← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 127

Sashe 27

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ashe ma kin san matar yayanki ce, matukar kina son girmama ďan'uwanki dole ni ki bi ni sau da kafa, ban san abun da kike son yi a bangare na ba, bayan kuma mijina yayi muku part din dabam saboda kun zama abokan zamana”

“Na shigo nan ne saboda na dauki ďana domin danginmu suna bukatar ganinsa kakaninsa da suka zo, sannan nan gidan ďan'uwana ne ina damar na zaga duk inda nake so a lokacin da nake so, ba uwa ba uba wa kika tunani zai rika mu bayan ďan'uwanmu?”

“Saboda na zama kishiryarki mana, shiyasa ba ki yarda ki tare a ko'ina ba sai gidan nan”

Ummiter ta karaso kusa da ita tana fadin.

“Kwarai da gaske, Yayana zai iya canja mata be canja yar'uwarba ina fatar kin san da wannan! A tunaninki mugun halinki zai hana mu zama a gidan ne? Kamar yadda ya hana sauran matan da yake aurowa zama? Kin dai tsira tun da kin haifo mana ďa ba dan haka ba da babu abun da zai hana ďan'uwanmu kara aure a karo na biyar”

“To sai ayi mu gani, matsalar haihuwar ai ba ni kadai ba ce har da ďan'uwanki, ke ma kuma ba ki wuce matsayin ba”

Hajiya Jamila ta fada cike da zafin rai sannan ta fice a fusace ta bar Ummiter a bedroom din, harara Ummiter ta bita da shi ta ja tsaki.

“Duk abun da kike so akaina ba zaki taba samu ba, ni ba irin Imaan ba ce da zan yi zuciya na bar miki gidan ba, nan da ke idan kika ga na bar shi to aure na yi”

Ta saka hannu tare Bismillah ta dauki jaririn tana murmushi.

“My sleeping handsome, da ama ace ba ta cikin wannan wicked matar ka fito ba, but hakan ba zai hana mu nuna maka kauna ba Habibi”

Tana fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa.

“Ni Wallahi ban so yaron nan ya dauko hasken matar nan ba, na so ace bakin mu ya dauko ayi baki mai kyau Allah yasa ka zama baki kamar ni”

Haka dai ta yi ta maganarta tana takawa a hankali gudun kar ya farka ta fice da shi.

*** *** ***

Tana shiga dakinta ya cire ďankwalin kanta ta wulgar da shi saman gado.

“Wannan yarinyar ko? Idan ban mata sanadi da gidan nan ba, ba zata bar ni na zauna lafiya ba, ta hana ni jindadin gidan mijina”

Ta nufi wayarta tana kai hannu ta dauka kenan sai ga wata gwaggon Mr Bashir ta shigo bakin har kunne tana mata barka, wani irin yauki take gwaggon bata fita ba Sister din Jamila ta shigo da wasu bakin, daman tun da ta haihu babu ranar da ba a zuwa yi mata barka daga bangarenta har zuwa bangaren mijinta, da kuma abokan arziki da makota wasu ma tun da ta haihu suka tare a gidan bayan sabin yan aikin uku da mijinta ya daukar mata, sai dai be yarda daya daga cikinsu ta taba masa yaro ba. A dole ta hakura da wayar da zata yi har sai da ta gama sallamar bakin sannan ta dauki wayar ta fita daga dakin zuwa can wani dakin da ba a shiga ta turo kofar ta shige bandaki sannan ta kira Dr Hamid.

“Yarinyar nan gani take tana iya wasa kada a tsakiyar ruwa?”

Ta fada bayan ta gama sauraren bayanin da Dr Hamid yayi mata na abun da Zahra ta shar'anta masa.

“Saboda tana ganin an zo nema a gurinta ne, mu kyale ta na kwana biyu idan ta ga ba mu sake yi mata magana ba zata tuntube mu”

Ya cije lips dinta tana jinjina lamarin.

“Ba zan taba yarda yarona shiga wannan kazamin gidan na su ba, shan nononta ma saboda ya zama dole ne, gashi mijina yace daga yau zuwa gobe idan ya sake jin kukan yaronsa da kanshi zai kai shi asibiti”

“Amman ban baki shawarar ki dauki yaron nan ki kai mata ta shayar da shi ba, zata ma iya guduwa, ko kuma ta samu damar aikata wani abu, kin san kuma ba ke kadai ce a matsala ba har da ni”

“Ko da wasa ba zan yarda a fitar da shi ba tare da ni ba, domin hakan zai janyo min matsala kuma dole wata rana asirina zai tonu”

“To ya zamu yi yanzu?”

“Ka fada mata zata dawo ta zauna a gidana ta cigaba da rainon ďana har zuwa lokacin da zai samu lafiya”

“Hakan zai kara tona asirinmu ne, saboda mutane za su fara lura wata kila m iyayenta ba za su yarda ta dawo ta zauna a nan ba, kuma a nan yau da gobe dole gaskiya zata fito”

“Ba zan taba bari a gane ba, kuma ita ma dole ta yi taka tsantsan domin ta san har da tata rayuwar tana cikin matsala, Dr Hamid yaron yana nufin komai na rayuwata ka fi kowa sanin yadda na sha wahala kamin na samu yaron nan, da asirina ya tonu a yanzu kara na rasa igiyar auren dake tsakanina da Mr Bashir, idan kuwa har zan iya yarda na rasa igiyar aurena ka san yaron nan yana nufin rayuwata ne ina nufin rayuwata gaba daya!”

“Kaina wannan abun ya saka ni a cikin matsala, ban taba aikata ko da zubar da ciki ba balle wannan! Idan gaskiya ta bayyana da wani ido zan kalli mijinki? Kuma sunana zai bace i think auren yarinyar nan zan yi idan ba haka ba zai zama kamar na kashe maciji ne ban tsare kan ba”

“Kama ganin haka zai zame mana mafita?”

“Shi kadai ne mafita”

“Karka aureta, ni na san wata mafitar amman a yanzu ina son ta zauna a tare da ni a gidana, zata dawo da zamanta a nan ne gaba daya har zuwa lokacin da ďana zai samu lafiya”

“Zan yi magana da ita”

Ta sauke wayar tana kashe ido.

“Kina wasa da rayuwarki, baki san Wacece Jamila ba, ke dai na taimaki rayuwarki yanzu kuma kina son wasa da damarki, hmmm yaro be san wuta ba sai ya taka, da na rasa igiyar aure ko ďana sai dai ke ki rasa farincikinki ko ma rayuwarki gaba daya”

ZAHRA POV.

Sai da na fara share ďakin da nake kwana na kwashe sannan fara share waje, kamar daga sama na ji sallamar Anty sai na dago na kalli kofar shigowa cikin gidanmu. Na kuwa can ka daidai domin Anty ce tare da yaranta biyu Aisha da Narjis ban amsa sallamar ba kuma ban fasa sharar da nake ba, sai na yi kamar ban san da shigowarsu cikin gidan ba.

“Zahra shara ake yi?”

Na dago na kalleta kamar na amsa kiran sunan da ta yi sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin kazafin da Abiey yayi ma Deen a yanzu ya saka na kara tsanar Abiey ba shi ka dai ba har da yan'uwansa da duk wani da yake da alaka da shi. Mama ce ta tashi tana mata maraba daman can Mama bata iya fushi ba ko da ka bata mata rai zata iya nuna maka ta huce sai dai ta bar abun a zuciyata, amman a gurin wasu a gurin yayanta kam kamar ni da Yaya Maryam idan muka bata mata rai a take muke sani domin fushi take da mu mai tsanani kamar bata san inda muka fito ba, musamman ma ni da take cewa na fi kowa rashin jin magana. Mama ta dauko tabarma ta shimfida musu ni kam ko inda suke ban sake kallo ba.

“Zahra ko baki gane ni ba?”

“Na gane ki mana Anty, ai ba zan manta fuskarki ba, da kuma dalilin da ya saka na san ki ba”

Ta yi murmushi.

“A yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zo ki zauna mu ba bakin zafi ba ne gaisuwa muka zo”

Kamar na musa mata sai kuma na aje tsintsiyar hannuna na nufi inda take na zauna.

“Zahra kin dauki zafi da yawa, kuma kina da yancin nuna bacin ranki amman a rika sassautawa, kuma abun da ya wuce ayi hakuri a bar shi a matsayin abun da ya wuce”

“Har abada abun da Abiey yayi min ba zai taba wuce ba, kuma ba zan taba mantawa ba, kuma ba zan fasa rokon Allah ya saka min ba”

Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, sai kuma ta juya gurin Mama ta yi mata gaisuwar sannan ta dora da cewa.

“Muna tare da Abiey yana waje yana son ya shigo yayi muku gaisuwa idan da hali”

“Ya shigo mana, bari na dauko mayafina”

Mama ta tashi ta shiga daki ta dauko mayafi ta rufe jikinta, ni kam daman da hijabi nake zama a yanzu saboda Mama tace ba a son mai jego na sakin jikinta any how. Sam ban jidadi da Mama ta amsa kai tsaye tace ya shigo ba, sai dai ba zan iya hanawa ba. Anty ta kalli yarta ta ce

“Narjis je ki ce ma Yayanki ya shigo”

Ina jin haka na tashi na shige dakin Mama na zauna zuciyata na wani irin tafasa, sallamar ma shi ma da naji sai da na ji kamar na saka reza na yanke kunnuwana, ga wani matsifafen turare daya saka da ke ta tsokata ta har cikin dakin Mama da nake zauna.

“Mama Zahra fa...?”

Ya tambaya bayan ya gama yi ma Mama gaisuwa, wani kololon bakinciki ne na ji ya taso min ya tsaya min a kirji, har sai da na sauke numfashi sannan na samu sukuni.

“Zahra.... Zahra...”

Mama ta kara ni har sau biyu ba ta yi na uku ba na amsa na taso na fito, zaune yake kusa da Anty ya sadda kanshi kasa yana motsa keys din hannunsa a hankali. Zaunawa na yi kasancewar tabarmar irin mai fadin nan ce da zata wadaci mutum biyar ko fiye ma, ya dago ya kalleni da wasu mayun idanuwanshi dake kara saka ina jin haushinsa.

“Zahra ya hakuri?”

“Baka ji kunya ba Abiey? Kai da kanka zaka tako ka iso har cikin gidanmu da sunan gaisuwa?”

Ya sauke kansa kasa yana murmushi.

“Subhanallahi ya kike magana kamar ba musulma ba”

Na kalli wanda ta yi maganar.
Chapter 27 · 0% Book details