Sashe 25
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“A matsayin da kake a yanzu ai kai ne mace ita ce namiji domin idan har bata ce ta fasa auren ba, kasan Mai Martaba ba zai aminta matsala ta fito daga gurinka ba, kuma zai dauka kana wasa da hankalinsa bayan an je an tambaya aure sai kuma ka ce ba ka son yarinya a yanzu, kar fa ka manta wannan ne karo na farko da Mai Martaba ya nuna damuwarsa akan lamarin ka har ya shiga ciki, aiko ka ga wannan amaryar mai tsada ce”
“Na yi magana da ita tun shekaranjiya kuma na samu Dr ita na mata magana na san zata yi mata magana”
“Zauna Abiey”
Ya zauna yana kallonta.
“Wata Dr ko Ammy ko ni ko Momy ba za mu iya canja ra'ayin Yasmin akanka ba matukar tana sonka, amman kai zaka iya canja ra'ayinta ko da kuwa tana sonka”
“Anty na yi magana da ita, kuma ina tunanin ta fahimta in dai ba jan ido take son na yi mata ba”
“Ba maganar jan ido ka zaunar da ita ka fahimta da ita cikin hikima ku yi magana ta fahimta ta yadda zata fahimce ka kai ma kuma ka fahimce ta, a tunani zata yi ta amsa maka da to ne kawai amman ba zata taba aikata hakan ba”
“Shikenan zan sake magana da ita, amman shi ne na karshe idan ba ta yi ba zan samu Mai Martaba da kaina na fada masa cewar bana ra'ayinta”
“Karka aikata haka kara dai ka hakura matsalar ta fito daga gurinta”
“Okay... Anty yaushe zaki je yi ma Zahra gaisuwa?”
“Tare da kai ya kamata mu tafi kafata kafarka kai ma ya kamata ka fara motsawa ai, duk dai be dade da rasuwa ba, amman ya kamata ka fara nuna mata kulawa ta san da cewar har yanzu kana kaunarta”
Anty ta fada tana murmushi.
“Zamu je tare da ke da su Aisha sai ku shiga ciki ni zan tsaya daga waje, idan ta ga tana ra'ayin gaisawa da ni zata fito”
“Shikenan to ka saka mana rana”
“Gobe”
“Allah ya kai mu”
Ya amsa da Ameen, sannan ya mike tsaye yana shafa aljihun wandonsa ya fice daga dakin. Dakinsa ya koma ya dauki one of his car keys sannan ya nufi downstairs ya sauko yana kallon Aisha dake cin salad ya mayar mata da murmushin da ta yi masa sannan ya nufi kofar.
“Abiey ina zaka je?”
Ya dawo baya yana kallonta.
“Ke ba uwata ba, ke ba matata ba ki tsayar da ni haka nan kawai da tambayar inda zan je? Kin fi kowa sanin na tsani tambayar nan carefully next time”
“Sorry..”
Ta fada tana kama kunnuwanta be sake ce mata komai ba ya fice, few steps suka isar da shi gurin motarsa tun kan ya karasa ya dannan keys din hannunsa ya bude motar ya shiga. Tun kamin ya isa yake ta tsara kalaman da zai samu Yasmin da su, but before yayi magana da Yasmin ya kamata yayi magana da Dr so that ya san yadda suka yi, kamar ya dauko hanyar gidanta sai kuma wata zuciyar ta raya masa ya fara kiranta. Wayarsa ya dauka yayi dialing mumber ta ringing daya ta yi piciking.
“Hello Abiey yanzu fa nake kokari kiranka”
“Miya faru? Kin yi magana da Yasmin?”
Dr ta juya ta kalli Yasmin dake zaune a kusa da ita sannan ta amsa masa.
“Eh amman zai fi kyau ka same ta ta kanka akwai abubuwan da take son fada maka”
“Kamar ya?”
“Tana gidana yanzu haka, saboda na kirata na yi magana da ita”
“On my way”
Ya yanke kiran sai sake kiran Sauban.
“Sauban ya maganar ginin gidan nan?”
Shi ne abun da ya fara tambaya lokacin da Sauban yayi picking call din.
“Yana nan ana kan shi abu yayi nisa ma”
“Thank you, and you too ya kamata ka samu time ka je gaisuwa”
“Idan ka shirya sai mu tafi tare”
“Zamu je da Anty gobe”
“Okay kira ni idan kun tashi”
Da haka suka rabu, sannan ya rike wayar a hannunsa ya cigaba da tukin da dayan hannu har ya isa gidan, ya dade cikin motar domin ba kasafai yake son shiga cikin gidan ba gudun kar mijin Dr ya same shi a ciki domin ba sa jituwa da juna tun daga lokacin da aka fasa aurensa da Zahra. Har ya daga waya ya kira Dr yace mata yana waje sai kuma ya fasa ya bude motar ya fita ya nufi cikin gidan. Sau daya ya taba door bell din ya ja ya tsaya yana kallon harabar gidan, Dr ce da kanta ta bude masa.
“Welcome”
Ya shigo ba tare da ya amsa ba, idonsa be sauka gurin kowa ba sai Yasmin dake zaune a kujerar dake facing din kofar idonta yayi ja sosai har ya kumbura. Juyowa yayi ya kalli Dr sannan ya sake juya ya kalleta.
“Yasmin?”
Ta sauke kanta masa wasu hawayen na sake taruwa a idonta, sai ya sake kallon Dr a karo na biyu irin kallon nan mai alamar tambayar, kafada ta daga masa ta rufe kofar ta nufi kitchen tana fadin.
“Ka sauke ta gida”
Yasmin ta mike tsaye ta dauki yar karamar rigarta ta gyara mayafinta kamar daman can shi take jira, Abiey can't tell why yake jin rashin dadi na ganin hawayen Yasmin duk kuwa da be san dalilin zubarsu a idonta for now. Da kansa ya bude mata front seat ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya zagaya driver side ya shiga yayi ma motar key, the whole journey is full of silent words, ko da abun da yake tunani kuma yake sakawa a zuciyarsa. Sai da suka kusan isa gidan Momy sannan Abiey ya kalli Yasmin da har lokacin hawaye take sharewa ya ce.
“Are you okay Yesmin? Can we talk?”
“Me zamu yi magana akai? Rabuwarmu?”
“Mu ba masoya ba ne, balle ace zamu rabu”
Ya fada yana wata yar siriyar dariya.
“Anty Zainab ta yi requesting wani abu a gareni mai matukar tsada da wahala, Momy ma ta yi kai ma kai yi saboda na su san abun da nake ji ba, amman ina son na tambaye ka?”
“Uhmm”
Ya maida dukan hankalinsa gurinta.
“Ya aka ji a lokacin da ka rasa Zahra?”
Ya tsayar da tukin da yake ya samu gefen titi ya faka motarsa.
“Kamin na fada miki abun da na ji, ina son ki shirya ki tafi gidansu Zahra ki tambaye ya taji a lokacin da aka fasa aurenmu? Ya take kallona? Wane irin hali ta shiga? Daga lokacin zaki fahimta ki yanke hukunci akan dalilin daya saka nake ta rokon ki sa a fasa baikon nan da kanki”
‘Miyasa ka koya min sonka?’
Ta tambayi kanta tana kallonsa wani irin kaunarsa na fisgarta kamar ta bude zuciyarta ta saka shi ciki ta rufe, can kuma sai ta lumshe ido ta hade yawu a hankali, ya kalleta sannan ya cigaba da tukin har suka isa gidan be sake ce mata uffan ba, sai dai hawayen da take sun saka shi jin babu dadi.
ZAHRA POV.
Nasiha sosai Hajiya ta yi ta min tana kwantar min da hankali, ban taba ganin wata sarakuwa mai son matar ďanta kamar yadda Hajiya take so na ba, tun kamin na auri ďanta bata taba nuna min banbanci da yarta Bahijja ba balle kuma yanzu da nake ganin kamar ma tafi so na fiye da yarta, farfesun kan rago ta kawo min yan'uwanta da suka zo tare da ita kuma kowa ya dauki kudi ya bani sai bayan sallah magariba suka tafi. A daren ranar da tunani biyu na kwana a raina, tunanin abun da Yaya Maryam ta fada akan Deen da kuma nonon da za a baiwa yarona ina ta addu'ar Allah yasa kar nonon ya saka shi ciwon ciki. Washe garin bayan na yi wanka na shirya Mama ta kawo min abun karyawa, a yau kukun mai kayan sabe sabe tayi min wato na gyaran nono daman tun da asuba na ji ta tana aikin daka kayan da muke da su sai dai ban yi zaton ni zata damawa ba. Ban kuma yi mamakin ganin haka ba saboda na san ta yi min ne saboda nono na yayi kyau. Da rana ma tuwo ta yi min da miyar shuwaka da kifi, ba laifi na ci tuwon sosai kamar ba ni ba, domin na dade ban sake jiki na ci abinci mai yawa haka ba.
“Zahra kin san abun da kika yi ma yayarki ba ki kyauta ba?”
Ina daf da gama sudar yatsun hannuna Mama ta yi min wannan maganar.
“Amman Mama ita baki ga abun da ta yi min ba? A kaddara ma da gaske Deen ya aikata abun da take fada, ai be dace ta zo tana fada ba a yanzu saboda baya raye, kuma akwai ďana a tsakanina da shi ba zan jidadin ta aybanta uban ďana ba, Mama Wallahi ko da ace Deen ya aikata hakan da gaske to na jidadi domin shi yake nuna cewar kaunar da yake min mai kyau ce marar algus, domin ya rike ni amana ya nuna soyayya da kaunar da na san har na mutun ba zan sake samun irinta ba, a tsawon zaman da muka yi Deen be taba daga min murya da sunan zai min fada ba ko kuma ya nuna ni da yatsa balle har ta kai ga ya doke ni, mahaifiyarsa bata taba nuna min banbanci da yarta ba, shin hakan be isa ya saka na so Deen ba? Miya laifinsa idan ya yaki kowa akan abun da yake so? Da ace Abiey yana so na da gaske da be guje min ba ko da kuwa mutuwa zai yi a ranar, balle ma na san karya take ita ma kuma ba laifinta ba ne laifi Abiey ne shi ya shirya wannan saboda ya wanke kansa kuma ya sake dawowa ya cutar da ni”
Mama ta gyada kai.
“Gaskiya ne, idan na gaske ya aikata to ya rike amana irin rikon da ko wace uwa take son ayi ma yarta, Allah ya masa Rahma”
“Ameen”