← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 127

Sashe 110

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ammy wani zuwa da Zahra ta yi a nan kika koreta, bayan kin mareta na bi bayanta, ina bata hakuri sai ta ce Abiey ka nuna min kana kaunata tsakani da Allah ta hanyar bin umarnin Ammy da Mai Martaba, so yayi kadan ya saka ka bijirewa umarnin mahaifanka, ina son ka nuna min banbancin naka so da na Deen, karki yi son kai bakan ne kawai zai tabbatar min da kana so na da gaske, tun daga lokacin sai na dauki alkawarin zan nuna mata da duniya ina Sonta so na hakika, a lokacin ne na bullo da shawarar Sauban ya fara nemanta, yana nuna mata kulawa har ta amince da shi, saboda na san duk wata hanya da zan bi ba ku yarda ina son Zahra ba balle har ku tausaya min ku bar ni na mallaketa, ita kuma ba zata aminta da ni ba idan na fito mata a mutum, saboda tana matukar tsoron halin da zan jefa kaina a sanadinta, shiyasa na biyo ta wannan hanyar”

“Har yanzu ban fahimci abun da kake nufi ba, da ka biyo ta wannan hanyar sai aka yi yaya?”

“Hakarmu ta cinma zuwa da Sauban domin be fito a sigar yana sonta ba, har sai da wata mafitar ta bullo mana ta siyar da cikinta da ta yi ga matar da take zaune a gidanta a yanzu, kamin tafiya ta yi nisa sai da Sauban ya sanar da matarsa ni ma kuma na same shi har gida muka kara yi mata bayani saboda ta gamsu, gudun kar wata matsala ta taso ko kuma wani ya kawo mata wata maganar daga baya, ban aiwatar da komai a karan kaina ni kadai ba har sai da na shawarci Dr”

Ammy ta daka masa tsawa.

“Kana ta bata min lokaci Aliyu ka fada min abun da ka aikata”

Ya hade hannayensa guri daya.

“Mun yi nasara, Zahra ta karbi Sauban da hannu biyu, sai muka yi amfani da damar siyar da cikin da ta yi Sauban ya cilasta mata aurensa, mun tafi tare da Dr mun yi magana da mahaifiyar Sauban, ganin mahaifinsa baya raye sai ta samu kannen mahaifinsa ta gabatar musu da abun da muke bukata, kuma muka yi nasara suka amince, Zahra ta gabatar da Sauban a gurin iyayenta, da aka tashi daura aure sai aka ambaci sunana a maimakon na Sauban”

Ta mike tsaye da sauri tana kallonsa kamar wanda ta yi arba da wani abun tsoro.
[12/2, 11:00 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣7️⃣

“Aliyu kana cikin hankalinka kuwa, da gaske kake wai ko wasa?”

Ya saki murmushi.

“Taya zan zauna na tsara miki karya mai tsawo a haka? Idan baki yarda da ni ba zaki iya kiran Sauban ko mahaifiyarsa ko Dr kinji”

Ammy ta koma kallon sabuwar farar shaddar dake jikinsa ga wani uban kamshi da a yau yake da ya banbanta da na kullum.

“Aliyu ka aikata babban kuskure, taya son zuciya zai dauke ka ka aikata wannan abu? Ina tunaninka ya tafi? Ina taya idonka zai rufe ka aikata wannan abun?”

Ya mike tsaye yana kallonta fuskarsa cike da damuwa.

“Ammy karki kasa fahimtata mana kin fi kowa sanin yadda nake kaunar Zahra”

“Na ji kana kaunarta! Idan ma na fahimce ka taya mahaifinka zai fahimce ka? Daman shirin da kake kenan shiyasa ka ce a matso da aurenka da Yasmin?”

“Tasa mai sauki ce, idan har ke kin fahimta, a yanzu ne zan gane idan Mai Martaba ne mahaifina ko akasin haka, na san labarin zai fita kuma kamin kowa ya ji shi ni zan fara sanar da shi”

Ammy ta girgiza masa kai.

“Aa karka aikata wannan kuskuren Aliyu, ba zai fahimce ka ba, kuma tsabanin da zai shiga tsakaminku zai saka yan'uwanka jindadi, akwai makiya a tare da kai be kamata ka aikata wannan abun ba Aliyu”

“Na gagara fahimtar irin son da kike min Ammy kina so na amman baki son farinciki na? Mi Zahra ta yi miki ne kika juyar da soyayyar da kike mata zuwa kiyayya?”

Ammy ta matso kusa da shi tana kwantar da murya.

“Ba son Zahra ne bana yi ba Aliyu, ka fi kowa sanin irin rayuwar da Zahra ta yi a gidan nan, ka fi kowa sanin yadda nake son farincikinka, amman haka ba zai saka na goyi bayan butulcewa mahaifinka ba”

“Ba zan butulce masa ba, zan bi umarninsa zan auri Yasmin, amman ba zan rabu da Zahra ba, kuma haka da na yi ta taimaka masa domin an yi auren a sirrance, ba tare da sanin kowa ba, na san abun da Mai Martaba yake gudu yan da jama'ar gari su zage shi ko kuma su zafafa da mugayen kalamai akan auren, kamar yadda suka buga labarin cewar na rusa gidan uban matata saboda ya hana ni ganinta”

Ammy ta yi baya ta zauna saman gado ta lumshe ido.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, shekara nawa ina neman hanyar da zata gyara tsakaminka da mahaifinka, sai a yanzu da komai ya zo karshe sai kuma ka bullo min da wannan?”

Ya durkusa a gabanta.

“Ban yi dan na bata tsakanina da mahaifina, kuma bana fatar haka, kuma na miki alkawari idan har Ke ko Mai Martaba kuka dage akan sai na rabu da ita, tabbas zan hakura da ita, amman ki sani tana ciki raina kuma rabuwa da ita zai iya ajalina”

Ammy ta kai hannu ta shafa kansa.

“Allah ya sanyaya zuciyar mahaifinka ya fahimce ka, kuma ya karbi Zahra da hannu biyu, ba ni da matsala da haka, ina son abun da kake so ďana, amman ba zan boye maka ba, wannan abun da ka aikata ko a film ba a haka, ita ma dai Zahra ta yi sake ta yi ganganci”

Ya kwantar da kansa jikin cinyarta yana jin wani sanyi da kalaman da ta yi masa.

“Wallahi ko kadan Zahra bata da laifi Ammy, ba da saninta muka aikata ba, gargadi ta yi min yasa ban yarda na tura Sauban ko kuma ni na tafi mata kai tsaye ba, kuma ina son ki bar ni na fara yin magana da Mai Martaba har sai idan abin ya gagara tukuna sai ki shiga ciki, amman ina son na yi magana irin ta uba da ďa shi, ina son na samu wannan yanci da zan iya tunkarar mahaifina at any time na yi magana da shi”

“Allah ya saka ya fahimta”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarsa dake vibration ya mike tsaye.

“Sauban ne”

Be amsa kiran ba sai kawai ya juyo ya fito daga dakin ya sauko downstairs ya nufi kofa ya bude, sai suka sakarwa juna murmushi Sauban ya shigo cikin falon suka rumgume juna.

“Congratulations”

“Thank you na samu komai ta dalilinka”

“Yeah anything for our friendship, Allah yasa Ammy bata yi maka tsawa ba”

“for now dai kamar ta fahimta, sai dai ban san abun da gaba zai haifar ba, kasan Ammy wani lokacin bata da dadi, amman ba samu sauki ta fahimci, kuma ta fada min idan har Mai Martaba zai karbi Zahra bata da matsala”

“Alhamdulillah, haka muke so, fatan Allah ya sa Mai Martaba ma ya fahimta”

Ammy dake saukowa ta amsa da

“Ameen, Sauban kai kake biyewa Abokinka kuna aikata duk abun da ya zo muku ko? Sam sam sam haka be de ba, kuma na tabbatar da ba ni ce ba, da abun da zai faru zai fi wannan”

Sauban yayi dariya ya karasa shigowa cikin falon, ya zauna yana fadin.

“A gafarce mu Ammy, mun aikata kuskure amman dole ce ta saka, mum aikata hakan ne saboda muna tunanin kamar hakan shi ne mafita”

“Amman kuskure Babba Sauban, abu ya zo mana ta inda ba mu yi zato ba, kun saka mu a ciki tashin hankali, kuma na yi mamakin da har Dr ta iya biyewa kudirinku”

“Mi zai hana ta yin haka Ammy? Matar dake neman hanyar da zata gyara tsakaninta da kanenta? Kuma ta san abun da Abiey yake so, na tsorata da irin son da Sauban yake yi ma Zahra Ammy, idan ya rasa Zahra ke ma zaki iya rasa shi, sannan ban ga dalilin da zai saka ku tsaya kai da fata ku haramta abun da Allah ya halatta ba, ban san ko dan tana bazawara ne, amman Zahra mace ce kuma tana da hali mai kyau sam ban ga wata matsala a tare da ita ba”

“Matsalar ba daga ni ba ne, daman can ni ina kaunar Zahra sai dai hayyalar da ta tsira bayan mutuwar Deen ya shafa mata bakin fenti a fuskata, a yanzu kuma ina kallon yadda Mai Martaba zai dubi abun ne, domin abu ne na bacin rai ace ďanka yayi aure a boye bayan kuma ka zaba masa matar da zai aura, daman can basa jituwa yanzu kuma ban san yadda zai ji ba kuma ban san wani irin hukunci zai yanke ba,”

“Wata kila zai fahimta idan aka biyo masa ta siffar da zai fahimta din”

Sai a wannan gabar Abiey yayi magana.

“Shiyasa na ce zan yi magana da shi da kaina, kuma zan sanar masa tun kamin labarin ya yadu wasu su sanar masa”

Ya mike tsaye yana.

“Zan je na duba Zahra, tun da na baro gurin ban koma ba dazun”

“Miyasa same ta?”

Ammy ta tambaya tana kallonshi.

“Suma ta yi, lokacin da ta fahimci ni ta aura ba Sauban ba”

“Saboda dadi?”

“Saboda tashin hankali dai”

A tare suka fito da Sauban. Ammy ta sauke ajiyar zuciya, ko kadan bata son ganin laifin ďanta, ta san yadda yake son Zahra, kuma ta san yadda so yake domin ta taba shiga a makamancin wannan halin ba. Number Dr Zainab ta yi dialing sannan ta mike tsaye ta fara safa da marwa a falon. Dr na yin picking Ammy ta hauta da masifa.

“Haka ake yi? Sai ki biye masa ku zama marasa tunani? Ke ma kin zama kamar Deen kenan ai”
Chapter 110 · 0% Book details