← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 127

Sashe 73

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Tun a kwanan baya da wani aikinshi da nake kula da familynshi ya hada mu yace yana son na zo na duba ďanshi akan idan ya sha nono yana saka shi ciwon ciki, na je gidan na duba yaro na lura kamar mahaifiyar yaron bata jidadin zuwa ba domin tun a gaba ta fara kuka, sai dai yaje ya rarrasheta yace hankalinta ne ya tashi saboda bata son ana yawan taba yaro, ni kaina nayi zaton ko dan saboda bata tana haihuwa ba ne kamar yadda ake ta fada, sai after na tafi sai Dr Hamid ya same ni da zancen ma bashi kwana biyu saboda yana kan yi ma yaron wani maganin ne baya son a samu matsala, a lokacin da zuciyar Zahra ta buga a lokacin ne ya roki wannan alfarmar, ni kuma na amince mashi ba tare da tunanin komai ba, ban kawo komai a zuciyata ba a zatona da gaske ne, ashe wani abu suke boye min”

Abiey ya koma ya zauna yana kallonta cike da tashin hankali.
[11/14, 10:03 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣8️⃣

Ta numfasa sannan ta cigaba.

“The following day ya sake kirana a waya yace min be ji daga gareni ba, ni kuma na sai na mashi karya cewar na dora shi akan wani magani da na bawa matar ta bawa yaron idan ya samu sauki shikenan idan kuma be samu ba zan cigaba da bincikar Matsalar, har yake ce min yana son na auna jinin yaronshi na hada a cikin file din yaro idan na kammala bincike na yana son zai gani, sai dai zan cen ya kau saboda na fada mashi cewar na dora yaron akan magani, shi kuma ya yarda daga haka muka shashartar da zancen, sai shekaran jiya ya kira ni yace min yana son na gwada jinin matarshi da yaron shi da kuma Nannyn yaronshi da na shi jinin shi kanshi, ya bukaci na zo gidanshi na dauki jinin na su kuma ya dankamin amana kar na zance mashi komai ko da matarshi ko wani ya bukaci haka, duk ban fahimci komai ba har sai da na je daukar jinin yadda matarshi ta rika dari dari ya bani mamaki, sai kuma da muka je gurin Zahra tana kuka sosai na debi jininta, bayan mun fito yace min Dr ina cikin wata matsala da kwankwanto wani da nake fatar ya kusance ba gaskiya ba, amman na yardar dake na san ba za a hada kai da ke a cutar da ni ba, kuma ina son ki yi gwajin nan a sirrance a wani asibitin da ba za a iya canja komai ba”

Ta kalli kofar ďakinta jin hayaniyar yaranta kusa da kofar, Abiey kuma ya sake maida dubanshi gurin results din yana dubawa.

“After na baro gidan da minti ashirin Dr Hamid ya kirani yace ana son ya hadu da ni, babu irin hakurin da ban bashi ba akan ya jira na fito aiki amman yace ba zai iya ba magana ce ta gagawa, a dole na fada mashi meet point muka hadu sai ya fara karanta min halin da yar'uwarshi take ciki kamin daga bisani ya roki na bashi gwajin jini i refuse sai yace zai ba ni miliyan ashirin saboda na bashi jinin yaje ya yi gwajin idan ya gama zai kawo min results sai na bawa mijin kanwarshi nan ma na ki, a dole ya fito ya fada min gaskiya kuma ya roki na rufa mashi asiri na rufawa kanwarshi da kuma ita kanta Zahra, duk da haka ban yarda ba na dawo gida na shirya na tafi wata private hospital aka gwada jinin results din da ya bada kenan, Wallahi yau kasa aikin komai na yi a office saboda magiyar da Dr Hamid yake min da kuma ganin wannan results din”

Ta mike tsaye ta bude wardrobe dinta ta dauko wata bakar jakar ta kawo gaban Abiey ta aje.

“Miliyan hansi ne a cikin jakar nan a lokacin da nake ta kiranka baka daga ba har na kira Ammy na ce ta sanar da kai magana ce mai muhimmanci a lokacin ne Dr Hamid ya kawo min kudin nan har cikin gidan nan yana rokon na canja results din nan, fitarshi da minti talatin Alhaji Bashir ya kira ni yace min yana son ganin results din tsakanin yau da daren nan zuwa gobe”

Ta karashe maganar cikin wani irin damuwa na rashin makama, Abiey ya ce

“Har yanzu ba ki kai gurin da nake so na ji komai ba”

“Abiey baka taba mamakin dalilin Zahra na zuwa a gidan matsayim yar aiki tun a lokacin da ka fada min cewar Nuratu ta ganta a gidan ba? Ni kaina na tabbatar da haka ne a lokacin da na sake komawa gidan tare da Dr Hamid ka tuna lokacin da na fada maka cewar Zahra tana gidan?”

“Yeah amman zuciyata bata raya min wani bad abu ya kai Zahra gidan ba, she even told Sauban cewar matar gidan ta tausaya musu ta ba su gurin zama ita kuma tana kula da babynta, Sauban ma be taba fada min komai ba?”

“Wata kila shi ma be sani ba”

“That's mean Zahra ta siyar da yaronta?”

Dr Zainab ta daga mishi kai.

“Tun yana ciki domin har takardar yarjejeniyar na gani a hannun Dr Hamid da kudin ta biyawa Deen kudin aikin da aka mishi”

Abiey ya runtse ido da sauri ya cige bakinshi.

“Ohhhh nooooo Zahra why?”

“Bata da yadda za ta yi ne a lokacin domin tana neman mafita ne, sai suka yi karya cewar abun da ta haifa ya koma, ko a lokacin da ta haifi yaron na shiga dakin ina mata sannun sai cewa take ita mai rai ta haifa a cikin kuka sai a yanzu na gane abun da take nufi, Zahra ta jefa kanta a matsala gashi yanzu ta koma ta tare a gidan tana shayar da yaron saboda nonon matar ba shi da kyau kuma cikin yaron yaki karbar nonon kowa sai na Zahra”

“Yanzu na fahimci dalilin alakar Dr Hamid da Zahra wata kila ma ita ta sska a rushe gidansu Zahra saboda ta dawo gidanta ta zauna, why on earth Zahra zata siyar da cikinta saboda ceton rayuwar da bata cancanci cetonta ba?”

“A cikin takardar yarjejeniya Zahra ta saka hannu akan cewar idan har ta tsaba daya daga cikin dokokin zata biya naira miliyan ashirin, daman ina ta mamakin ina Zahra ta samu kudi haka ashe ta wannan hanyar ta same su”

Abiey ya mike tsaye kallon yayarshi.

“Sun yi haka ne saboda suna ganin bata da mafitar kudin kuma babu inda zata samu, what if i pay the price?”

Dr Zainab ta mike tsaye ita ma tana kallonshi har lokacin da damuwa a fuskarta.

“Ba biyan price din ne matsala ba, zaka iya biyan fiye da haka ma, fuskarta Alhaji Bashir a fada mishi gaskiya ne Matsalar abu ne mai wahala ya kyale ta wata kila zai iya cewa zai dauki matakin shari'a ka ga kenan Zahra ce a cikin matsala da kuma Dr Hamid”

“Don't make the same mistake twice, idan wacan karon tsoron rasa rayuwar mijinki ne ya saka kika canja results yanxu kuma son kudi ko kuma rufawa abokin aikinki asiri? Taya zaki ci amanar mutumen da yarda dake ya baki amana? Ki bashi results dinshi ya karanta ya san halin da yake ciki ki maida ma matarshi da Dr Hamid din kudinsu”

“Zahra fa...”

“Let him face her... Let him know the truth...Zahra bata da laifi nema suka yi ita kuma tana neman mafita shiyawa ta siyar, idan duk abun da na tara a duniyar nan zai kare kowa ya tsane ni ba zan bari wani ya nunawa Zahra yatsa a gaban goshinta balle ya ce zai hukunta ta”

“Idan su ba su yi ba baka tunanin mahaifan Deen za su iya ce za su hukuntata?”

“A nan zan nuna musu inda talauci ya banbanta da arziki, na saka a daure uwar da uban akan laifin da ďansu ya aikata domin da saninsu ya aikata trust me Dr this time around I'm joke about her idan har zan iya yarda na rasa raina to zan iya yardar na rasa Zahra a karo na biyu Zahra is innocent put this in your mind”

Ya juya ya fara tafiya ta rike shi domin ta lura ba da wasa yake furta kowane harafi ba.

“Abiey karka ayi abun da zai daga hankali Ammy karka kuma ka aikata abun da zai bata tsakaninka da Mai Martaba ka manta gargadi da yayi maka ne?”

Dawowa yayi ya kalleta.

“Idan har uwa tana son ďanta cilas ne ta so abun da yake so, kuma abun da yake saka shi a farinciki, apart from Mai Martaba kuma he's no longer my father...”

Ba shiri ta saki rigarshi baki sake tana mishi wani irin kallo na na tsananin mamaki, a gurin ya barta tsaye da mamaki ya fice daga dakin, a falon ma kamar guguwa haka ya fita yaran na mashi sai da safe be kula su ba, yana ya ari kafa haka yake tafiya har ya fice daga cikin gidan gaba daya ya nufi inda ya faka motar Ammy ya bude ya shiga yayi mata key kamar wanda baya son ranshi haka yayi reverse yana dukan sitiyarin motar.

“Why Zahra Why.......”

Ya furta da karfi kamar ya cire makogaronshi tsabar daga murya yana yamutsa gashi dake kanshi.

“Be cancanci kan akaifarki ba Zahra akan me zaki salwantar da rai?”

Ya runtse ido ya bude yana jin karin wata tsanar ta Deen, ga kuma tausayin Zahra a gefe da ya lullube shi.

“Allah Baiwar Allah, Allah kadai ya san irin hawayen da kika zubar a kan wannan abun how i wish kina kusa da ni Zahra you need a hug”

Wayarshi ya ciro ya kira Sauban few ringing Sauban yayi picking murya kasa kasa domin ranshi ya bace da abun da Abiey yayi mashi a dazun.

“Hello”

“Sauban kana ina?”

“Gida”
Chapter 73 · 0% Book details