Sashe 54
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammy ta fada bayan ta bude kofar tana kallonshi, damuwa ce da tashin hankalin da ba zai kirgu ba a fuskarshi.
“Aliyu...lafiya? Mai Martaba yayi maka wata maganar ne? Ya ci mutuncinka a ciki jama'a ko?”
Ta tambaya dan ta san abun da tsohon mijinta zai iya yi ma ďanta ne. Abiey ya dauke kanshi daga barin kallonta ya shigo cikin falon ya nufi first set na cushion ya zauna, ganin haka ya sa ta rufe kofar ta dawo kusa da shi ta zauna ta shafa kanshi kamar wani karamin yaro.
“Aliyu talk to me mana wani abun Mai Martaba yayi maka ne?”
Ba tare da ya kalleta ba ya ce.
“Tun da na taso na bude ido a rayuwata ban san wani abu soyayyar mahaifi ba, amman na san ta mahaifiya, ban san kulawa da uba na amman na san ta uwa, Mai Martaba be tana kirana ya tambayi lafiyata ba be taba cewa min Aliyu ko Abiey ka ci abinci? Kana ina yanzu? Ina zaka je? Ka ci gasa ina taya ka murna, amman ke har yanzu kina min wannan tun tasowa ta har zuwa girma na, kina son abun da nake so kina kin abun da zai bata min rai ko ya saka ni a damuwa, hakan yasa nake son ki sama da yadda kowane ďa yake son uwarshi a duniyar nan, amman a yau Mai Martaba ya ambaci sunanki ya ce kin gurbata mashi zuri'a”
Ta dauke hannunta daga kanshi ta kalli wani bangare na ďakin ta lumshe ido.
“Zuciyata ta dade tana raya min cewar ba saboda magani kawai Mai Martaba ya tsane ni ba, kuma ba zan cilasta ki fada min ba, amman ina son ki tabbatar min shim da gaske kin aikata wani abu da ya saka kai kayi a zuciyar Mai Martaba ya kasa mantawa da shi har ya tsane ni?”
[11/5, 2:07 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣8️⃣
Ammy ta tashi tsaye da sauri tana kokarin hana idanuwanta tara hawaye.
“Wayata tana ringing?”
Ta nufi upstairs, Abiey ya bita da kallo har ta fice sannan ya sauke kai yana furta.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ammy na shiga ďaki ta maida kofar ďakin ta rufe ta nufi gadonta ta zauna sai ta bashe da wani irin kuka da ita kanta ta dade bata yi shi ba, hannayenta ta saka ta rufe bakinta saboda kar kukan ya ci karfinta ya fita, bata bi ta kan wayar dake ringing ba har sai da ta samu sukunin zuciya, bathroom ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta nufo wayar ta dauka missed calls din Anty Amarya ne da na Momy mahaifiyar Yasmin, Anty Amarya Ammy ta fara kira ta dawo ta zauna saman gadon wayar a kunnenta tana gyara murya so that kar a fahimci kuka ta yi ko kuma tana cikin damuwa.
“Salamu Alaiki Ammy”
“Na'am Zuwaira ya gida?”
“Abiey ya fada miki abun da ya faru?”
Gaban Ammy ya fadi.
“Aa be fada min komai ba...”
“Ya dawo gurinki?”
“Eh amman be ce komai ba”
From a to z Anty ta labartawa Ammy hukuncin da Mai Martaba ya yanke akan Abiey Ammy tana ta saurare ta ji cewar ko a gaban Anty Mai Martaba ya furta cewar ta gurbata mashi zuri'a amman bata ji Anty ta fada ba.
“Na taso na bar su a can, ban san abub da suka tattauna ba amman na ga Abiey ya fito rai a bace kamar ma baya cikin hayyacinshi”
“Zan yi magana da shi kuma zan yi magana da Mai Martaba”
“Toh Allah ya kyauta”
“Ameen”
Ammy ta amsa sannan ta sauke wayar ta kalli kofar ďakinta Dr ce ta shigo riga da Lab coat a hannu dayan hannunta kuma rike da handbag.
“Ammy Lafiya na ga Abiey a damuwa?”
Ammy ta ja dogon numfashi ta sauke.
“Kin san ďan'uwanki kullum yana cikin damuwa, yanzu ma wata matsalar ce ta sake bullowa”
“Ni ma abun be min dadi ba, amman yace be aikata ba yanzu haka ma daga gidansu Zahra na ke na samu gidan ya zama fili kuma babu kowa a gurin na tambaya aka ce tace za su je gidan kawunsu amman su makonta ba su san ina gidan yake”
“Mai Martaba ya saka auren Aliyu da Yasmin nan da wata uku, kuma zai nada shi a matsayin Galadima nan da wata biyu, sannan ya ba shi umarni aje wasan kwallon kwandon da yake a gafe zai hannata mashi wasu kamfanonu da zai kula da su, kuma ya ce baya son ya sake maganar Zahra”
“Amman Ammy wannan hukunci be yi tsari ba? Kin san yadda Abiey yake son kwallo fa kuma kin san abu ne mai wahala ya iya rabuwa da Zahra”
“Mai Martaba baya son wasan da Aliyu yake yi kuma yana daya daga cikin dalilin da ya saka tsabani a tsakaninsu, zancen aurenshi da Yasmin kuma ya min daidai, kuma shiga tsakakaninshi da Zahra ma ya min daidai, domin hakura da juna shi ya fi, amman zan yi magana da Mai Martaba ya hakura ya bar shi ya cigaba da sana'arshi ta kwallo”
“Ammy kina ganin Abiey zai iya hakura da Zahra?”
“Ke kuma kina ganin zan iya bari tarensu da Mai Martaba ta lalace? Wannan hukunci ma da ya yake na san ba zai musu dadi ba, domin ba haka suka so, ko ba komai Mai Martaba ya nuna mashi kulawa a yanzu abun da ya kasa ba shi can baya, a yanzu da girma zai kama Aliyu da Mai Martaba ba zan yarda abubuwa su lalace ba”
“Ina tausayin Abiey sosai Ammy da dai za ku hakura ku kyale shi da Zahra”
“Be zama lallai tarayyarsu ta zama alheri ba, so da tari zaka so kuma ya zama rashinshi shi ne alheri, idan ba ayi ma tukfar hanci ba nan gaba ba mu san iya abun da zai faru ba”
“Haka ne, Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri a tsakaninsu”
“Ameen”
Ammy ta amsa sannan ta mike tsaye.
“Tsaya a nan zan yi magana da shi”
“Okay”
Ammy ta bude kofar ta fito har ta sauko downstairs idonta na kan ďanta da ya soke kai yake zaune a inda ta bar shi har lokacin. Kusa da shi ta zauna sai ya dago ya dubeta.
“Aliyu karka yi maganar nan da Yayarka kuma karka yi ta da kowa domin babu wanda ya san komai daga ni sai Allah sai Mai Martaba sai kuma Zahra da na taba fadawa, bana son ka tattaunar maganar nan da kowa saboda karka sakawa kowa hakku a rai”
Ya daga mata kai alamar gamsuwa yana jika makoshinshi daya bushe da yawun bakinshi ya runtse ido.
“Allah ya maka albarka”
“Ammy zaki iya roko min Mai Martaba ya bar ni da Zahra? Saboda ina son ta sosai kuma bana son tsaba Umarninsa, bana son na janyo abun da zai zame mana abun magana”
Ya fada ba tare da ya bude idon ba. Ammy tana ta kallon ďanta kamar ta yi mashi wata maganar sai kuma ta amsa mishi
“Zan yi magana da shi”
Abiey ya bude ido ya mike tsaye ya nufi ďakinshi, sosai hankalin Ammy ya tashi ganin yadda ya koma jiki a sanyeye saboda damuwa. Tashi ta yi ta shiga nufi upstairs, Dr dake kwance kan gadon ta tashi zaune, Ammy bata ce mata komai ba ta dauki key din motarta da mayafinta
“Ammy ina zuwa?”
“Gurin Mai Martaba”
“Amman kina ganin zai saurareki?”
“Sosai kamin ya min yanzu ba ni kadai nake tafiyar da rayuwar ďana ba?”
Ta fadar haka ta dauki wayarta Dr ma ta tashi suka fito tare Ammy ta sauka downstairs ita kuma ta shiga ďakin Abiey. Kwance ta same shi idonshi a rufe fuskarshi na fuskantar ceiling.
“Abiey?”
Ya bude ido ya kalleta.
“Magana nake son yi da kai”
Sai ya tashi zaune ita kuma ta karaso ta zauna saman gadon tana kallonshi cike da tausayawa.
“Abiey ka yi hakuri da duk yadda rayuwa zata zo maka, wani lokacin sai an jarraba bawa sosai kamin a bashi abun da yake so, na san kana son Zahra kuma baka son Yasmin tonka roki Allah ya saka maka kaunar Yasmin idan har aurenta alheri a gareka, kuma ya cire maka son Zahra idan ita din ba alheri ba ce a gareka, kuma ka yi hakuri”
Ya daga mata kawai alamar gamsuwa, it's just like kamar kalmomin bakinshi sun kare, tunaninshi ya tsaya guri daya damuwa na neman maida shi kamar lokacin da ya taba rasa Zahra.
“Na je na bincika ban samu Zahra ba, kuma na tambaya makota sun ce taje gidan kawun mamarta amman ba su san gurin ba, amman na samu an maida gurin fili”
Nan ma kai ya daga mata ya koma ya kwanta ya runtse ido, Dr ta sauke ajiyar zuciya kana ta tashi ta fice daga ďakin. Wannan karon Ammy bata tsaya jiran ayi mata iso ba, domin kuwa tun kamin ta isa Masarautar ta kira Mai Martaba a wayarta ta sanar mashi tana tafe, hakan yasa ta faka a harabar apartment dinshi ba na Anty ba kamar yadda ta saba, ta fito ta nufi katuwar kofar kusan ko wace kowa a bude ta same ta har kofar falonshi da yake ciki yana hutawa. Da sallama ta shiga sai ya dago ya dubeta Mama Lami ta kalleta ba tare da ta amsa ba.
“Wa'alaikissalam”
Mai Martaba ya amsa mata da kanshi, da mamaki Mama Lami ta kalli Mai Martaba sannan ta sake kallon Ammy tana dariyar kyaƙe.
“Sannu da zuwa Hajiya Umaima”
“Sannu dai Lami ya aikin kula da Mai Martaba?”
“Alhamdulillah sai kace karamin yaro”
Cewar Mama Lami tana dariya sai Ammy tace
“Ai a gurinki ba, ba mu guri zan yi magana da Mai Martaba”
Mama Lami ta kalli Mai Martaba sannan ta mike tsaye ta fice tana jin kamar ta tsaya sauraren dalilin zuwan Ammy sai dai ba dama domin Ammy ba kanwar lasa ba ce ba irin Anty Amarya bace, duk da dai ta san maganar ba zata wuce ta hukuncin da Mai Martaba yayi ma Abiey ba. Ammy ta tsaya kallon Mama Lami har sai da ta fice sannan ta juya ta fuskanci Mai Martaba dake kokarin cire gilashin dake sanye a idonshi.
“Ina son mu yi magana ne akan Aliyu”