← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 127

Sashe 51

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba kira ne neman jin lafiya kadai ba domin bata taba mashi makamacin irin wannan kiran ba, labarin abun da ake zargin ya aikata ya je mata a kunnenta sai dai bata san taya zata fuskance shi da maganar ba, me zata ce mashi? Zuciyarta na raya mata Abiey ba zai iya aikata hakan ba musamman a lamarin abun da ya shafi Zahra, to waya aikata? Kuma miye dalilin aikatarwa? Sosai take jin damuwa domin hakan ya taba martabar gidansu da kuma kimarshi, duk wanda ya aikata haka yayi ne domin neman bata mashi suna da taba darajar gidansu, lura da yadda kowace gidan jarida suka yi na su shimfidar labarin, comments din mutane kowa da kalar fararsa da yake mashi har da masu cewa Zahra kasuwarshi ce, wasu kuma su ce neman lalata mata rayuwa yake, sam abun be mata dadi ba.

“Lafiya ta kalau na gode da kulawa”

Ya amsa mata bayan yaja dogon numfashi ya sauke.

“Mu wuni lafiya”

Ya kasa furta komai har ta yanke wayar.

“Oh Ya Rabbi Allah”

Ya fada yana jin ina ma be aikata ba, yanzu a wane hali Zahra take ciki ita da mahaifiyarta? Nunberta ya sake gwadawa aka tabbatar mashi da wayar a rufe take har lokacin, hakan ya saka shi yanke shawarar kiran Dr Zainab yayinda yake kokari kunna motar. Ringing biyu ta yi kamin ta yi na uku ta dauka.

“Abiey na kira baka daga ba kana da abun da yake faruwa kuwa?”

“Na san komai Dr”

“I don't want to ask you amman...”

“Ban aikata ba, all what i know is na saka a kama mutumen yau da safe kawai sai ga yan jarida a gidan nan suna min tambayoyi Sauban kuma ya turo min hoton da ake ta yadawa a media, ban san wanda ya rusa gidan ba, ina ta kiran number Maman Zahra bata shiga, that's why i call you alfamar nake son ki yi min ki je gidansu ki bincika min saboda Ammy tace kar na je da kaina”

“Ni ma ina gidansu Mr Bashir Auta idan na fito gida zanje, amman zan bincika gurin Zahra”

“Thank You”

Ya saka wayar aljihunsa sannan ya yi ma motar key, tun kamin ya isa masarautar gabanshi ke mugun faduwa kanshi har sarawa yake. Lokacin da ya isa masarautar bangaren Anty Amarya ya fara shiga yana kokarin hawa upstairs ya ji motsinta a kitchen tana magana da Aisha, sai ya sauko ya nufo kitchen din bakin kofa ya tsaya ya jingina da kofar, Anty dake aikin gyara allayahu ta juyo ta kalleshi cikin yanayi na damuwa.

“Ina ta kiranka baka daga ba”

“Anty idan na daga ma ban san me zan ce ba”

“Mai Martaba yana son magana da kai”

“Ya kira Ammy”

Anty ta matsa kusa da shi.

“Ka yi hakuri da duk abun da Mai Martaba zai fada maka, kuma karka musa mashi, kuma ina fatar baka aikata”

“Ban rushe gidan ba, amman na saka an kama mutunen”

“Wani lokacin muka bukatar taka tsantsan saboda mutunci da kimarmu, Abiey da zaka hakura da yarinyar nan wata kila shi zai fi zama alheri, ina ta son na maka magana akan karka tunkari Mai Martaba da maganar nan har sai abubuwa sun daidaita sai gashi wannan abun ya faru”

“Ko da ba yanzu ba dole ne na sanar da Mai Martaba, ni kaina ban jidadin yadda labarin zai riskeshi a yanzu ba, amman dole zai sani domin aurenta nake son yi ba zaman banza ba”

“Yanzu dai mu tafi kar yace ka bata mashi lokaci domin dazun a tare ya tara mu gaba daya yace na kira ka yana son magana da kai”

Aisha dake gafe tsaye ta tabe baki.

“Allah kadai ya san wanda ya isar wa Mai Martaba da labarin nan, kuma wannan abun ma akwai wanda ya shirya haka”

Anty Amarya ta juyo ta kalleta.

“Ko ma dai minene ya riga da faru, sai a kiyaye gaba, amman Abiey ka yi maganar nan da wani ne?”

Anty ta karasa tana kallon Abiey.

“Babu wanda na fadawa sai ke, Ammy ma sai a yau take samun labari Sauban ma ban fada mashi ba”

“Ni fa gani nake kamar Siyama ta fitar da labarin nan, saboda lokacin da ka shigo ka zauna kana magana a waya tana falon nan muna duba Lace din angon Zubaida, na lura hankalinta gaba daya yana kanka kuma ta ji komai”

“Ko da ta ji ai sai dai ta kai labari”

Anty ta kalleshi tana murmushi.

“Baka san halin makiyi ba Abiey, za su iya riga Malam Masallaci su aikata saboda a bata tsakaninka da Mai Martaba kuma a bata maka suna, daga Mama Lami har Hajiya Kilishi sun san gidansu Zahra kuma sun san abun da ke tsakaninka da Zahra”

“Amman ba su san Zahra bata da aure ba”

“Ai kamar ka bata labari ne, saboda ka yi maganar a gaban Siyama kuma mai son abun ka ya fika dabara, kai ma kuma an koya maka darasi domin ba a magana a gaban makiyi musamman irin wannan”

“Ban kula ba ne saboda na shigo raina a bace, kuma ban yi tunanin wannan maganar zata saka ayi wani abu ba”

“Ko daga yanayin yadda aka rubuta labarin ai kasan biyansu aka yi kuma am ba su labarin abun da ya faru ne, idan ba haka ba daga faruwar abu jiya jiya ace yau har ya shiga media”

Hannayenshi ya saka Aljihu ya juyo suka fito tare da Anty suna tafi suna maganar har suka isa bangaren Mai Martaba, zaune suka same shi karamin mayafi a kafadarshi kanshi sanye da tsadadiyar hula ya dora kafafuwanshi akan tuma kasa (Titimi) kofin Shayi na gafenshi hannunshi kuma rike da waya har biyu.

As usual Anty ta yi sallama, Mama Lami dake zaune kusa da kujerar Mai Martaba ta amsa mata, kallo daya Abiey yayi mata ya dauke kai ya zube a kasa ya kwashi gaisuwa Mai Martaba ko kai be dago ba balle ya amsa mashi, Hajiya Lami ta mike tsaye sai Mai Martaba ya daga mata hannu yayi mata alama da ta zauna, sannan ya kalli Anty.

“A kira Hajiya Kilishi”

“Toh”

Ta amsa sannan mike tsaye ta fice, Abiey dai yana zaune a gurin kanshi a kasa. Anty bata jima ba ta dawo tare da Hajiya Kilishi suna tafe suna hira sama sama, a kujera daya suka zauna daga Hajiya Kilishi har Mama Lami kallon Abiey suke suna kallon junansu alamar gulma na cinsu Anty kuma idonta na kansu.
Mai Martaba ya dauki tsawon lokacin ba tare da yace komai ba, har sai da ya gama abun da yake da wayarshi sannan ya mikawa Abiey wayar, Abiey ya kalleshi tare da mika hannu ya karbi wayar, hotunan labaran abubuwan da suka faru ne da hotunanshi.

“Miya kai ka unguwar?”

Kamar saukar aradu haka Abiey ya ji saukar tambayar Mai Martaba a kunnenshi, be taba jin tsoron amsa wata magana kamar yadda yake ji a yanzu ba.

“Akwai wata yarinya da na yi nema shekara biyu da suka wuce, an mana baiko da ita domin ka san da maganar sai dai lokacin kana fushi da ni shiyasa baka saka hannu a ciki ba, sai su Baba Waziri ne suka yi komai, to mijin da ta aura ya rasu tana gidansu a yanzu shiyasa na je”

Hajiya Kilishi da Mama Lami sun kalli juna.

“Kana da wata alaka da yarinyar ne?”

Abiey ya hade yawun bakinshi.

“Ina son.. Ta... Ne Mai Martaba kuma ina fatar aurenta”

“Ita ce yarinyar da muka nema maka aurenta?”

“Allah ya baka yawan rai, ba ita ba ce amman ita ce yarinyar da na ke so?”

“Ita kuma wacan fa?”

Sai ya sauke kai kasa ya kasa amsawa, wata kila idan yace yayi haka ne saboda kar Mama Lami ta hada shi da yarinyar zai bata ran Mai Martaba domin zai ce yayi wasa da hankalinshu ne.

“Magana fa ake maka Baba”

Cewar Hajiya Kilishi, Anty ta kalleta tana dan murmushi domin ta san an sosa mata inda yake mata kaikayi ne. Abiey ya dago jiki a sanyaye

“Mai Martaba Zahra ce yarinyar da nake so kuma nake fatan aure”

“Ita kuma wacan ba aurenta zaka yi ba kasa na nema maka aurenta? Ko kuma zaka auri mata biyu ne dayar a boye?”

“A gafarce ni Mai Martaba na yi kuskure kuma ina son na fada maka maganar Zahra ban samu dama ba ne”

Mai Martaba ya gyara zama fuskarshi babu annuri ya ce.

“Soyayyar ta ce ya saka Mahaifinta yace ka daina zuwa kofar gidan har ka rusa mashi gida kuma ka saka a ka hukunta shi? Ko kuma saboda ka bata sunan masarautar nan ne?”

“Ba mahaifinta ba ne, mahaifinta ya rasu mijin mahaifiyarta ne kuma daman can baya so, kuma Wallahi ban rusa musu gida ba, ban yi sa'insa da shi ba, ban kuma saka a kama shi ba akwai dai wanda ya shirya duk wannan abun”

“Kamar wa kenan?”

Abiey ya kasa cewa komai ya sauke kai kasa.

“Zan maka wani gargadi karo na farko kuma na karshe”

Wani irin faduwa gaban Abiey yayi numfashinsa na fita da karfi.

“Kar wata alaka ta sake hadaka da yarinyar nan, domin ba zaka maida mu mutanen banza ba, ka zubar mana da kima kuma ka janyo mayo mana surutu a gurin jama'a, abu na biyu bana son na sake jin labarin zaka buga wata wasa ko ka buga, akwai kamfunan da zaka iya kula da su, zan nema maka aiki a duk inda kake so, amman bana son maganar wasanka, na uku nan da wata biyu za a nadaka Galadiman, zaka daina yawo kai kadai sai tare da fadawa, kuma surarka da mu'amalar da zata canja daga yanzu, ka kiyaye duk wani abu da zai zubar da mutuncin Masarautar nan, karka sake janyo mana wata magana ”

Kamar a mafarki haka Abiey ya ke jin dokokin Mai Martaba yana kallonshi baki da kunnen a sake ido kamar yayi magana. Mai Martaba yayi gyaran murya sannan ya kalli matanshi ya ce.
Chapter 51 · 0% Book details