← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 127

Sashe 14

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Mama na je gidan a rufe yake, dan Allah ki yi hakuri ki bar na zauna nan ba ni da inda yafi min nan”

“Kin san da wannan kika kama kafa kika maida gaba gabas kika gudu? Kina takaba da tsohon ciki?”

Ta tashi ta shiga dakinta bata dade ba ta fito ta jefo min makullin gidana.

“Ashe kin san da gidan kika bar shi kika tafi, to ga makulli nan dauki ki juya”

Na duka na sauka wasu irin hawaye masu zafi suna sauko min.

“Mama na tafi?”

Na tambaya ina jin kamar tace min aa Zahra dawo ki zauna.

“To har sai na fada miki? Kin manta halina wai?”

Na juya na fara tafiya kamar bana son fita na bar gidan, kamin na isa titi ma wata uwa da ga duniya ce, haka na sake tare wani mai daidaita na shiga ya maida ni gidana, na saka makullin na bude na shiga ciki ina ganinsa kamar kangon gida, tsaye na ji a tsakar gidan bayan na tura na kara kofar ban rufe ba, ina kallon kofar falona, ji nake kamar na bude baki na ce Deen na dawo ya amsa min, ji nake kamar ya fito ya rumgume ni yana murna da ganina, amman babu hali saboda babu shi a tsaye. Na karasa na bude falon na shiga na zauna sai na rasa ta ina zan fara kuka, ina zaune har aka kira zahar na tashi na yi alwala na yi sallah na yi ta ambaton Allah har wata sallah ta tararda ni, na gabatar da ita na kwanta a gurin ina jin yadda yunwa ke neman dauki a cikina, amman bana da kuzarin yin komai sai kuka. Har aka kira magariba babu wanda ya shigo gidan saboda babu wanda ya san na dawo sai Mama ira kuma na san ba fadawa kowa za ta yi ba saboda tana fushi da ni, kuka kan a ci shi har na koshi daker na samu na lallaba na yi sallah magariba a zaune na kwanta ina da tunani can na ji an kira isha'i na tashi na yi, sai zuciyata ta cika da kewar mijina mutumen da baya barina da yunwa no matter how yake fushi da ni, mutumen da komai zan masa a duniyar nan baya iya barina cikin bakinciki da damuwa. Tashi na yi na bude jakar da tufafinsa suke ciki na fiddo wani fari yadi nasa da yake yawan sakawa ranar jumma'a na dauki filona dake kan katifa na saka masa rigar na kwantar da fito sai na dora kaina ina ta jin kamshin jikinsa, halshen dake cikin bakina har rawa yake saboda kukan da nake jikina na amsawa ta ko'ina.
A rayuwa babu bakincikin da ya kai na miji ya tafi ya bar matarsa tana begensa, abun nan yana da matukar zafi da ciwo, ka tuna cewar ba zaka kira mutun ya amsa maka ba ba zai san halin da kake ciki ba, kuma ba zai taba dawowa ba sai dai taka zuciyar tai ta begensa.

“Tafiyarka ce ta haddasa komai Mijina, mutuwar ta yaye farincikina ta gusar da hasken da yake zuciyata, ina ma ina ina ma ka dawo Deen ga Zahra na ta begenka”

Na karasa ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya da dan kuzarin da ya rage min, ina cikin wannan hali wutar unguwar ta dauke gaba daya. Can na ji an turo kofar gidan ana haska ko'ina da fitila mai haske.

“Sallamu Alaikum”

Wata murya da nake jin kamar na sani tana ta doko sallama, sai dai ba ni da kuzarin amsawa sai na kuka, har cikin falo aka shigo wannan karon sunana ake kira sai na gane mai muryar tun kan ta karaso cikin dakina.

“Zahra...”

Ta haska ni da fitila bana iya komai sai kuka.

“Subhanallahi”

Ta furta tana karaso kusa da ni da sauri.

“Miya faru kika zauna ke kadai kuma cikin hudu babu ko haske”

Na mika mata hannuna sai ta miko min sannan nata ta tashe ni zaune ta haske fuskata da kyau, sai ta yi saurin aje wayarta akan tafitar ta rumgume ni.

“Na gode da kika zo Anty Zainab, na gode...”

Na furta cikin wani irin kuka ina kankanmeta...

*Allah yasa ba ni kadai Zahra ta tabawa zuciya a yau ba* 😪
[10/6, 2:52 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣0️⃣

Kuka na yi sosai a kafadarta sannan ta dago ni ita ma idonta na zubar da hawaye ta ce.

“Miya same ki Zahra? Miya kike wannan kuka haka?”

Na yi shiru domin ban san me zan fada mata ba.

“Kina zaune ke kadai acikin duhu daman ke kadai kike kwana a gidan?”

Na girgiza mata kai.

“Guduwa na yi sai yau na dawo, kuma Mama ta ki ta karbe ni”

“Amman miyasa kika gudu?”

Na kalleta kamar na fada mata sai kuma na ga fadin ba shi da amfani saboda ba zata sama min mafita ba, kuma dan'uwanta ma ba zai min ba domin be taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon ba balle yanzu, kuma fada mata zai kara bayyana sirrin dake rufe ne, a tonawa kaina da ita kanta Jamila asiri.

“Babu komai”

“Babu komai zaki gudu? Look Zahra na san kina jin haushina ni da dan'uwana amman wannan matsalar da kike ciki ba abu ne da ya shafe ni ko ya shafe shi ba, ki kawar da komai a ranki ki fada min damuwarki wata kila zamu iya samun mafita?”

Na girgiza mata kai.

“Ba komai, me kika zo yi nan?”

Ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa fuskata.

“Ba komai na zo na duba lafiyar Kanwata ne kawai zan je gurin aiki sai kuma na tsaya ta nan na dubaki”

Na sauke kaina kasa.

“Yanzu fada min kina son Mama ta dawo ta zauna ne ko kuwa kina son ki koma gurinta ne da zama?”

“Zan koma gidanta”

“To taso muje”

“Tace ba zan zauna ba, fushi take ni”

“Zan mata magana kuma zata ji i promise”

Na sauko saman katifar na dauki hijab dina na saka na dauki makullin gidan, a tare muka fito ita ta rufe min gidan ta saka ni gaba har gurin motarta ta bude min gaba na shiga na zauna sannan ta zagaya ta shiga ta tashi motar, har muka isa gidan Mama hawaye na ke ga idona ciwo yake saboda kukan da na yi, ko da muka doshi kofar gidan sai na tsaya daga baya tana ganin haka sai ta riko hannuna ta wuce gaba sai da ta yi sallama aka amsa mata sannan ta shiga cikin gidan. Mama ta fito daga daki tana kallonta da ni kamin ta ce.

“Sannu da zuwa”

“Mama ina wuni?”

“Lafiya kalau”

Ta amsa da muryar da ke nuna har yanzu bata sauka daga fushin ba.

“Mama zamu iya zama?”

Anty Zainab ta fada sannan Mama ta dauko tabarmar dake jingine ta shimfida mata muka zauna kaina na kasa.

“Mama na taso zan je gurin aiki sai na tsaya ta gidan Zahra da zimmar na duba halin da take ciki, sai na same ta tana zaune ita kadai a dakina tana ta kuka idonta har ya kumbura, ga hudu babu wuta a gidan na tambaye ta abun da ya faru bata fada min ba, sai tace kin ce ba zata zauna a gidanki ba haka ne?”

Mama ta kalleni sannan ta amsa mata.

“Haka ne”

“Ban san girman laifin da Zahra ta aikata miki ba, amman a yanzu Zahra bata da wani gata sai na ki bata da wanda zai tsaya mata sai ke, tun da mijinta baya raye mahaifinta ma baya raye duka duka yaushe Deen ya rasu? Bata gama fita daga jin zafin rashin mijinta ba sai kuma ace ta fuskanci wata damuwa daga gareki? Ke fa uwace Mama kuma kin san yadda mace take ji idan ta rasa miji domin ke ma kin rasa mahaifinta, idan kika ce Zahra ba zata zauna tare da ke ba gurin waye kike son ta je ta zauna? Dan Allah ki yafe mata idan wani abun ta yi miki ki tausaya mata ki dubi halin da take ciki, ta ya zaku barta can ta zauna ita kadai kamar wanda ta rasa kowa?”

Mama ta sauke ajiyar.

“Shikenan ya wuce na gode”

“Yanzu zata iya zama a gurinki ko? Ko kuma zaki koma can inda take ne ki zauna?”

“Aa sai dai ta zauna a nan”

“To na gode Mama Allah ya saka da alheri”

Sai a lokacin na dago na kalli Mama Anty Zainab kuma ta mike tsaye ta yi mana sai da safe ta fice.

“Mama kin yafe min?”

“Idan ban yafe miki ba tsine miki zan yi Zahra?”

Na tambaya kuma ta amsa min da muryar kuka.

“Akan me zaki aikata wannan abun? Yanzu da kin jefe kanki a wannan halin ya kika ji? Ke idan zaki yi abu ba ki san ki yi tunani ba? Akan me zaki siyar da abun cikinki akan mutunen da be cancanci haka daga gareki ba? Ina kika taba jin an siyar da cikin? Sai kasashen inyamurai”

Kalmar akan mutumen da be cancanci haka daga gareki ba ya fi komai tayar min da hankali.

“Mama Deen din ne be cancanci haka daga gareni ba? Ko dai kin manta waye Deen?”

“Na san waye shi mana ai yana kaunarki yana sonki amman ba so da kauna na gaskiya ba, idan yana sonki akan me likitoci zasu ce ya ke6e kansa daga kusantar ki amman be yi haka ba? Kuma mahaifaiyarsa ta san da wannan ta kyale ku? So yake ke ma ki kwashi ciwon ki wahala ko? Sannan da zai rasu ma cewa yayi ki masa alkawarin ba zaki taba auren kowa ba har ki mutu wannan ma duk soyayya ce”

Na girgiza mata kai hawaye na sauko min.

“Mama baki fahimta daidai ba Deen yana so na sosai”

“Toh Allah ya bar kauna Laila matar Majnoon”
Chapter 14 · 0% Book details