Sashe 61
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Karki damu zan baku BQ ku zauna kamin a siyo muku gurin da zaku zauna saboda Zahra babu abun da ba zan iya ba, yarinyar nan ta taimaki rayuwata kuma na jidadin haka fiye da zatonku ba dan Allah ya bata iko ta taimaka min da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, kuma na jidadin da kika tuna da ni a lokacin wannan matsalar ta same ku kuma kuka nemi taimako na”
Magana yake kallonshi nake amman bana ganin mutun balle wani abu dake cikin falon gaba daya hudu ya baibaye idona maganar shi kawai nake iya ji da kuma na yarinyar dake tambayata.
“Wai daman labarin da ya karade media akan Abiey ke ce yarinyar da ake fada?”
Juyawa na yi na yi na kalli inda nake jin sautin muryarta na fitowa, da kuma ta Alhaji Bashir dake tambayar matarshi.
“Ba kin fada min cewar mijinta ya rasu ba? To wanene wannan?”
“Wannan kuma sai dai mu ji daga bakinta Hubby ni kaina ban san alakarsu ba...”
Ita ce amsar da Hajiya Jamila ta bashi kuma ita ji sautin murya ta karshe da na ji daman na dade da rasa ganina halshena kuma yayi nauyin da ba zan iya daga shi na furta ko da A ba, da wani irin karfi aka fisgi numfashina har sai da na mike tsaye na saka hannuna a kirjina ina wani irin kugi ina jin hannayen mutun biyu a jikina masu kokarin rike ni amman hakan be hana ni kai wa kasa ba ina ta kokuwa da ran dake neman barin jikina, kamar an yaye min hijabi haka ganina ya dawo farat daya wata kila ina rabon na yi ma Mama ganin karshe ne domin fuskarta na fara arba da ita tana ta jijjigani tana kuka kamin wani duhun yayi min sallama numfashi ma ya tafi ban sake sanin komai ba.
ABIEY POV.
Banbanci shi da mai jinya asibiti kadan ne, mai jinya asibiti yana samun kulawar likita a yayinda shi kuma ya kulle kanshi ciki ďaki yana jinyar zuciyarshi ba tare da samun kulawar kowa ba, domin ya ki yarda da sake da Ammy ma balle ya karbi kulawarta tun a shekaran jiya da Zahra ta yi masa furucin rabuwa, sosai yake son ya tabbatar mata cewar yana kaunarta kuma akwai banbanci a tsakanin soyayyar da yake mata da kuma ta Deen, sai dai ta dayan bangaren yana jin kamar ba zai iya ba, domin a yanzu ya fi kaunar Zahra fiye da da, sonta na fisgarshi kamar zai raba zuciyarshi da gangar jikinshi.
Kamar jiya da shekaran jiya ya wuni a ďaki yau ma a dakin ya kuduri aniyar wuni, yana kwance saman gadonshi Ammy ta shigo cikin yanayin na damuwar da ya gagara boyuwa a fuskarta, bakin kofar dakin ta tsaya tana kallonshi.
“Aliyu ka daina fitowa cin abinci, idan an kawo maka haka za a fita da shi lemu kawai kake sha sai ruwa, so kake ka jawa kanka wani ciwon ne?”
“Bana son abinci ne shiyasa ko ina son na ci bana iya ci”
“To ka tafi asibiti mana”
“Zan tafi gobe”
Har ta juya sai kuma ta juyo.
“Yasmin tana garden tana jiranka”
Ya daga mata kai cike da ladabi.
“Zan fito yanzu”
Sai da ta sake kallon kyakkyawar fuskar ďanta sannan ta juya ta fice. Mikewa yayi tsaye ya zura talkaminshi tare da daukar wayarshi ya rike a hannu ya bude kofar ya fice, kai tsaye garden ya nufa har ya isa gurin da Yasmin take zaune be kalleta ba ita ma kallo daya ta yi mashi ta dauke kai gabanta na faduwa, zaunawa yayi a dayar kujerar ita da shi aka rasa wanda zai fara yi ma dan'uwanshi magana, can dai ta daure tana wasa da hannun Hijab dinta ta ce.
“Ammy ce tace a dauko na zo na duba ka baka da lafiya”
Be ce mata komai ba sai yawo yake da idonshi a swimming pool din dake gabansu.
“Ya jikinka?”
Sai a lokacin ya kalleta
“Babu sauki kuma babu ranar warkewa, idan har zaki biye Ammy to zaki ta ta zuwa duba lafiyata ne har zuwa lokacin da za'ayi auren sai ki cigaba da jinyata har ki rufe gawata”
Ta sauke idonta kasa.
“Daman na yi zaton rashin lafiya ce irin ta mutane I'm sorry”
“You shouldn't ba laifinki ba ne, but I'm telling you this saboda ki saba tun yanzu”
“Sabawar ba mai wahala ba ne, yardar ce mai wahala, ka jefa mu a cikin matsala musamman ni zan cutu da yawa Abiey”
Tana fadar haka ta mike tsaye hawaye sai zuba suke mata ta fice daga gurin, shi kam binta yayi da kallo har ta bace mashi sannan ya cire key wayar dake hannunshi ya kira line Sauban. Yanayin yadda Sauban ya amsa wayar ya isa ya sanar da Abiey cewar Sauban yana tare da matarshi ne.
“Abiey?”
“Sauban ina son ganinka ni zan zo ko kuma kai zaka zo?”
“Kana ina?”
“Garden din Ammy”
“I will be there soon”
Abiey ya dauke wayar daga kunnenshi yana ta kallon harabar gurin da tunani kala kala a zuciyarshi, cikin mintunan da ba su wuce salatin ba Sauban ya iso gidan yana faka motarshi ya nufi hanyar garden din dake ta bude kasancewar hanya biyu ce za a iya shiga garden ta harabar gidan kuma za a iya shiga ta cikin falon Ammy. Abiey kallon abokinshi yake har ya iso ya zauna a inda Yasmin ta tashi.
“Gaba daya ka canja Abiey ka ga yadda ka rame wai? Jiya baka kai yau rama ba gobe kuma ban san ya zaka zama ba, ya kamata ka dauki kaddara baka san me Allah yake nufi da ku ba”
“Ina ta kokarin haka Sauban”
Ya fada sannan ta tashi zaune daidai yana aje numfashi a muhalin da ba nashi ba.
“Akwai wata matsala ne?”
Sauban ya tambaya domin ya ga alamar hakan a fuskar abokinshi kuma ya san Abiey ba zai bukaci ganinshi haka nan kawai ba tare da wata matsala ba, kamar yadda shi ma idan wani abun ya ta so shi gaba yake neman Abiey su warware.
“Sauban so nake na je ka nemi auren Zahra...”
Abiey ya fada mishi kai tsaye babu alamar wasa ko zolaya a tare da shi, mutuwar zaune Sauban yayi wanda ta fi ta tsaye tashin hankali da mamaki.
“Wh... Wha... What...”
Har furta har sau biyu sai a na uku ya iya hada kalmar. Wayar Abiey ce ta yi ringing da kamar izza Abiey ya kalli wayar ganin number yayarshi ce Dr Zainab ya saka shi amsa kiran.
“Hello”
“Abiey yanzu aka shigo da Zahra asibitin nan gurin abokin aikina wanda ka taba ganinsu a tare wai zuciyarta ta buga, Mamanta sai kuka take”
A firgice Abiey ya mike tsaye be san lokacin da ya saki wayar ba ya mikawa Sauban hannu.
“Ba ni key din ka”
“Lafiya”
Sauban ya tambaya, Abiey be tsaya ba shi amsa ba ba ya fisge key din hannunshi ya fice Garden din da gudu.
[11/8, 9:35 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣2️⃣
Kamar mahaukaci haka ya isa asibitin tun suna cikin mota Sauban ke tambayar Abiey abun da ya faru amman ya kasa magana ka kasa ce mashi komai, sai gudu yake har suka isa asibitin. Kamar an koroshi haka ya fito daga motar Sauban ma saurin sauka yayi ya zagaya driver side ya kashe motar ya rufe sannan ya bi bayan Abiey, Office din Dr Zainab Abiey ya shiga hankali a tashe ita kanta Dr Zainab sai da ta tsorata da yanayin yadda ya shigo office din.
“Ina take?”
Dr dake magana da wani abokin aikinta ta mike tsaye tana kallon shi.
“Da sauki fa ka kwantar da hankalinka”
“Wane ďakin take?”
Abiey ya sake tambaya a daidai lokacin da Sauban ya shigo office din.
“Follow me”
Dr ta fada sannan ta wuce gaba suka bi bayanta shi da Sauban kamin ta kai shi ďakin da Zahra take har jin yake kamar ya kara mata saurin kafafuwa, suna isa bakin kofar ďakin Dr Hamid na fitowa tare da wani likitan da nurse, Abiey be tsaya komai ba ya mika kafa zai shiga ciki sai Dr Hamid ya tara mashi hannu a bakin kofar.
“You're?”
Abiey yayi mashi wani banzan kallo.
“Abiey”
Sauban ya amsa mashi sai Dr Hamid ya kalli Sauban.
“Alakarsu nake magana ba sunanshi ba”
“Dr please bar shi ya shiga, hankalinshi ba zai kwanta ba har sai ya ga yarinyar nan”
Dr Hamid ya dauke hannunshi yana kallon Dr Zainab zai bar Abiey ya shiga ne kawai saboda shi ma yana son yayi requesting wani abun a gurin Dr Zainab ba dan wannan ba da sai ya wulakanta Abiey a gurin.
“Amman karka tashe ta bachi take bukata, domin zyciyarta ta yi bugawar da ba dan tsarin Allah ba da yanzu an rasa ta”
Abiey ya shiga ďakin da sauri, sai Dr Hamid ya kalli Sauban ya ce
“Zaka iya jiranshi a waje”
Sauban ya kalli Dr sai ta daga mishi kai, hakan yasa ya juya domin komawa gurin motarshi zai fi mashi ya jira shi a can sama da ya jira shi a nan. Sai da Sauban ya wuce Likita da Nurse din dake tare da Dr Hamid suka fice daga gurin sannan Dr Hamid ya jero tare da Dr Zainab yana tafiya yana labarta mata a halin da ya samu Zahra.
“Subhanallahi Allah ya tsare gaba”
“Ameen, Dr akwai rokon da nake son na yi miki”
“Ina saurarenka”
Ta furta a yayinda ta ja ta tsaya ta hade hannayenta tana kallonshi.
“Akan maganar yaron kanwata ne Amir ďan wajen Alhaji Bashir shekaranjiya matarshi take fada min cewar mijinta ya zo da ke akan Matsalar yaron na rashin shan nono”
“Eh an yi haka yau ma na ce ta zo asibiti mu fara auna nononta”