← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 127

Sashe 76

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ita dai bata sake haihuwa ba, ni kuma na sake samun cikin Zainab a haifeta lafiya kalau tana da shekara uku mahaifinta ya rasu ya bar mu da yara, bayan na cika idda mutane suka ta aikowa suna sona wasu kuma suna nunawa da yawan wasu na san suna kallon dukiyar da mijina ya mutu ya bar mana ne ni da yarana wanda na tabbatar ba zamu taba iya cinyata mu kadai ba duk da kasancewar an raba
gado an bawa kowa na shi, a cikin mutanen da suka ta so neman aurena har da mahaifinka ba wani wata wata ba na amince aka daura mana aure ba wata da wata matsala ba sai dai na shiga gidan cikin rashin sa'a saboda yan'uwanshi ko kadan basa so na, saboda ni ba yar sarauta ba ce kuma suna ganin be kamata ace yana matsayin Sarki ya auro mazawara mai yaya uku ba, Mahaifiyar Yasmin bata bar ni na tafi da Auwal da Muhammad Sani ba, sai ta kama su ta rike daman ba ni da haufi na san ba zata cutar da yayana ba, sai na tafi da Zainab kadai, aiko sai Mai Martaba yace wa yake son a cikin yaya ba ita ba, kaunar da yake nunawa Zainab be taba nunawa yayanshi ba, na rayu a cikin wata soyayya da mulki Mai Kulki Martaba ba baya shawara da kowa sai ni, har mantawa yake yana da wasu matan komai dai Umaima zamanshi Umaima tashinshi Umaima, komai aka kawo sai yace a kawo gurina, idan na ce abu baya tsallaka ba hakan yasa kowa yake zargin wani magani na yi mashi, alhalin ban taba zuwa gurin kowa na roki ya ba ni magani da zai kara kaunata a zuciyar shi ba, mu yi zama na rashin dadi tsakanina da matanshi mun yi ta samun tsabani, suna magani kala kala ni kuma bana yin komai sai dai na san abu daya, bana wasa da addu'a kuma a lokacin da mahaifinta tana raye ta rubuta min Bismillah dubu na sha, sai dai bakina yana min yaki sosai domin idan aka min abun da ban gamsu ba ko ban jidadinshi ba a take nake fara masifa kuma idan ya zo ni zai shigarwa ko da kuwa ba ni da gaskiya har muka kai wani matsayi da Mai Martaba baya iya kwantanta adalci a tsakanina da sauran matanshi, kamin ya aureni yayi alkawarin cewar ba zai taba yarda a sakawa ďanshi ko yarshi sunan iyayenshi ba, amman ni shi da kanshi ya fada min cewar idan na haifi namiji sunan mahaifinsa sai saka mashi wato Aliyu idan kuma mace na haifa sunan mahaifiyarshi zai saka Khadija, idan kuma na haifa mace da namiji duka zai saka sunan iyayenshi, ai kuwa sai yan'uwanshi suka ce ba su da makiyiya abar tsana sai ni, duk kuwa da irin kyautata musu da nake da kuma nake sakawa yayi musu, sai dai akwai wani kanenshi Margayi Surajo wanda Waziri ne a wacan lokacin kamin ya rasu ubansu daya da Mai Martaba shi kam yana so na sosai ba kamar sauran ba, da tsanar ta yi yawa sai Mai Martaba ya kamin min gida dabam”

Ammy ta ja dogon numfashi ta sauke tare da tashi tsaye da sauri ta shige bathroom tana hawaye, sakamakon shigowar yaran Dr Zainab, Abiey ya tashi tsaye yana musu murmushi yaja su suka fice daga ďakin rike yana musu wasa dayan hannunshi rike da da plate din apple da ya kwashe.

ZAINAB POV.

Ba a dauko dogon lokaci ba Mijinta ya shigo, a tsanake ta yi mashi bayanin komai sannan ta kora mashi da abun da take ganin shi ne mafita a gareta a yanzu.

“Ina son na hadu da shi na bashi nono results din ya san gaskiyar komai, bana son ya kai gobe domin ba mu san abin da zai iya faruwa ba, wacan karon ma saken da na yi na ya haifar da matsala har Deen ya samu damar da ya samu”

Engr yayi shiru na dan lokaci yana nazari.

“Amman kina ganin zaki samu ganinshi a yanzu?”

“Zan fara kiranshi”

“Kira shi to, ki fada mashi za ku hadu wani guri safe da ba gidanshi ba”

Yana rufe baki Dr ta dauki wayarta ta kira Mr Bashir be daga ba, sai ta yanke shawarar tura mashi sakon kar ta kwana.

“Salam, ina son hadu wani guri da ba gidanka ba ina son na baka results din da ka bukata a yau din nan, kuma akwai magana mai muhimmanci da nake son mu tattauna”

Tana tura sakon ta dauke hannunta sai ga kiranshi ya shigo, jiki na rawa ta yi picking.

“Hello ranka ya dade”

“Dr kina lafiya?”

“Alhamdulillah ka karanta sakona”

“Shiyasa na kira ki ai, zaki iya zuwa ki same ni a Mr Bashir Auta Estate?”

“Eh ranka ya dade amman zan zo tare da mijina”

“Ba matsala i will text the house number”

“Okay”

Ta kalli mijinta bayana ta kashe kiran.

“Yace mu same shi a Auta Estate”

“Tashi ki saka mayafinki i will drop the kids gidan Ammy zai mu je mu ganshi domin a can zasu fi samun tsaro idan mu ka bar su nan ba su musan me zai faru ba”

Tashi ta yi ta dauki mayafinta ta saka da jakarta da results din yake ciki, mijinta kuma ya saka yaranshi a mota duk da kasancewar akwai mai gadi amman hankalinshi be natsu da shi ba domin ba manta yadda aka taba shigowa cikin gidan aka tafi da shi ba. Sai da suka fara sauke yaran gidan Ammy suka tabbatar sun shiga cikin falon sannan suka juya ba tare da su sun shiga ba, suka dauke hanyar Estate din Mr Bashir wasu manyan gidane ne da ya gina na alfamar yake badawa haya ga wandanda suka ci suka koshi, domin Estate ne ba babu ta biyunta a garin Kano, komai na bukatar rayuwa a saka a unguwar babu abun da za su fito su nema sai dan ra'ayi ba dai da rashi ba, tun daga gurin hutawa har shopping da makaranta da police station da private hospital. Suna tafe suna hirar abin da da yadda suka kallon lamari har suka isa gaban wani wangalelen gida da number shi take rubuce a jikin screen din wayarta da Mr Bashir ya turo mata da kanshi. Sai da ta kira shi ta sanar mashi suna waje ya aiko manyan bodyguards din da zaka iya rantsewa da Allah naman mutan suke ci tsabar girma da karfi fukarsu babu annuri, suka shiga da su ciki su kansu sai da suka tsorata, ko'ina na gidan cameras din tsaro ne ga kuma police daga ciki suna gadin gidan, Dr ta san da unguwar amman bata taba sanin yana da gidan da yake zama a ciki ba sai yau. Hankalinta be kwanta ba har sai da suka shiga cikin gidan ta yi arba da shi ya tarbe su da far'ah sannan ta samu natsuwa har ta zauna suka soma gaisawa, Engr ma hannu ya mika mashi suka gaisa sannan ya samu guri ya zauna kusa da matarshi.

“Dr Allah yasa results din ne?”

“Ranka ya dade results din ne, amman kamin na baka akwai abun da nake son na fada maka, kuma akwai rokon da nake son na yi maka, ina fatar zaka saurare ni kuma zaka duba abun da zan fada ko na gabatar da idon basira”

Mr Bashir ya kalli Engr duba na natsaki sannan ya kalli Dr Zainab ya gyara zama.

“Ina saurarenki”

Dr Zainab ta sauke ajiyar zuciya ta kalli mijinta sannan ta fara magana cikin natsuwa.
[11/16, 4:39 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣0️⃣

“Na san ba hurumi na ba ne shiga cikin rayuwarka ko yin magana akan wani abu da ya shafi iyalinka, sai dai a matsayina na wanda ka yardar da ni kuma a matsayina na musulma ina da hakki na lurar da kai ga wani abu da be zama lallai idonka ya kai can ba, bana son ka ce na maka katsalandan a al'amurra...”

Bata karasa ba ya daga mata hannu.

“Dr... Zainab ina tunanin kin san da cewa akwai likitocin da suka fiki gwarewa a aiki, kuma akwai likitoci da yawa a kasar nan har wajen kasar nan, amman yarda da ke da abokina da wanda ya hada ni dake yayi ya sa na aminta da ke na dauki ragamar aikin nan na danka a hannunki, ina fatar ba wata matsalar kika samu ba, and you can go ahead kai tsaye ba sai kin tsaya rabe rabe ba, kuma idan da dama mijinki ya ba mu guri a iya sanina dokar aikinku sirrin majinyaci da likita sirri ne”

“Haka ne, amman na shigo da shi ne saboda na yardar da shi kuma shi ma yana daga cikin wani bangare na labarin da zan baka, kuma ina son ka aminta da ni ne ka san da cewa bayan shi da kanena babu wanda ya san da wannan labarin, kuma babu wanda zai taba sani ko da za a dora min wuka a wuyana”

Dr Zainab ta fada sannan ta saka hannunta cikin ta dauko results din ta rike.

“Bana son ka dauki abun da zafi ne, Dr Hamid ya same ni gida ya ba ni tukicin kudi naira miliyan hansi akan na canja results din dake cikin takardun nan, amman ban aminta da yin haka ba domin ba zan iya lalata aikina ba kuma ba zan iya cin amanarka ba, amman ina son zan roki alfarma karka yanke hukunci a cikin fushi ka tsaya ka yi nazari kuma ka yi adalci karka dubi cewar wannan matar ka ce wannan kuma baka da alaka da ita”

Ta mike mashi results din sai ya mika hannu ya karba zuciyarshi na bugawa da mugun karfi bugawar da ya wuce misali bugawar da zai iya haifar mashi da matsala a take, sai ya gama zagaye katon falon da ido sannan ya sauke akan takardun dake nade, ya saka dayan hannunshi ya warware ya fara dubawa, sai ga naman fuskarshi na rawa kamin ilahirin jikinshi ya karba duk sanyi dake falo sai da gumin bakinciki ya karyo mashi.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Chapter 76 · 0% Book details