← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 127

Sashe 121

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi saurin daga jikinsa ta kalli fuskarsa sai ya kashe mata ido daya.

“Kin san Anty ta saka mana ranar tarewa?”

“Yaushe?”

“Cikin satin nan, Mai Martaba ma yayi min magana yace ya kamata na tare kamin a yi nadin sarautar”

“Aa ni ban shirya ba”

“Haba Hiayatee me zamu jira kuma? So nake Mama ta tare a sabon gidan da aka gina da yake kusa da na Baba, ta koma tsohuwar unguwarku saboda ta saba da can da mutanen ciki, idan Mr Bashir ya baku gidan idan haya zaku saka ko ki aje sai ku yi haka, but for now Mama gidana zata zauna, mu kuma zai mu tare a jibi”

Ta lake kafada daya tana masa abun da ya ke kara rikitashi wato shagwaba.

“Aa ni ban shirya”

Hannunsa ya mika ya janyota.

“Ni ban ce a shirya min komai ba, Inda zaki zauna za a zuba komai a ciki, lefe ne kawai zamu hada da kan mu, idan an gama nadin sarautar sai mu tafi siyayyar a kasar da kike so ki hada lefenki da komai a can”

“Aa ni dai”

“Haba Babe ya kike son na yi ne? Ba ki san ina cikin mawuyacin hali ba? Kuma kin ga Anty zata ce ba ki ji maganarta ba, Mai Martaba ma zai ce ba mu ji shawararsa ba”

“Sai na yi magana da Mama”

“Shikenan, idan baki ra'ayin tarewar a yanzu ba zan cilastaki ba, amman babu abun zai rage ni da shi ina son ki san wannan”

Ta dago ido tana kallonsa

“Me kake nufi?”

Ya hura mata iska a idon yana murmushi.

“Abun da zuciyarki ta raya miki”

Cikin rada ya bata amsa yana goga mata hancinsa kamin ya sauke bakinsa a kai ya fara tsotsar hancin nata.
[12/9, 5:32 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣3️⃣

Ba dan ya so ba ya barta ta fita motar ta shiga gida, ya dade a cikin motar kwance domin jikinsa ya gama mutuwa gaba daya, sannan ya juya motarsa ya nufi gurin Ammy. A inda ya saba parkin ya faka motar ya fito ya shiga ciki, yana shigowa falon ya samu Dr da Ammy suna lunch, Dr sai zolayarsa take wai ango Ango, murmushi kawai yayi ya shige dakinsa sai da yayi wanka ya shirya sannan ya fito, wannan karon akan sofa Ammy take zaune domin ta gama cin nata abincin, Dr ce kawai zaune a kujerar tana ta ladawa, kujera yaja ya zauna ya dauki plate ya fara zuba ma kanshi.

“Dr kullum kika zo gidan nan sai kin ci abinci”

Wani kallon uku saura kwata ta yi masa

“Hana ni cin abincin ni da gidanmu, kai na ai ka kusa daina cin abinci”

“Aa ba wannan ranar”

“Idan matarka ta tare ai dole ka dauke mana kafa ko?”

Cewar Ammy tana dariya, juyawa yayi ya kalleta.

“Ammy ai kin san Matata bata iya girki ba, kuma ni bana son Mai aiki ni zan rika yin wanke wanke da shara, sai ki rika mana girki na zo na dauka ko ki aiko mana”

“Hmmm Allah ko? Ashe kana da aiki, to Wallahi ka fada mata ta koya tun yanzu domin ba zan yarda Ammy ta yi muku wannan wahalar ba”

Harara ya watsawa yayar ta shi.

“Ina ruwanki da shiga tsakanin uwa da ďa”

Ammy ta ce.

“Da gaske ne fa, in dai ba wai auren nan da ta yi ta koya ba, Zahra bata iya girki ba, amman dai ga Yasmin ai ta isheku da dai ita kam na san mahaifiyarta ba zata yarda ta kai gidan miji bata iya girki ba”

“Au wai aurenka da Yasmin yana nan?”

Dr ta tambaya yana kallonsa ya daga kafadunsa.

“To ya zanyi, tun farko ta dage sai an yi abun nan, gashi nan tana son rusa mana jindadi ni da Zahra”

Yana aje numfashi Ammy ta karbe tana fadin.

“Aa babu inda ta rusa muku jindadi fa, ita ma kanta take yi ma yaki, kuma ai ta riga ta fadawa Iyayenta cewar tana son a fasa auren amman suka ce hakan ba zai yiyu ba saboda sun riga da sun amincewa Mai Martaba, yanzu haka Anty tana nan tana ta hadin lefe”

“Ni kam da dai zaka bi shawarata da ka samu Mai Martaba ka yi masa bayani domin a yanzu yana fahimtarka ai, sai ka nuna masa kai fa baka son Yasmin, saboda ka samu Zahra ne ya saka ka yi kara da ita, saboda kar bayan aurenku ka zo abu yana damunka”

Abiey ya kalli Dr yana nazarin maganarta.

“Ni ma ina tunanin haka, har ina ganin kamar Yasmin zata fi Zahra zafin kishi ma, kuma na san Zahra ba zata jidadin zama da kishiya ba, amman sai nake ganin kamar Yasmin ba zata jidadi ba idan na yi haka, kuma mahaifiyarta ma ba zata jidadi ba, shi kan shi Mai Martaba zai zama kamar na cilasta shi ne ya aikata hakan, domin da ace yayi ra'ayin janyewa da ya janye ko kuma yayi min maganar da kansa”

Ammy ta taso daga inda take zaune ta dawo kusa da ďanta ta zauna.

“Aliyu, indai har kana jin kaunar Yasmin ko kadan ne a ranka to ka yi hakuri da ita ka aureta a haka, domin idan har ka janye maganar auren nan bata kyauta mata ba ni da mahaifiyarta kuma ba zamu jidadi ba, sannan baka san tanadin da Mai Martaba yayi ba wannan bikin naka, ka ga ka riga ka daura aurenka da Zahra a sirrance ba kowa ya sani ba, sannan wasu bukukun da ya kamata ni da mahaifinka mu gabatar ba zamu samu wannan damar ba, amman a aurenka da Yasmin zamu samu wannan damar mu yi bikin da zai amsa sunan biki, kuma ina tabbatar maka idan ka auri Yasmin zaka jidadi domin tana da tarbiya ga ilmin addini, sannan zaka rage wani abun kamar ta bangaren girki da ka fada, wata kila ganinta zai saka Zahra ta maida hankali ita ma ta iya, sai dai fa karka yarda son Zahra ya saka ka zalinci Yasmin, kuma karka nuna musu banbanci kyautatawa ce kawai ba zan cilasta ka ka yi ma wata ka hana wata ba, dole wannan wanda ka fi so ko kuma wanda ta fi kyautata maka kai ma ka kyautata mata, kuma ban baka shawarar ka aje su a gida daya ba, domin kazantar da baka gani ba tsabta ce inji hausawa, idan daya bata ganin daya an fi marmarin juna, kuma wata soyayyar da zaka nunawa daya ta banbanta da wata ba lallai ne dayar ta sani ba, sannan karka yarda ka nunawa Zahra ka fi kaunarta akan Yasmin haka ma karka nunawa Yasmin ka fi kaunar Zahra akanta, kuma karka wulakanta ko wace, kar ka daya wata ta zagi wata a gabanka, karka aikata irin kuskuren da mahaifinka ya aikata wanda ya haifar mana da matsala a yanzu”

Ya jinjina kai cike da gamsuwa da shawarwarin da Ammy ta ba shi.

“In'Shaa Allah, Allah ya ba ni ikon yin haka, amman abun nan ba sauki, ni ban ma taba sammanin zan iya zama da mace sama da daya ba”

“Daman haka rayuwa take, kana nata Allah na nashi, dukam mu ba mu yi tsammanin haka ba, kai dai ka yi ta godiya ga Allah na yadda abubuwa suka zo maka da sauki kuma cikin farinciki da jindadi”

“Ina ta yi kuma zan kara i love you sweet Mom, Amman ina son na fada miki Zahra ta barwa Allah Mr Bashir Amir”

Abiey ya karasa yana kallon Dr dake murmushi domin ta san da labarin, Ammy kuma da take jin labarin wani banbaragwai ta zaro ido ta rufe baki.

“Ya sanar yana ra murna, ya fada a yanzu har ya fi jin kaunar Amir fiye da baya, ta yi abu mai kyau domin ta rufa masa asiri kuma shi ma ya cancanci haka, ya kira ni da kansa ya fada har ya nemi na zama mai rike masa sirrinsa”

“Amman Zahra ba ta yi tunani ba, anya kuwa da sanin mahaifiyarta ta aikata wannan abun?”

Abiey ya kalli Ammy dake tambayar.

“Da saninta ta aikata, ita ma ta bata shawarar yin haka wai suna tunanin haka zai fi saboda tana tsoron kar labarin ya fita ace ita ta aikata, kuma tace min yaron ma kuka yake idan ta rabe shi ya fi sha'awar zama a gurin Mr Bashir din, and Ammy kin san indai yaron nan yana hannun kakaninsa ko gurinmu hankalina ba zai kwanta ba, domin Zahra zata tattara hankalinta gaba daya ta maida gurinsa ne, ba dan abun da ubansa yayi ba da yanzu ďana ta haifa ba Amir ba”

“Kai dai Abiey kana ta kishin mutumen da bashi raye, ni fa har yanzu ina ganin Deen ya aikata abun da ya aikata ne saboda yana son Zahra, kamar yadda ka aikata abun da ka aikata a yanzu wanda na tabbatar da ace Mai Martaba da Ammy tsine maka albarka za su yi zaka yarda ka sauki wannan”

A take ran Abiey ya bace da maganar da Dr ta yi.

“Daman ai kina goyon bayan abun da ya aikata shiyasa ba ki ganin laifinsa, and that's why i hate him so much wannan Amir din ma ba dan Zahra ba da babu abun da zai saka na kula shi, domin jinin makiyina ne”

Ammy ta ce.

“Yanzu ai komai ya wuce tun da shi ya bar duniyar kuma ka mallaki Zahra a yanzu me ya rage, gashi Allah ya kara maka da Yasmin zaka auri budurwa kai ma ayi maka wanka lalle irin yadda ake yi ma kowa”

Mikewa yayi tsaye ya fice daga dinning.
Chapter 121 · 0% Book details