← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 127

Sashe 80

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kamar na san zaki zo na dauke abincin mijina na boye, yarinya da ta zo bata aikin komai sai bincike”

Na yi dariya ina tsude hannuna.

“Hala na muku albashi? Na ga daman da yawa kuma cin ce kin cire na mijinki”

“Ina ruwanki, muguwar yarinya ina Mamata”

“Tana can gida Hijabinta ne ma na saka, ga kuma cinga tace a baki na bikin Anty Maimuna”

Ta dauko mai ta shafa shafawa tana fadin.

“Ikon Allah ashe bikin ya tashi”

“Eh kuma ban yi anko ba, Mama tace ba zata min ba”

“Mama ai tana iya kar kokarinta komai kika kwaso ita”

“To wa zai min idan ba ita ba?”

“Ina da 3k bari na baki idan kinje can ki saka mata kuka dole ta cika miki ki siya atamfar 3500 take ai sai ta baki na dinki”

“Jibi za a fara bikin ma”

“Ki siye atamfar da wuri ki kai dinki zan cika miki 3500 din”

Da sauri na tashi na rumgume ta ina murna.

“Na gode Yaya Maryam wai kin karbo atamfarki gurin dinki ko na je na karbo miki”

“Na karbo kuma Wallahi karki satar min abu ki saka”

Ta yi min gargadi domin ta san halina na saba daukar tufafinta na saka sai na gama yawo na dawo mata da shi, wani lokacin ma bata sanin na dauka har na dawo mata da shi. Kyalkyale na yi da dariya, ban bar gidan ba sai da yamma lis ina ta jiran mijinta ya dawo ya ba ni kudin Napep domin na saba idan na tafi gidan shi ke ba ni na komawa shi kanshi ya san da wannan dokar da kudin atamfar na fita daga gidan a nufin gidan Hajiya, ana kiran Sallah Magariba na isa gidan ko da na shiga Hajiya na gaban murhu tana tuka tuwo Deen kuma na alwala ba karamin dadi ba na tararda shi da na yi daman zuwan nawa kusan saboda shi ne.

“Ina kika fito Zahra da Magariba?”

Na karasa inda yake alwalar na zauna.

“Daga gidansu Yaya Maryam, so nake ka rakani gida saboda na saka Hijab din Mama zata iya cewa zata dake ni saboda sabo ne”

Hajiya dake kwasar tuwo ta juyo.

“Kin san sai ta dake ki kuma dole sai kin aikata? Ke dao ba zaki taba jin magana ba”

Na cinno baki gaba.

“Kuma Yaya Deen wani zai kira ka yace yana nemana to ni na bashi number ka”

Ya tsayar da alwalar da yake ya kalleni.

“Wanene?”

“Wani Mai Napep daya dauke ni dazun yace na bashi number na fada mashi ba ni da waya Mama kuma fada take min tana cewa ina raba mata number shi na na bashi number ka”

Mama ta saka dariya.

“Zahra mai farin jini kullum sai kin yi sabon saurayi”

Deen kuma ya mike tsaye ya nuna ni da yatsa.

“Duk kika kuskura ya kira ni sai na miki mugun duka, akan me zaki bada number ta har da wani zuwa ki fada min ke yar son maza, kullum kika fita sai wani ya biyo ki ke kuma gani sakarya sai kin tsaya kamar gareki farinjini ya yanke saka”

Haka ya rufe da fada har ya kammala alwalar ni dai sai turo mashi baki nake ina hararshi kasa kasa.

“Kuma ba zan raka ki gidan ba sai dai Mama ta kashe ki”

Na fada min kamar zai doke ni, Hajiya sai dariya take mana, ni kuma na tashi ina mita na dauki buta na zuba ruwa na fara alwala.

“Wallahi idan be raka ni ba sai dai na kwana nan”

“Zo dauki ga tuwonki ki ci”

“Ni ba zan ci tuwo ba”

“Sai me?”

“Indomie na ke so”

“To bari Deen ya zo shi da ya daukar miki wannan sai ya siya miki ni kam ba zan iya ba, zo dauki ga na shi tuwon ki kai mashi a ďakinshi”

Na aje butar bayan na gama alwalar na dauki tuwon na kai mishi dakinshi, kwalbar Coca-Cola da na gani aje gefen kujera na dauka na shanye ragowar lemun ciki sai na ji test din shi kamar ba irin na lemun gora ba, ban fadawa kowa ba ban kuma nuna na sha ba, na fito na kuskure bakina na shiga dakin Hajiya na yi sallah sannan na fito na zauna waje, shiru shiru ban ga ya dawo ba hakan ya saka dole na dauki tuwon na saka a gaba na fara cin ina mita kamar ance dole sai na ci, can na fara jin kaina na juyawa wani abu mai kamar bachi kamar ba shi ba yana son daukata kuma be dauke ni ba, na ji yawun bakina na tsinke kaina yaki tsayawa akan wuyana, ina bude baki na kira sunan Hajiya sai na ji sunan yana ja muryar na min nauyi sosai.

“Hajiya.... ”

Na daga kai daker na kalli sama sai taurarin dake sama suka fara hadewa da juna, na sauke kaina kasa tsoka biyu dake cikin miyar ya suka fara tsalle kamar ana ball da su, kwanon tuwon kuma sai yawo yake, na kalli yatsu hannuna sai na ga sun zama goma goma sabanin da da suke biyar biyar.
[11/18, 10:04 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣2️⃣

Na kwala mata kira da wata muryar da ke jinta kamar ba tawa ba.

“Hajiya”

Ta fito da sauri tana dubana.

“Zahra”

“Hajiya kin taba ganin nama na tsalle?”

“Aa”

“To wannan naman tsalle yake, kalla ki gani”

Ta duba ko bata duba ba shi ne ban sani ba, nidai idona suna kan naman dake ta aikin tsalle a idona, can na ji Deen ya shigo yana tambayar ba'asi.

“Ban san miya faru ba ta kira ni wai na fito na ga nama yana tsalle, sai kuma na same ta a wannan halin”

Na daga kai daker na kalli Deen shi ma tsalle na ga yana yi.

“Eh nama yana tsalle kai ma kana tsalle”

Can kuma na ga ginin gidan shi ma yana dagawa.

“Gini ma tsalle yake, ka gani ko tukunyar tuwo ma tsalle take”

Ya diko daidai inda nake zauna yana kallon fuskata, can na ga idanuwanshi suna ta yawo hancinshi na juyawa.

“Kin shiga dakina?”

“Eh na sha lemu, na shanye dika”

“Kin shawa kanki bala'i, dole sai kin yi bachi zai sauka”

“Yau ba zan yi bachi ba, a haka zan zauna har a bada komai tsalle yake Hajiya ke ma tsalle kike”

Na fada ina kallon Hajiyar dake aikin tsalle kamar zata je sama, wani abu mai kama da bachi ya fara zuwa yana jana ban sake sanin inda nake ba. Asubar fari na ji saukar ruwa a jikina aiko na zabura na tashi da sauri ina kallon Hajiya kamin idona ya sauka akan Deen daya bata fuska alamar be jidadin ruwan da Hajiya ta zuba min ba.

“Da kin barta idan bachi ya sake ta farkawa za ta yi, gashi nan kin jikata kuma sanyi fa ake Hajiya”

“Ina san ko ba zata farka ba yarinya tun jiya da aka kwantar da ita bata motsa ba kamar gawa, na sha maka magana Deeni bana son abubuwan nan da kake ajewa a cikin gidan nan idan abun ya zama maka dole ka rika zuwa can waje ka nayi abun ka ba sai ka shigo min cikin gida da wani kayan ba”

“Lemu ne fa kawai, kuma ita ma kwadayinta ne ya kai ta ai”

Ya miko min hannu na rika hannunshi na mike tsaye sannan na fashe da kukan jika min tufafi da Hajiya ta yi.

“Daga bachi dazu dazun ban ko dade ba kin jika min tufafi yanzu da wanne zan je gida kuma Mama tace zata min masifa”

“Mamar da aka kira aka fada mata a nan zaki kwana”

Na gwalo ido domin na san halin Mama bata yarda na kai dare wani gurin ma balle na kwana, ya aka yi aka yi convinced dinta ta yarda ma wani abun mamaki ne a gurina.

“Hajiya ashe ko yau sai ta soya namata, bari dai na yi sauri na tafi kamin a gama sallah Isha'i”

“Isha'i ki dai jira safiya ta yi asuba ce”

Kamar almara haka nake ganin komai, sai dai na lura da Deen da zarar ya kalleni sai yayi murmushi, Bahijja kuma dariya ma take min kai tsaye sai da Hajiya ta yi da gaske sannan ta shafa min lafiya. Ban iya cin komai a gidan ba saboda tsoron abun da zai biyo baya daga bangaren Mama, Deen ya aro babur din abokin shi ya goyani muka dauki hanyar gida yana fada min yadda suka yi da Mama.

“Na fada mata kanki ke ciwo ba zaki iya zuwa ba, saboda haka idan kin je gida haka zaki fada mata”

“Toh amman ka ji ta yi fada a waya”

“Tace ko kanki zai tsage ki dawo gida sai Hajiya ta roke ta ta barki ki kwana a nan domin gidan ba bakonki ba ne”

Na yi shiru ina ta kallon hanya, can ya jefo min tambaya.

“Waya baki kudi Zahra?”

Sai a lokacin na tuna da kudin ankon da Yaya Maryam ta ba ni.

“Laa Yaya Maryam ce ta ba ni na ankon Anty Farida, saboda Mama ta ce ba zata min ba sai ta ba ni 3500 tace na nemi na dinki”

Ya san ba zan mashi karya ba, domin karya ba halina ba ne ban saba yi ma mutum karya ba ko da kuwa za a yanka ni.

“Nawa ne na dinki?”

“2k suke cewa amman ka ga lokaci na kure bikin fa jibi ne ba za su karbi haka ba sai yayi tsada”

Be ce min komai ba, ni ma ban sake ce mashi ba har muka isa gida. Sai da ya fara shiga sannan na bi bayanshi, sai da yayi ta bawa Mama hakuri yana rokon kar ta dake ni sannan na yarda na shiga cikin dakin, Mama na ganin ya fita ta shigo dakin ta bulalarta data saba duka da ita, can saman gadonta na hau na fara ihu kamar zan tashi gidan.

“Mama dan darajar iyayenki ki yi hakuri”

“Oya shirya ki tafi makaranta ba san abun da zaki yi ba idan kin wuni a gidan”
Chapter 80 · 0% Book details