← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 127

Sashe 64

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karon ma be cigaba ba sai da ya sake kamin lomar tuwo a bakina, sannan ya dauki kofi ya bude ruwan roba ya zuba ya dauka da hannunshi ya kai min a baki na sha kadan ya aje ya sake daukar spoons din ya cigaba da ba ni abincin da na tabbatar da be yi feeding dina ba ba zan iya ci ba.

“Ban san wani abu na rayuwarki ba bayan wannan, wace rayuwa kika yi kamin yanzu asalinki wacece ke ban sani ba, kuma ina bukatar sani amman kamin nan na san ina daya daga cikin mutunanen da suka saka zuciyarki ta buga ko kuma suka hanaki farinciki a baya bayan nan wanda hakan ya haifar miki da damuwa”

Na kalleshi cikin yanayin damuwa yake min maganar yana cigaba da ba ni abinci.

“A lokacin da Jamila ta kira ji cikin tashin hankali tana fada min cewar gani nan kin fadi a kasa kin suma, hankalina ya tashi sosai na fada mata ta saka ki a mota ta turo ki asibiti a motar mijinta aka kawo ki asibitin kamin a iso da ke na shirya komai, sai dai na tsorata sosai a lokacin na fahimci cewar zuciyarki ce ta buga”

Na kawar da kai daga spoon din da yake kokarin saka min a baki.

“Na koshi”

Sai ya dauki ruwa ya mika min na saka hannu na karba, yana kallon gefen fuskata ya ce.

“Zahra da ace faduwar nan da kika yi baki farkawa ba, wata kila da hakkinki be bar mu ba, musamman ma ni, i know da amincewar ki na aikata but still zalinci ne saboda ke kina neman mafita ne da ace wani nace ki kashe zaki iya kasheshi saboda ki taimaki rayuwar mijinki, if i could turn back the clock zan dauki kudin nan ne na biyawa mijinki a kyauta, ko da zai rayu ko ya mutu”

Ya mike tsaye ya fara kankara maganin yana miko min.

“Zahra zan fada miki wani da na boye miki, ni da Jamila uwa daya uba daya muke kanwata ce, shekararta tara da aure wannan ce ta goma, ta shiga damuwa sosai domin mijinta yana son haihuwa gashi ya tara dukiya amman Allah be ba shi haihuwa ba, ita da shi duk suna son junansu ya kara aure ba sau daya ba sau biyu matan suna fita, sun yi ta neman magani na asibiti da na hausa amman shiru, daga baya sai ta fahimci hankalin mijinta ya tashi sosai saboda rashin haihuwar da kuma tsana ta yan'uwan miji da suke nuna mata ita kanta tana son ganin jininta, a shawarce ta shawarce shi akan a ciri kwanshi a ciri nata a dasa a cikin wata amman be yarda, sannan ta yi mashi magana akan ya bada kwanshi a hada da bata a raini ďan ko yar a cikin machine irin yadda wasu turawan suke a waje shi ma be yarda ba, duk wata shawara da zata kawo zai ce aa”

Na karbi maganin na sha sai ya karbi kofin ya aje.

“Tausayin halin da take ciki yasa na kawo mata shawarar mu busa cikinta idan zata haihu sai mu samu cikin wata mu siya, sai kuma muka yi sa'a da ke a lokacin daman can mun fi a samu irin wannan ďan naki saboda ya zamana na sunna ne ba na banza ba, Zahra karki so ganin farinciki a gurin mijinta da yan'uwanta da kuma yan'uwan mijin a lokacin da aka bada sanarwar tana da ciki, wannan abun ya kara min kwarin guiwar cigaba da abun da muke har muka samu wannan nasarar”

Ya tura akwatin maganin zuwa inda ya dauko shi dazun.

“But then i realized mun cutar da ke, haihuwar fari muka karba kuma ta mutumen da kike tsananin kauna wanda ya mutu ya barki kina bukatar ďanshi iyayenshi ma suna son ganin jinin jikansu ke ma na ki iyayen suna son ganin ďanki, yanzu kuma mun saka ki gaba akan muna son ki shayar da shi, na san ďanki amman ba hakkinki ba ne, ban san Jamila taje ta same ki tana ta magiya ba, sai a jiya da ta fada min dazun ma kamin ki farka ta kira ni tana cewa idan kin farka tana son an sallamo ki ki dawo cigaba da zama gidan saboda ki shayar da yaron, mijinta da tun a jiya wata tafiyar ta kama shi ya kira ni ya ce duk abun da ya kamata na yi miki shi zai biya na san yayi hakan ne saboda kin taimaki rayuwarshi a lokacin da hatsarin jirgin nan ya faru kamar yadda Jamila ta fada min, you saved him and now you saved his wife you're such a wonderful soul Zahra, precious, humble and beautiful”

Ya tako ya karaso kusa da ni yana kallon fuskata ni kuma na sauke nawa idon kasa.

“You deserve happiness Zahra, na miki alkawari zai na cire duk wani ciwo da yake damunki sai na kuranye miki duk wata damuwa i promise you this i will fix what is broken zan cire abun da yake ciwo ne a rayuwarki”

Ya durkusa a gabana yana kallon hawayen dake zuba a idona.

“That's why nake son sanin wacece ke, wace kalar rayuwa kika yi kamin yau akwai labari mai yawa a cikin sumanki da kuma hawayen da kiks zubar ba a yanzu Zahra, N miki alkawari ba zan sake bari abu ya takura miki ba, ba zaki sake tsintar kanki cikin damuwa ba...”

Turo kofar ďakin aka yi daga ni har shi muka juya muka kalli kofar Sauban ne tsaye bakin kofar ďakin yana kallonmu hannunshi rike da manyan ledodi yana sanye da kananan kaya kamar abokinshi. Dr Hamid ya mike tsaye ni kuma na saka hannuna na share hawayena.

“Ya kamata ka kwankwasa kamin ka shigo Malam”

“Nan asibiti ba gida ba Dr ina fatar ka san haka”

Dr Hamid ya nuna mashi kofa duk kuwa da kokarin da yake na kunno kai cikin dakin.

“Tana bukatar hutu you can leave”

“Only if she says so...”

Sauban ya fada a yayinda ya karaso kusa da ni ya aje manyan ledodin a gurin da aka tana da domin dora kaya. Dr Hamid kamar zai sake mashi magana sai kuma ya kalle ni na girgiza mashi alamar aa hakan ya saka shi juyawa ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba.

“How are you Dear”

Na kalli Sauban da sauri ‘Dear’ Kalmar da be taba fada min ba ko a wacan lokacin da nake wasa da shi balle kuma yanzu, ban amsa ba na kalli kofa.

“Ba mu zo tare da Abiey ba”

Ya fada da murmushi a fuskarshi kamar ya san tunanin da nake kenan.

“Da zo jiya kina bachi, dazun ma na zi kina bachi ya jikinki?”

“Na ji sauki”

Ya dauko ledar ďaya ya bude babu komai a ciki sai tarin chocolate wani ma har na manta rabon da na ci irinshi domin a wacan lokacin da muke tare da Abiey yana siya min chocolate masu tsada sosai bayan rabuwarmu kuma Deen ba shi da karfin siya min.

“Na san za a kawo miki abinci so i brought some chocolate for you hope you like it”

Na kalleshi na kalli chocolate's din.

“Ya aka yi ka san ina asibiti”

“Ina tare da Abiey a lokacin da Dr Zainab ta kira shi ta fada mishi cewar an kawo ki asibiti, sai yace Allah ya baki lafiya”

“Shi ya ce ka zo ka duba ni?”

“No”

“Why are you here”

“Because i care for you”

Na kalleshi magana yake kamar ba shi ba, ban samu saba makamancin wannan da Sauban ba, kuma be tana min irin wannan game din ba kamar yadda ban ga alamar da zolaya yake wannan maganar a fuskarshi ba.

“Care for me?”

“Yeah”

Ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinshi yana kallona da duba ba na wasa ba.

“Zahra you go through enough, kin dade kina ba ni tausayi sosai saboda na san zaki fuskancin irin wannan kalubalen a duk lokacin da kika gane gaskiyar cewar Deen yaudararki yayi, amman ban dauka bayan haka wata matsalar zata iya kunno kai a tsakaninku ba, the way da kuke son junanku na tausaya muku sosai musamman ma ke, kuma Inshallah zan yi iya kokarin na ganin komai ya daidaita a tsakaninku”

Na sake kallonshi.

“Ni da Abiey mun yanke wannan shawarar ne saboda muna ganin kamar hakan shi ne mafita a tsakaninmun, bana son wani abu da zai shiga tsakanin Abiey da iyayenshi musamman Mai Martaba, kuma ya kamata dukammu mu yardar da kaddara mu ta mu kaddarar kenan”

“Duk da haka Zahra kina bukatar kwanciyar hankali, idan Abiey yana da Yasmin da zata kawar mishi da damuwarki ke wa kike da shi? Ina fatar shawarar da kuka yanke ba zata shafi alaka ta da dake ba, even though we're friends amman ina son ki aje kallona a matsayin abokin Abiey, ba ina tausayinki kawai saboda wata manufa ba, no ko da ace ban san ki ba iyakarcin tausayin da zan miki kenan, tun daga lokacin da na samu labarin abun da Abiey yayi na san za a samu matsala amman ina son ki dauki wannan a matsayin kaddararki kamar yadda kika fada ki ma jajirtacciyar mace Zahra”

“Deep down i know one day things will change, ba zamu dawwama a haka ba Sauban, wata rana komai zai zama labari idan muna raye wani lokaci kamar haka mun manta da komai, ina son na tafiyarda rayuwata kamar Abiey be taba rayuwa a cikinta ba, not because of bana son but because of kaddararmu, kuma idan har ina son na manta da Abiey dole ne chanja komai na rayuwata mu'amala ta zamantakewa, abokanin mu'amala so that i can move on i have to believe in myself”

Na fada hawaye na sauko min.

“Hakan yana da kyau”

Ta furta a gajarce yayi shiru, jikina ya ba ni cewar kallona yake, a yayinda nake ta aikin sharar kwalla.

“Am... Ban san ko akwai abun da kike so na zo miki da shi idan zan dawo”

“Ba sai ka dawo ba Sauban na gode da kulawa”

Na fada mishi ina kallonshi.
Chapter 64 · 0% Book details