Sashe 21
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Not for him, for your baby i just want to let you know that idan kina bukatar wani abu ko wani taimako I'm here for you”
“Allah ya raba ni da neman taimako gurin wulakantacen mutun irinka, na yi na daya kuma ba za sake ba har abada”
Na juya na cigaba da tafiya zuciyata na mini wani irin zafi marar misaltuwa, haka na bi hanya ina tafiya ina hawaye daga asibitin zuwa gidanmu akwai nisa sosai amman a kafa na taka har gida saboda bakincikin da ya zame min biyu a yau, bakincikin rashin saurare da Dr Hamid yayi da kuma ganin Abiey da na yi a yau wanda shi ya fi ko wane bata min rai. Kamar wanda talauci yayi ma mugun kamu haka na shigo gida domin na rame sosai ga lafiya bata isheni ba ga kuma kuka da na sha, ga kuma tafiyar kasa da na yi sai kashi ya game min. Ina shigowa na fadi kwance saman tabarma sai hawaye suka fara taruwa a idona. Mama na ganin haka ta taso daga inda take zaune tana alwala ta karaso kusa da ni ta taba ni.
“Zahra?”
“Mama ban samu magana da Dr Hamid ba, tun a lokacin da na tafi be saurare ni awa biyar da ni ina jiransa daga karshe da ya fito ma rufe ni yayi da fada”
“Saboda?”
“Ban sani ba, be ma saurare ni balle ya ji abun da ke tafe da ni”
“Zahra...”
Na kalleta sai ta ce.
“Tashi zaune”
Na tashi zaune sai na jingina da kujerar dake bayana ta zaman tsakar gida.
“Kin san dai ni mahaifiyarki ce ko? Ba zan baki gurbatacacciyar shawara ba?”
Na daga mata kai.
“Ki yi hakuri ki karbi wannan kaddara da hannu biyu, ki barwa Allah komai, da be rubuto miki haka ba da komai be faru ba, ki cire yaron nan a ranki”
“Mama so nake na sake ganinsa ko sau daya ne, wata kila shi ne ganina na karshe”
“Ki cire wannan a ranki, ka rasa rai ma ka hakura balle wannan da kika san yana raye? Kuma a inda zai samu kulawa mai kyau? Dan Allah ki kwantar da hankali ni ma nawa hankalin ya kwanta kin ji Yata”
Na daga mata kai na lumshe ido ina hawaye.
“Zan gwada Mama Allah yasa zan iya”
Ya rumgume sai na fashe da wani irin kuka mai taba zuciya.
“Mama na ga Abiey”
Na fada cikin kukan da nake.
“A ina?”
“A can Mama na tsane Shi”
Bata ce min komai ba ta cigaba da rarrashina har na samu natsuwa.
ABIEY POV.
“Ka yi magana da ita?”
Dr ta tambaye ayayinda suka jero suna tafiya.
“Yeah but...”
Sai kuma yayi shiru.
“Ni fa tun dazun kai na tsaya jira and you keep telling me kana cikin asibiti nan all this while baka shigo ba”
“Ina shigowa na zan wuce na hangota tana ta safa da marwa i hide somewhere ina ta kallonta you have no idea i feel right now God i love that girl, i love her so much...”
Dr ta girgiza kai tana murmushi.
“She even called my name Abiey.... And she nailed it”
“Just like that tace Abiey”
“Tace what now Abiey? But tana cikin damuwa sosai na ga damuwa a idonta kuma na ga kaunata a idonta”
“Idonka sun maka karya bana tunanin zaka ga kaunarka a idon Zahra a halin yanzu ban sani ba dai ko gaba maganar damuwa ita kam na yarda 100% tana ciki saboda ta rasa mijinta couple months yanzu kuma ta rasa babynta”
“He's not more her miji, kuma wannan tsanar da kika ganin Zahra na min soyayya ce and her first love, Zahra ba zata taba manta rayuwar da muka yi ba, ba zata taba son wani kamar yadda take so na ba, na yarda tana son Deen but not as much as she love me”
Wannan karon Dr tsayawa ta yi kallonsa sai yayi murmushi.
“Ina son sanin wanene likitan nan kuma me take nema a gurinsa har yake nuna mata yatsa”
“Wane likita?”
“Ban san shi ba, ban ma taba ganinsa ba sai yau”
“Don't tell me you're jealous?”
“I have a right to, but it's not about that it's about pointing his finger on her face”
“To sannu baban soyayya, yanzu fada min miya kawo ka a gurina?”
“Daman ina son na ce ki je ki bincika min lafiyarta ne, but yanzu ba zan sake saka kowa ba i will go by myself, saboda na gane zuciyata tana kirana izuwa gareta ne kai tsaye, abu na biyu na yi magana da Yasmin amman ina son ke ma ki yi na san tana jin maganarki kuma zata fi fahimtarki, so nake tsakanin yau zuwa gobe a lalata maganar nan”
“Bata saurareka ba ne?”
“Ta saurare ni mana na shiga gidan....”
Dr ta yi murmushi bayan ta gama sauraren yadda Abiey yayi da Yasmin.
“Zan yi magana da ita you can rest now”
“Thank you”
Ya furta sannan ya saka hannunsa aljihu yana lalaba keys dinsa, a gurin ya barta tsaye ya nufi gurin da ya faka motarsa domin gurin da nata motar yake aje daban da inda kowa ke ajewa. Farinciki ganin Zahra da yayi a yau ya saka shi manta duk wata damuwa da yake ciki.
“You look beautiful when you are looking at me”
Ya furta yana murmushi kallon tsana take masa amman a gurinsa kallo ne mai muhimmanci da ace bata kaunarsa da yanzu ta manta komai da ya faru ta masa magana kamar ba au taba samun matsala ba, but ta kasa mantawa saboda ta kasa cire sonsa a zuciyarta.
“Let give love another life”
Ya furta yana shafa kansa, a maimakon ya tafi gida sai ya juya motarsa zuwa unguwarsu Zahra, ya faka motarsa nesa da gidansu sosai ta jingina da kujerar motar yana hangen gidansu sai ya samu kansa da murmushi yana tuna lokacin da yake fakawa ta fito da gudu wani lokacin saboda ta saci kafa ta shige motarsa ya dauke zuwa wani gurin ko gurin Ammy.
“I missed those days, i miss you Zahra so much”
Sosai ya kurawa kofar gidan ido yana jin kamar ya sallama ta fito. Ya dora hannunsa kan karjinsa saitin da inda zuciyarsa take yana sauraren yadda take buga masa. Ya dade a gurin kamin ya hango ta ta fito ta hanyar dake facing din inda ya aje motarsa sai dai bata san shi ba ne saboda bata san shi da wannan kalar motarta, gaba daya kuma hankalinta baya jikinta balle zuciyarta ta raya mata zai biyo har ta tsaya kallon ko'ina ta hango shi, tashi yayi zaune da sauri yana kallonta har ta shige cikin gidan.
“Bukata ta biya”
Ya furta kana ya yi reversed ya juya motar ya fita daga unguwar ya dauki hanyar gidansu Ammy.
ZAHRA POV.
Bayan sallah Isha'i ina zaune bayan Mama dake sallah Baba ya shigo, na gyara zama na gaishe shi ya amsa ya zauna kusa da ni yana aje ledar dake hannunsa.
“Lemu ne bude ki gani idan zaki iya sha”
Kallonsa na fi sai na yi murmushi duk da kasancewar ba lallai ne ya gani ba, domin babu nepa a gidan sai hasken fitilar da aka juya kanta zuwa kofar waje. Hausawa suka ce kamar kumbo kamar korensa, salinsa sak irin na ďansa haka Deen yake min baya som shigowa gida ba tare da ya riko min komai ba, ban ankara ba na ji hawaye suna sauko min.
“Sannu da zuwa”
Na ji Mama ta fada sai na share hawayena na ina jin zuciyata tana min wani iri.
“Na gode Baba, ya Hajiya?”
“Lafiya kalau take, na yi magana da wanda zai kawo rago jibi idan Allah ya kai mu mahauci shi zai yanka ya gyara...”
Yana rufe baki wayar Mama ta yi ringing alamar kira, sai na ga Mama ta yi saurin yanke kiran.
“Zahra ina kawarki Hameeda ce ta yi flashing duba ki ga idan akwai kudi sai kirata”
Na karba ba dan na san ina da kawa Hameeda ba kuma ban fahimci Dr Hamid ne ya canjawa suna ba har sai da na duba kiran.
“Eh bari na kirata”
Na tashi da sauri na nufi daki na bar Mama da Baba a waje, ina shiga na kuma can karshen dakin na zauna a kasa na rage muryar wayar sosai kuma na yi kasa da tawa muryar saboda kar a aji na kira shi. Ringing daya yayi picking.
“Hello”
“Hello”
Ni ma fada ba tare na san da wace kalmar zan biyo baya ba, domin shi ya kira ni ba ni na kira ba ban kuma manta da wulakancin da yayi min dazun ba.
“Zahra”
“Na'am”
“Ya gida?”
“Lafiya Kalau”
“Na kira kika yanke”
“Eh wayar ta Mama ce daman line na na saka a ciki, kuma ka kira a lokacin akwai mutane shiyasa aka yanke kiran”
“Yanzu fa? Allah yasa ke kadai kike”
“Na kebe ni kadai a yanzu”
“Ki yi hakuri da abun da ya faru a dazun, ina cikin bacin rai ne sosai shiyasa”
Magana yake min ba kamar ba shi ne ya fusata sosai dazun ba akan abun da ban san dalili ba
“Amman ya kuke da Abiey?”
“Ka san shi ne?”
“Fitaccen mutum ne, zai yi wahala wani yace miki be san shi ba”
“Mun yi zama makota da shi ne”
“Kawai?”
“Eh”
“Okay....”
Ya amsa kamar be yarda ba, sai kuma ya ce.
“Anyway dazun me kika zo yi a gurina”
“Ba komai”
Na amsa domin ban ga amfanin fadin matsalar a yanzu ba.
“Am.. Uh.... Yaron nan... Idan aka ba shi nono yana saka shi ciwon ciki...”
Faduwa gabana yayi sai na mike tsaye da sauri ina dafe da kirjina.
“Miya faru? Miya same shi?”
“Ina son na tambaya ko ki bashi wani abu ne lokacin da na bar miki shi a asibiti?”
“Wallahi ban masa komai, taya zam cutar da ďana”
“Ba maganar cutarwaba ce ina nufin ko kin ba shi wani abu da zai saka shi gurbacewar ciki?”
“Ban masa komai ba”
“Idan kin san kin yi ki fada so that a samu mafita tun wuri karki je ki kashe shi”