← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 127

Sashe 70

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ga wannan ki samu wayar da zaki rika magana da mutane, ga kuma sabon line ba lallai kowa ya san kina da shi ba sai wanda kika aminta kika bawa number”

Kallon wayar na yi sai na ke jin kamar yana min maganar Abiey.

“Aa bana son rike waya a yanzu”

“Kin fi son idan zan zo na rika aikawa ana kiranki ko da yaushe? Kuma idam ina son na gaisa da ke sai na zo”

“Aa ba lallai masu gidan su rika bari kana zuwa ba”

“That's why nake son ki karbi wayar nan i promise you ba zan bawa Abiey number ba, you can trust me”

Na dade ina tunanin karba sannan na mika hannu na karbi wayar na yi mashi godiya, sannan na juya na shiga ciki na sanar da Mama ta ba shi izini sai ya shiga ya gaisa da ita ya bata hakurin abun da ya faru har yayi ikirarin siya mana gurin zama.

“Aa nan ma ya ishe mu ba sai an nema mana wani gurin ba, amman dai idan da hali ina son ka je ka samu shi Malam ka bashi hakuri kuma ka biyaki kudin gidanshi idan kuma yama bukatar a gina mashi wani ne sai ka gina mashi saboda an shiga hakkinshi”

“Wallahi Mama ba Abiey ya saka a rushe gidan nan ba, amman dai za a yi haka saboda kowa yana kallon mu muka aikata kuma shi ma ba zai fahimta ba zan bashi hakuri da yardar Allah”

“Toh Allah ya bada iko mun gode”

“Akwai wani gida da yake gabanku sabo ne da ake ginawa na yi maganar shi idan zai muku sai a siya muku shi”

“Aa nan din ma wadatar karka bata kudinka mun gode Allah ya kara rufa asiri”

Duk inda ya taro akan siya mana gida sai Mama tace mashi aa da haka dai ya hakura yayi mata sallama bayan ya aje mata kudin da zai kai 100k ya taso na rakoshi muka dawo gurin motar.

“Ke da Mama halinku daya na kawaici idan ance za a muku abu sai ku ce aa”

Na yi murmushi, sai ya bude motar ya dauko wata karamar leda ya miko min.

“Ga chocolate na siyo miki karki ce aa please shaidan kawai ake yi ma kyauta ya ce aa”

Da wannan furucin ya daure sai na saka hannu biyu na karba ina mashi godiya.

“Yanzu kuma sai yaushe?”

“Shikenan mana ba sai ka sake zuwa ba”

“Korata kike yi?”

“Aa ka ga nan ai ba gidan mu ba ne, ba kowa zai dauka a rika shigo mashi a gida kai tsaye ba”

“Shikenan idan akwai waya ai ba zan rika takura miki da yawa ba zan san halin da kika ciki so that na tabbatar da lafiyarki”

Da wannan muka rabu, sai dai hakan be saka ya daina zuwa ba ya maida kiran a waya kamar wani abinci da safe zai kira ya tambaye lafiyata da yadda na tashi haka ma da rana da dare ma idan zai kwanta sai mun yi waya, tun abun na damuna ina kin sake jiki har na ya fara same min jiki abun ka da mai bukatar abokin hira ya kan cire min kewa shi da Dr Hamid dake zuwa lokaci lokaci wani lokacin kuma sai na wuni a falon Hajiya Jamila ina kula da Amir ina kallo, domin na fara sabawa da gidan da kuma ma'aikatan gidan sai dai na ki yarda na sake jiki da kanwar Mr Bashir saboda ta cika saka min ido da yawa ga yawan tambaya kamar yar jarida a wata daya da na kwashe a gidan har yanzu ban gama karantarta ba idan bata garin saboda yanayin aikinta na zuwa kasashe da garuruwa har sakewa nake ita ma kanta Hajiya Jamila bata sakewa idan bata cikin gidan, sai dai na lura Ummiter yarinya ce mai son mutane da hira, kawai dai basa jituwa da Hajiya Jamila ne domin idan muka zauna a falon daga ni sai ita zata yi ta zagin Hajiya Jamila ne a gabana ni kuma wannan yasa bana cewa komai gudun kar ta kara gaba da ni tace na ce alhalin ban ce ba.

Ba a iya kiran waya Sauban ya tsaya ba har sakon karta kwana turo min yake wani lokacin na kan tsaya na karanta wani lokacin kuma bana karantawa na ke gogewa, a sati sau daya yake zuwa mu gusai ina kallon kamar Abiey ne ya saka shi yi min haka wata zuciyar kuma na raya min kamar Sauban yana son ya maye min gurbin Abiey ne, duk kuwa da kasancewar be nuna min ko ya furta min yana so na ba amman yanayin yadda yake kula da ni da yawan waya akai akai abun ya daure min kai, idan na yi mashi magana sai ya nuna ba saboda Abiey yake yi ba, ita ma kanta Mama ta fara zargin Sauban so na yake, duk zuwan da Sauban yake gidan be taba haduwa da Mai gidan ba, domin ya fi zuwa da rana shi kuma mai gidan baya zama sai da dare ko da safe, idan ma yana nan kullum yana bangarenshi ba kasafai yake shiga bangaren Hajiya Jamila ba, idan ma yana shiga bana gani domin ta gargade ni cewar idan yana cikin gidan kar na shigo sai ya fita bangarenta, ko Amir take son a goya wani lokacin sai dai ta dauko shi ta kawo min BQ a nan zan ba shi nono na goyashi.

Kamar ko wane sati muna jingine jikin motar Sauban muna gaisawa muka ga an bude gate da sauri motar mai gidan ta kunno kai, daga ni har Sauban kallon motar muke har ta karaso inda muke tsaye ta faka aka sauke gilashin motar, tsabar faduwar gaban da nake kaina har wani tsarawa yayi.

“Sannu na zuwa”

Na daga ina dan risinawa sai da ga karewa Sauban kallo sannan ya kalleni.

“Waye wannan?”

Na kalli Sauban na rasa ta ina zan fara.

“Ah... Ah... Ah”

Maganar ta ki fita na rasa kalar karyar da zan yi.

“Idan kin sallame shi ki same ni a bangarena”

“Toh Yallabai”

Na fada sannan ya wuce da motarshi ni kuma na kalli Sauban da tsoro na ce.

“Ka ga abun da na ke gudu ko? Ka tafi dan Allah daman irin mutanen nan ba sa son ganin kowa cikin gidansu”

“Zan tafi amman zan dawo, dole yayi hakuyi saboda ya aje ki a gidanshi”

Kamar na yi kuka haka na ji kamin Sauban ya bar gurin har gumi ya tarar min. Yana wuce na shiga BQ na fadawa Mama abun da ya faru da kuma son ganina da Mijin Jamila yace yana son yi.

“Daman can ni zuwan da yake ba son shi nake ba, saboda zai haifar da matsala ne kawai a tsakaninku kin san ba zai yiyu ki ce zaki aure shi ba yana a matsayin abokin Abiey, kawai dai bana son na hana shi zuwan ne ya ga kamar ina korarshi ne”

“Ni ma ai ba son zuwan shi nake ba shi ne yake zuwa ai”

Na fada ina kuka daman tuni na fara kukan.

“Toh yanzu sai ki tashi ki je ki ji abun da zai fada miki”

Na mike tsaye ina jin kamar na ce Mama ta raka ni mu je, cikin rashin kwarin guiwa na fito BQ na nufi apartment dinshi kai tsaye domin a can ya ce na same shi be ce bangaren Hajiya Jamila ba, kamar kazar da kwai ya fashewa haka na isa kofar na kwankwansa shiru ba a ce min komai ba na sake kwankwasawa sai sharar kwalla na ke nan ma ban ji ance ki shigo ba, sai na murda kofar na tura a tare ta bude sai da na fara lekawa kamar wanda zata yi sata karaf muka hada ido da bawan Allah dake zaune kan cushion hannunshi rike da waya, da sauri na koma na rufe kofar sai na ji wani sabon kuka ya taso keyar ido na gaba, ko kadan bana son na yi laifi da zai saka ya ga kamar na taka mashi dokar gida ko kuma yace zai sallame mu daga gidan domin zai zame min wahala ne a yanzu saboda na saba da ďana. Na kwankwasa ba a ce min komai ba sai na sake bude kofar na shiga na kuma ki yardar na kalli inda yake zaune.

“Karaso nan”

Sai na ji kamar yace zo nan na dake ki duk da na san na wuce duka a yanzu, haka na tafi ina ta kuka kadan kadan na zauna a kasa ina yarfar da hannu, shiru ban ji yace min komai ba dago kai na yi na kalleshi sai na ga ni yake kallo a take na fara ba shi hakuri.

“Dan Allah ka yi hakuri.”

“Dukanki aka yi”

Na girgiza kai alamar a a.

“Marinki aka yi?”

Nan ma kan ma girgiza mashi.

“Toh miye na kuka?”

“Fada zaka min”

Na fada cikin kuka marar sauti, murmushi na gani a fuskarshi.

“Miye alakarki da wannan mutumen ina yawan ganinshi a gidana”

Ban yi mamakin ya ce yana ganinshi na daman Dr Hamid da Hajiya Jamila sun fada min akwai camera ko'ina a gidan.

“Ba ni da wata alaka da shi”

“Karki min karya Zahra i respected you so much ina kamar ba laifinki ba ne, wannan ya sa na ke daga miki kafa”

“Kawai abokin tsohon saurayina ne”

“Tsohon saurayinki ko tsohon mijinki?”

“Saurayi dai”

“Mutumen da ya saka aka rushe muku gida?”

Na daga mishi kai.

“Anyway bana son na sake ganinshi a cikin gidana karka sake ganinki tare da shi har sai kin bar gidan nan, karki koya kanki tsayuwa da maza kala kala ďanki ya bude ido ya fahimci mahaifiyarshi na da samari barkatai”

idona kamar za su yi magana haka suka yi bayan wacan lokacin a yau ma mijin Hajiya Jamila ya sake min wata magana mai fasa kwakwalwa.

“Dana kuma...”

Na tambaya hantar cikina na kadawa.

“Ina nufin Amir”

“Ba ni na haifi Amir ba Yallabai”

“Ni ma ban ce ke kika haife shi ba, haka dai nake ganinshi kamar ďanki saboda kina kula da shi kuma kuna kama sosai”
Chapter 70 · 0% Book details