Sashe 60
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fada da sauri tana kama hannun Mama tana mata godiya har da kukanta.
“Na gode Allah ya biya muku bukatunku na alheri ya raya”
Ta taso ta rumgume kamar zata hadeye ni a cikinta tsabar murna.
“Amman dan Allah ina rokon wata alfamar ku yarda ku koma gidana a yau din nan ko kuma gobe idan da hali”
“Yau kuma?”
Ta amsa min da sauri Mama ta ce.
“Kin yi magana da mijinki ne?”
“Aa be san komai a kai ba, mijina baya son mai aiki amman na san zai amince da Zahra a matsayin mai aiki saboda ta taba taimakonshi, yanzu ma zan mashi karyar cewar an rusa gidanku ne ba ku da gurin zama shiyasa na baku bq ku zauna, idan na fada mashi kamin ku dawo zai iya cewa na bari a siya miki wani gidan, domin yana neman hanyar da zai saka miki da abun da kika mashi ne shiyasa yake ta yawan tambaya ta ke da inda za a same ki ni kuma na mashi karya cewar matar data kawo min ke bata sake dawowa ba, kuma ban san halin da kike ciki ba na fada mishi cewar kin tafi zaki dawo amman baki dawo ba, kuma zuwanki a yau ko gobe zai taimaka min a fasa zuwa asibitin”
“Sai dai zuwa gobe, amman yanzu zan shiga da ke ki gaishe da mutanen gidan su sanki kuma na fada musu kudirinki tun a yau”
Mama ta fada a take kuwa ta amince bayan ta fada mana cewar zata aiko mana da motar da zata kwashi kayanmu. Babu inda Mama bata zagaya da ita ba cikin gidan ta fada musu abun da ta yi mana cewar ta ba mu gurin zama a gidanta, sai dai Mama bata fada musu ko matar waye ba, su ma kuma ba su santa ba domin ba fita take ba kuma ba wata fitattaciyar mace ce ba da za a ce kowa ya sani, mijinta ne fitacce shi ma kuma wasu sunanshi kawai suka sani ba su san fuskarshi ba. Abun mamaki tun a ranar Hajiya Jamila ta aiko da motar aka kwashi kayan mu da suke can unguwar da aka rusa mana komai aka kai gidanta aka zube, sai dai ni da Mama ba zamu koma ba sai gobe da safe kamar yadda ta bukata bayan ta tsara mana yadda zamu yi idan mun shiga gidan, kowa da irin zaton da yake mana musamman makonta mu domin wasu sun yi tunanin mutumen da yayi fada da Baba ne ya bamu wani gurin wasu kuma suka ce yar uwarshi ce wasu kuma sai su tambaye mu wacece ita. Haka dai aka taya mu kwashe kayan muna mikawa mazan suna saka a mota ana ta mana tambayoyin gulma, ni dai bana iya cewa komai sai ta kama dole Mama ce take da karfin halin amsa musu ni kuma ina fama da wani irin ciwon kirji da ban taba jin irinshi ba kuma ban fadawa kowa ba. A daren daker bachi ya dauke ni saboda tunani da kukan rabuwata da Abiey wanda na tabbatar hakan shi ne alheri, bana da tsarki balle na ce zan raya daren da sallah, sai dai na dauki carji ina ta salati da istigifari har garin Allah ya waye ban samu bachi ba gashi numfashi ma ji nake kamar ba ya wadatar min yadda ya dace, sai dai bana son fadawa Mama kar na kara tayar mata da hankali tana cikin nata tashin hankalin.
Da safe bayan na yi wanka Mama ta saka Maman Mufeedat ta hada min tea amman ban iya sha ba, zuciyata sai zafi take kai kuwa kamar zai rabe gida biyu saboda ciwon da yake, ruwan sanyi na aika aka siyo min na sha na kwanta, sai ga yaro ya shigo wai ana sallama da Maman Zahra a waje, Mama ta yafa mayafinta fita bata dade ba ta dawo tace min na tashi na kintsa.
“Amman Mama mutane ba za su yi wani tunanin ba? Kowa tun da farar safiya? Ba tare da rakiyar kowa ba?”
“Ba zamu ce musu komawa zamu yi ba, zan fada musu cewar zamu je mu ga gurin ne idan mun yi magana da shi ya amince sai mu dawo mu fada musu cewar zamu koma a can din albashi idan suna son raka mu sai mu tafi tare”
“Toh”
Na amsa ina jin kaina na min wani irin tsara jiri har kwasata yake saboda ciwon da kan nawa yake, Mama ta sake fita ni kuma na tashi na dauko hijab dina na saka na saka talkamina na jingina da kofar ďakin ina jin kamar na yi ta ihu. Ganin idona a rufe yasa ta kira sunana.
“Zahra”
Na bude idon na kalleta da sauri.
“Lafiya?”
“Lafiya Kalau ina jiranki ne”
“Tunani kike yi?”
Kamar tace min fadi ki yi ta kukan rashin masoyinki haka na ji a take idona ya cika da hawaye, ai dole na yi tunani domin ina son Abiey musamman ma a yanzu, na fada a zuciyata a zahiri kuma sai na ce
“Aa kaina ne yake dan ciwo kadan”
“Bari na baki magani ki sha, ba ki ma ci komai ba Zahra”
“Ba zan iya ci ba, maybe sai mun dawo maganin ma ina jin kamar idan na sha zan iya yin amanshi ki bari sai zuwa anjima idan na ci abinci sai na sha”
Bata ce min komai ba, sai kallona take cike da damuwa.
“Mu tafi”
Na shiga gaba ta fi bayana ko da muka fito mun samu wani dan'uwanta a kusa da motar yana jiran fitowarmu ba karamin faduwa gabana yayi ba, ita kanta na tabbatar ta tsorata da ganinshi musamman da ya furta cewar zai bi mu mu tafi tare ne.
“Da dai ka hakura muje mu ga muhallin kasan masu kudin nan ba son jaye jaye suke ba, idan muka ga guri sai mu dawo a tafi tare gaba daya”
Da wannan Mama ta yi nasara ya yarda muka shiga bayan motar ni da Mama ya rufe mana direban da ta aiko jiya tare da Mai diban kaya yaja motar muka fara tafiya, kwantar da kaina na yi jikin Mama sai na ji hawaye suna min zuba, har yanzu zuciyata bata yarda ta dauki kaddarar rabuwa da Abiey ba, ban kuma san ranar da zata dauka ba, rabuwa da wanda kake so ba shi da sauki musamman ma ace mutumen yana raye, zafin rabuwar mu da nake ji a yanzu yafi wanda na ji a lokacin da ya fasa aurena, domin a wacan karon ina mashi kallon mayaudari ne a dole na koyawa rayuwata rashinshi wannan rabuwar kuma mai zafi ce wanda ta fi garwashin wuta, da zarar na tuna cewar Abiey yana raye an gina mana katanga a tsakaninmu ne sai na ji kamar na hade zuciya na mutu, da ace na san irin wannan wahala ake sha a so irin wannan zafin ake ji idan an rabu da ban yarda na karbi soyayyar Abiey ba tun farko wata kila da abubuwan da suka faru ba su ba faru ba, da yanzu ban ji wannan radadin da nake ji ba, zai dauke ni yaushe kamin zuciyata ta aminta da kadararta? Tsawon wani lokaci zan dauka kamin na saba da rashin Abiey?
“Ba zan sake son kowa ba, ba zan sake bari zuciyata ta kamu da kaunar kowa ba, ba zan yarda na sake kula kowa ba”
Na yi zaton a badini nake wannan zacen har sai da Mama ta yi magana sannan na ankara da zahiri ne.
“Hakuri ake Zahra kowa da kalar kaddararshi, ke na ki son a haka ya zo wasu a gurinsu dadi ne kuma waraka ce, ke kuma a gurinki ciwo ne”
Na fashe da kuka na saka kaina a jikin Mama, har muka isa gidan kuka nake, gidan ba bakona ba ne domin kuwa ba wannan ne zuwana na farko ba, hakan yasa ban maida hankali gurin tsari da kyau gidan ba, hankalina da tunanina sun ni nisan zango a duniyar damuwata, zuciyata ji nake kamar ta tsaya gurin daya ba bata motsa min, kaina sai sarawa yake kamar a ciki ake yakin duniya direban da ya kawo mu ne ya shiga cikin gidan be dade ba ya fito yace da mu shigo ciki, cikin karfi hali na daga kafana na fara takawa jiri na daukata har muka shiga cikin falon.
“Sannunku da zuwa ku karaso nan”
Na kalli saitin gurin da suke zaune ita da mijinta da kuma wata budurwa da ba zata wuce sa'a ta ba, wacce ta taba kai ni gurin yan'uwan mijin Jamila. Duk mutum daya a mutun hudu nake ganinshi saboda jirin dake daukata takawa nake ina tafiya amman ji nake kamar ina nutsewa a cikin ruwa, tafiya nake har muka karasa inda suke zaune a inda Mama take ganin ya kamata mu tsaya ta ja ta tsaya ni kuma na cigaba da tafiyar kamar zan fada kansu har sai Mama ta riko ni.
“Zahra lafiya kike?”
Na juyo na kalleta ita ma a mutun hudu nake ganinta bakinta ma dake motsi hudu nake ganinshi, zaunar da ni ta yi a kasa kamar yadda na ta zauna ta gaishe da mijin Jamila da Hajiya Jamilar kanta da kuma budurwar da ba zan iya shaidar sunanta ba.
“Yanzu nake mishi bayanin abun da ya faru na rushe muku gida da aka yi, na fada mashi jiya ma kun zo nan tun safe kuna jiranshi har yamma be dawo ba”
Cewar Hajiya Jamila cikin muryar magiya da tausayi irin na masu neman mafita Mama ta dora da
“Eh mun zo shiyasa ma tace zata aika yau a dauko mu idan kana gida kasancewar yau weekend, Alhaji a taimaka mana dan Allah a ba mu gurin da zamu laba cikin suturar da Allah yayi maka”
Cikin jindadi na ji muryar Alhaji Bashir yana fadar