← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 127

Sashe 42

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“I don't know how amman tabbas ta gane gaskiya, ban san ma me zan ce mata ba kawai na baro ta a can na dawo gida, ina ganin kamar mafarki na ke yi”

Ammy ta rika kallonshi with confused gabanta na faduwa.

“Ammy are you not happy?”

Ta yi saurin yin dariyar da bata kai zuci ba ta.

“Of cause I'm happy Aliyu ka samu abun da kake so me zai saka ba zan yi farincikin ba, amman ka lallabata ne ko kuma me? A ina ka hadu da ita?”

“Gidansu na je”

Ya furta yana ciro wayarsa dake ringing a aljihu ya mike tsaye yana amsa kiran Sauban ya nufi kofar fita. Ammy ta bishi da kallo har sai da ya fice sannan ta juyo da kanta tana mamakin yadda zai fada mata cewar Zahra ta yafe masa? Saboda maganar da tayi mata ne ko kuma wani abu take shirya masa? Ammy ta mike tsaye ta nufi upstairs tana tafe tana tunani har ta shiga dakinta ta nufi gefen gadonta ta dauki wayarta. Number Dr Zainab ta fara dialing ta dora kafa daya kan daya.

“Daman na ce sai Ammy ta yi missing dina”

Shi ne abun da Dr Zainab ta fada a lokacin da ta amsa kiran

“Amman ko a waya ai ya kamata ki kira ko?”

“Ammy kiran waya ma sai kana da time fa, kwana biyun nan aiki yake min yawa, gashi yara sun koma school shiyasa bana samun zuwa”

“Zaki samu shigowa yau?”

“Miya faru? Na ji muryarki wani iri”

Ammy ta sauke ajiyar zuciya.

“Aliyu ne ya zo min da wata magana mai nauyi kuma mai wuyar fassarawa”

“Kamar wace irin magana?”

Ammy ta nisa sannan ta bata labarin da Abiey ya bata, sannan ga dora mata na abun da ya wakana tsakaninsu da Zahra.

“Ammy ina ganin maganar da kika mata ne ya saka ta natsu, kin san mace tana da wani abu daya, tana aikata abun da take so idan aka lallabata sai dai daga lokacin da ka fara yi mata wuta to zata yarda a zauna lafiya”

“Hakan na nufin Zahra ta san Aliyu bw yaudareta ba kenan? Amman ta kyale shi yana ta bibiyarta? Har ta ci mutuncinsa a gaban yan'uwansa?”

“To wata kila kuma ta gane gaskiyar ne”

“Ko kuma tana son ta yi amfani da damarta ta cutar da shi ba”

“Kamar ya?”

“Zata iya nuna masa cewar ta gane gaskiya saboda ta raba shi da Yasmin kuma ta hada shi da Mai Martaba, daga karshe tace ba zata aure shi”

“Bana tunanin haka, yanzu dai abu mai muhimmanci musan ta ya aka yi ta fahimci gaskiya?”

“A kaddara ta gane gaskiya ne, gane gaskiyarta zai haifar da matsala, domin abu ne mai wahala Aliyu ya auri Yasmin, sannan Yasmin ko iyayen ta ba za su yarda wani matsala ya fito daga bangarensu ba, na kuma san waye Mai Martaba ba zai taba yarda a rushe maganar auren ba, kin ga hakan zai iya haifar da matsala a tsakaninsu”

“Ba zai ji dadi ba, amman zai fahimta mace ma yanzu ba a mata auren dole balle kuma Namiji”

“Ba lallai ne ya fahimta ba, Dr ina jin tsoro kar haka ya saka Aliyu da Mai Martaba su samu matsala, domin ba lallai ne Mai Martaba ya yarda Aliyu ya auri bazawara ba, kara ma a da lokacin da aka ta hidimar auren yanzu be ce komai ba kuma be saka kansa a ciki ba, saboda a lokacin be kula da Aliyu ba, yanzu kuma ya kula har yayi magana”

“To Ammy ya zaki yi yanxu? Kin san dai ba zaki ce Abiey ya daina son Zahra ba ko kuma ya ki aurenta ba zai ma saurareki ba, kin kuma san ba zai sake sakacin yarda ya rasa Zahra a karo na biyu ba, ba kuma zai auri Yasmin ya auri Zahra at the same time ba”

“Miyasa ban masa magana ba, ni sam zuciyata bata yarda da cewar yarinyar da zuciya daya take sonshi ba a yanzu, amman zan yi magana da Zuwaira”

“Ammy kar garin neman gyara gira ki rasa ido, karki aikata abun da zai saka Abiey ya yi ta kallonka da wata fassarar ta dabam”

Ammy ta sauke ajiyar zuciya.

“Zan yi tunani akai”

Ta sauke wayar sannan ta kashe tana kallon wani bangare na ďakinta, sai kuma ta mike tsaye ta nufi gurin windows dinta ta bude tana hango Abiey da har lokacin waya take makkale a kunnensa yana jingine jikin mota. Ammy ta maida dubanta gurin wayar hannunta ta shiga contact list dinta ta yi dialing number Anty Amarya ringing daya ta yi picking.

“Yanzu fa nake kokarin kiranki, Abiey ne ya fada min wata magana yanzu, wai Zahra ta nemi yafiyarsa”

“Haka yace min ni ma yanzu, amman ina son ki zauna da shi ki nuna illar rashin auren Yasmin, idan yaji zai hada biyu ruwansa ne, amman ni dai bana son ya fasa auren nan”

“Ni ma na yi wannan tunani, saboda Mama Lami da Hajiya Kilishi za su samu hanyar bata shi a gurin Mai Martaba, shi kan shi Mai Martaba zai ga kamar Abiey ya dauke shi karamin mutum ne, domin shi ya furta yana son Yasmin din a lokacin, ina ganin idan har zai fuskanci Mahaifinsa da maganar sai dai ya roki alfarma a amince masa ya hada da Zahra din”

“Ki yi magana da shi, ni ma zan nuna masa haka, ko dan ita Yasmin din domin na lura ita ma tana son shi”

“Inshallah”

Da haka suka rabu. Abiey ya dade a waje yana waya da sauran kamin ya kira Anty ya fada mata da Dr Zainab da kawarshi Safeena.

“Oh Congratulations finally zaka samu waraka daga ciwo kenan, kuma zaka farfado daga dogon suman da ka yi”

Safeena ta fada sai yayi dariya.

“Allah kadai ya san yadda na ke son yarinyar nan, ba ni da wani buri a yanzu bayan wannan”

“Ita ma kuma zata yi dacen miji Abieu ko da ace mace kaunarka take ka zauna da ita zata ji dadi balle kuma ace kai kake kaunarna, ai ko na so na ga fuskar Zahra yau, kuma na so na jidadin da ya ta fahimta yanzu har take neman yafitarka”

“Ni ma ina son jin haka, I'm out of worlds best out of control shiyasa ban ma iya tsayawa na yi magana da ita ba, komai ya zo min kamar mafarki sai kawai na bar gurin, but zan koma anjima da dare zan yi magana da ita”

“Okay idan ta labarta maka ni ma ka fada min, and ka fada mata Safeena na gaishe ta sosai da sosai”

“I will tell her Safeena, i will”

“Hmmm Happy Boy Congratulations once again”

Yayi dariya sannan ya sauke wayar.

ZAHRA POV.

Tashi na yi na dawo cikin gidan sai na zube a tsakar gidan ina jin kamar na narke a gurin saboda kuka da tashin hankali Abiey ya tafi be ce min komai ba, Mama na tambayar abun da na faru na zazzaga mata komai ina kuka. Yaya Maryam ta kama ni ta zaunar kan tabarmar da Mama ta shimfida sannan ta rungume ni.

“Haba Zahra ke ma kin san Abiey zai dawo mana, wata kila mamaki ne ya saka shi yin haka, amman wanda yake neman a hudu balle kuma yanzu da ya samu aka hasko masa, zai dawo ki kwantar da hankali komai ya zo karashe ai, daman bawa baya wuce kaddararsa da baki auri Deen ba”

Haka ta yi ta lallaba ni da kalamai masu dadi tana kokarin kwantar da min da hankali, cikin ikon Allah sai na samu sa'ida kuka da nake ya tsaya har muka dauko zancen wani bangare na rayuwar mu da Abiey. Ana daf da sallah azahar sai ga Hajiya ta zo gidan, Mama dai bata fasa halinta ba na tarbonta da far'a tana mata sannu da zuwa, ni dai kasa daga kai ma na yi na kalleta, sai dai duk da haka na lura Yaya Maryam ta fi ni daukar zafi domin tun da Hajiya ta dauko maganar Yaya Maryam bata ce komai ba, kara ji na kan jefa wata kalmar jefe jefe saboda na nuna mata ban jidadin abun da ďanta yayi min ba. Mama kuma tana nuna mata kamar Deen be aikata wani laifi ba saboda ya rike ni irin rikon da ko wace mace take so, tabbas ban san komai ba a tsawon zamana da Deen sai gata da soyayya, sai dai a yanzu na na kasa yafe masa saboda ya saka ni da Abiey mun mutu akan abun da ba shi ne gaskiya ba.

“Ban taba sanin haka kike Zahra sai yau, lallai ďana yayi hakurin zama da ke, ashe akwai abun da zai saka ki manta waye Margayi a gurinki? Ina soyayyar da kike masa? Ashe duk ta karya ce? Na gode Allah da ya nuna mana halinki tun yanzu, ashe da Margayi ya rayu ya kawo yanzu da ya wahala domin kiyayyar da zaki nuna masa ba kadan ba ce, Zahra kin yi ba zata”

Na dago na kalleta.

“Hajiya ba zaki ga laifin...”

Ban karasa ba Mama ta daga min tsawa hakan ya saka na ja bakina na yi shiru. Har ta gama abun da zan iya kira da borin kunya ta tafi ban sake ce mata uffan ba.

“Tsakani da Allah Hajiya ta raina mana hankali, ta ya ďan ka zai aikata abu bayan kuma an gano gaskiya ka ce ba za a ga laifinsa ba? Da saninta ya aikata duk abun da ya aikata, yanzu take son ganin Laifin Zahra”

Yaya Maryam ta fada sai Mama ta nuna ta da yatsa.

“Ke ma ki iya bakinki, har gobe Hajiya Mamanki ce ko ba dan Abiey ba miji daya muke aure, kuma har gobe Zahra bata isa ta goge kanta daga kasancewa matar Deen ba, dole sai an fadi cewar ta taba aurensa, saboda haka ku dauki wannan abun a matsayin kaddara”
Chapter 42 · 0% Book details