“Akwai abun tausayi akwai abun dariya a labarinki, haka ma akwai abun takaici da bakinciki da bacin rai, sai dai kin rage wani abu daga cikin labarinki”

Na dago na kalleshi da idanuwan da hawaye suka ki tsaya min.

“Kin manta baki fada min cewar kin siyar da ďan da kika haifa saboda ki nemawa Deen kudin magani ba”

A razane na koma baya ina kamar wanda ta ga wani abun tsoro.

“Ni.... Ban siyar ba....”

“Kin siyar Zahra kin siyarwa Jamila da ďanki wanda ta yaudare ni da shi a matsayin ďana”

Ban san lokacin da na rufe baki na mike tsaye da sauri ina girgiza masa kai.

“Ba haka ba ne...”

Sai yayi murmushin da na tabbatar iyakarsa a fatar bakinsa yayi min alama da na zauna, amman na kasa zaman.

“Haka ne, Zahra na san gaskiya saboda na saka a yi min bincike akanki kuma jinin da na saka aka dauka na ki, Dr Zainab ta kawo min gwajin na farko wanda shi ne na gaskiya ba wanda Jamila da dan'uwanta suka bukaci a ba ni ba, Dr Zainab ta fada min gaskiyar wacece ke tun kamin ki ba ni wannan labarin, kuma na tabbatar da gaskiyar haka domin babu banbanci da abun da Dr ta fada min cewar kin yi soyayya da kanenta, kuma kin siyar da cikin ne saboda ki biya kudin aikin da za'ayi ma mijinki”

Na fadi gurfane a gabansa.

“A yanzu na gane dalilin Jamila na kin yarda kowa ya dubata tun tana da cikin har zuwa haihuwar da a nan ba so ayi ta ba, kuma ta ki yarda kowa ya duba yaron nan sai Dr Hamid, ina ta zargin wani abu amman ban zafafa gudun kar na yi zaton abun da ba shi ne ba”

Na hade hannayena guri daya na mika masa daga inda nake zauna.

“Kana da damar ka hukunta ni, ka dauki duk matakin da ya dace a kaina, ka yi kokari ace ka san gaskiya kuma zuba mana ido, daman Sauban yace zai fada maka gaskiya, yayi min barazana da wannan, a kokarina na rufawa kaina asiri na amince zan aureshi, shi ne albishir din da Hajiya Jamila take maka domin a yau za a daura aurena na uku da mutum da be dace da ni ba, kuma na san da cewar ka san wannan gaskiyar da ban amince masa ba, na amince ne saboda na rufawa kaina asiri saboda kar duniya ta ji kuma kae iyayen Deen su ji, kai ma kuma sani saboda ina tsoron abun da zai biyo baya, ashe ba zan tserewa tambayoyin yan jarida ba, ashe Hajiya zata hukunta ni, ashe kuka be kare min ba zan kunyata a idon duniya, kuma ďana zai yi Allah wadai da abun da na yi, kaico na ni Zahra”

Na karasa ina jin wani irin nadama da bakincikin kuskuren da na aikata, wani irin kuka ya ci karfina. Bakinsa ya cika da iska ya busar yana girgiza kai.

“Na jidadi da ya kasance ďan sunna ne Amir ba shege ba, hakan zai karfafa min guiwar rainonsa a matsayin ďana, duniya ta sheidi cewar Amir ďana ne, taya zan fito a idon na fadi cewar ďan da Jamila take ikirarin ta haifa min ba ďana ba ne? Ya za'a kalleni? Na san Amir ba jinina ba ne amman ina sonsa a haka saboda ban taba haihuwa ba, ina son na rike shi a matsayin ďana, na miki alkawari Zahra babu wanda zai san da wannan kar barazanar kowa ta daga miki hankali, na saka muku idone saboda na ga iya gudun ruwanku, kuma na kara karantarki, ina da security camera a ko'ina a gidana ba dan na rashin yarda da matata ba, sai dan taimakawa tsoro, hakan kuma ya taimaka min makura gaya wajen fahimtar wasu abubuwan, karki cilastawa kanki auren mutumen da baki ra'ayi saboda neman rufi asirin da ya dade a rufe, idan har akwai wanda ya dace dake a yanzu Zahra to ni, ko dan saboda ki rika ďanki kuma ya tashi a hannunki, kuma ina d yakinin ta dalilin zan iya samun farincikin da na gagara samu a baya, wata kila ke Alheri ce a gareni”

Sam sam sam ban fahimci inda kalamansa suka dosa ba, ba dan ban fahimci da yare da yake magana ba, sai dan rikicewar tunani domin abun da ya fi karfin kwakwalwa ya shiga cikinta, mikewa na yi tsaye ina rangaji kamar yar maye.

Ya kalli agogon dake falon.

“Lokacin Sallah yayi, amman kamin na tafi ina son na tambayeki shin baki son ki zama silar farincikin wani ne Zahra? Ba ki son ta dalilinki ni ma na samu magaji? Shin baki bukatar kasancewa da ďanki ne? Ki kira yan'uwanki sanar musu kar a daura auren saboda zaki yi shi ne akan cilastawa ba dan kina son shi ba”

Na saka hannayena na dafe kaina, wani abu nake ji mai kama da juwa kamar mafarki yake daukata, da sauri na juyo na fito daga falon ina takawa kafafuwana suna yin kamar ba za su dauke ni ba. Daker na iya jan kafafuwan na kawo kaina BQ, Mama da bakinta sai kallona suke kamin Mama ta fara tambayar

“Lafiya kike?”

Bana tunanin ina cikin hayyacin da zan iya amsa mata, sai faduwa na yi kan katifa na runtse ina jin bachi nake a yanzu ne zan farka daga mafarkin da nake. Tunawa da Sauban ya saka na bude na murza idon na tabbatar ba mafarki nake ba, kuma na nemi tsarin Allah daga sherin shedan kana na zabura da dan kuzarin da yayi min saura na nufi wayata na dauka na kwada nasa kira. Be daga ba na sake kiransa nan ma be daga ba sai na fita waje da sauri gurin Mama na mika mata wayar.

“Mama ki kira su Baba ki ce a dakatar da daurin auren nan dan Allah?”

“Ba lafiya ba, zan miki bayani daga baya, ki yi magana da su yanzu dan Allah”

“Ke Lafiyarki? Baki fada min komai ba zan kira waya na ce kar a daura aure?”

Ta zaunar da ni ganin yadda nake ta lilo kamar zan fadi sai haki nake irin na wanda ta yi gudun fanfalaki.

“Miya faru?”

“Bana son shi Mama bana son shi, daman cilasta ni yayi kuma yanzu na gane gaskiyar bana son shi”

“Zahra? Ni fa kwana biyun nan ban gane miki ba? Mi ke damunki”

Ganin zata bata min lokaci ya saka na kira Baban da kaina, sai dai na yi rashin sa'a shi ma be amsa kirana ba, na sake kiran dayan shi ma the same be daga ba, wata kila suna cikin masallaci. Wata Gwaggota na kira tana dagawa na ce

“Gwaggo Baba na kusa? Ki fada musu a fasa daurin auren nan, kar a daura dan Allah”

“Lafiya kike?”

“Akwai matsala, Gwaggo kar a daura”

Sai ta nemi na sadata da mahaifiyata, a take na mika mata wayar ta karba tana amsar mata da cewar ita ma bata san dalilina na fadar haka ba, amman tun da nace kar a daura to a haka kura kawai kar a daura. Gwaggo ta amsa mata da to, kanen mahaifiyata da suka zo suma suka hau buga waya wasu ba su daga ba, wadanda suka daga kuma aka sanar musu cewar a fasa daura auren saboda an samu wata matsala. Sai kashhhhh mun yi latti aikin gama ya gama lokaci ya kure mai afkuwa da afku, domin daya daga cikinsu ya sanar mana cewar an daura. Baya baya na yi na fadi zaune.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un...”

Shi ne abun da nake ta fada ina girgiza kai, hawaye na cin karfina.

“Miya faru Zahra? Ki yi min magana mana?”

Kasa magana na yi sai kuka na ke, na sake daga wayata cikin karfin hali na sake kiran wayar Sauban wannan karon ya amsa muryarsa radau.

“Hello Zahra kin kira wayar tana silent lafiya?”

“Ina son ganinka yanzu yanzun nan”

“Lafiya?”

“Ina son ganinka na ce”

Na daka masa tsawa da muryar da ban taba sanin ina da irinta ba.

“Okay gani nan zuwa”

Ina sauke wayar Mama ta rika hannuna ta shiga dani dayan dakin.

“Kin fi karfin awa hudu a bangaren Hajiya Jamila, yanzu kuma kin fito a cikin yanayin dake nuna ba ki cikin hayyacinki kina cewa a fasa daura aure miya faru?”

“Mama Sauban ya cilasta ni amincewa da aurensa ne, saboda yayi min barazana da siyar da cikin da na yi, zuwan da na yi a yanzu kuma Mr Bashir ya riga ya gane gaskiyar komai”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Chapter 107 · 0% Book details