Sashe 86
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka dai na yi ta magana da kaina, saga karshe na yanke shawarar dauko wayar da nake kyautata zaton ta Alhaji Bashir din ce ya manta na duba yadda ake farfesun. Kamar wanda zata yi sata haka na dawo falon ina ta waige waige har na samu nasarar kai hannu na dauki wayar, tun da nake a rayuwata ban taba daukar wayar na ji tana neman subucewa a hannuna ba irin wannan saboda sulbin da take da shi, lallai kayan kamfani daban da na shago abun manya na manya ne a duk inda yake, maida kofar kitchen din na yi na rufe a hankali ba tare da na bari kara ta fito ba, sannan na taba wayar hoton Amir ne a gaban wayar yana bachi, a take tausayin Alhaji Bashir ya kamani ,domin yana kallon Amir a matsayin ďanshi ne alhalin ba jininshi ba ne, a yanzu kam ina jin rashin kyautawa a abun da na aikata, ko da yake ni dole ce ta saka amman Hajiya Jamila ta yaudari mijinta yaudara mai girma kuma yaudarar da babu wanda zai san gaskiya sai Allah. Na raba kaina da ďana zai girma be san ni a matsayin mahaifiyarshi ba, ban san Mama a matsayin kakarshi ba sai wasu familyn na dabam a matsayin familynshi, anya hakkin yaron nan ba zai kamani ba? Da kuma amanar Alhaji Bashir din na hada baki da ni a zalinci mutun da na lura babu komai a tare da shi sai alheri da son kyautatawa?
Na share hawayen da suka zubo miki na nisa ina taushe wani numfashi mai wuyar zama a masarafarsa.
“Ban yi da mugun nufi ba Amir, kuma ban aikata hakan saboda bana sonka ba, sai dai na ceto rayuwar mahaifinka rayuwar da bata tsaya ba”
Na aje wayar na dora hannuna akan sink hawaye wasu na rigan wasu sauko min, ina matukar jin kaunar yarona kalaman da Deen ya taba yi min da kuma wasikar da na karanta a gidan Hajiya suka tsaya min a rai.
‘Ki kula min da abun da zaki haifa ko da bana raye ki tarbiyantar da shi’
‘Karki tsani yayana saboda abun da na aikata’
Kuka na yi sosai sannan na share hawayena na wanke hannuna da fuskata a jikin fanfon kitchen ko na kwashe dankalin daya soya, na rage wutar gas din na maida hankalina gurin wayar sai a lokacin tunanin pin din wayar ya zo a kai, ga mamakina ina taba samn wayar sai ta bude ashe babu password a jiki, ba karamin dadi hakan yayi min ba a take na kunna data wayar na saka wayar a silent na shiga cikin ina dubawa har na gano YouTube, kai tsaye na shiga na rubuta farfesu, a take aka nuna min video kala kala, farfesun kaza na kifi na kan garo na kayan ciki and so on. Freezer na nufa na bude na ina dubawa, babu komai a cikin sai kayan marmari, rufeta na yi na nufi dayar dake kwance na bude sai na yi arba da nama kala kala.
Da taimakon video dake playing na yi musu farfesun nama zallarshi, yadda na ga suna zuba abubuwa haka na yi sai dai ban saka kayan kamshi ba domin ban ga ko daya ba, sinadarin dandano ma daker na ganoshi, sai da na gama na sauke sannan na fasa kwai na soya, ban yi tunanin dandanawa na ji yadda girki yake ba domin na gama girkin ne cikin rashin natsuwa ina ta fargabar kar Hajiya Jamila ko Mijinta su shigo su same ni da wayar, wannan yasa idan na kalla sai na boye wayar a cikin zane, domin idan wani ya same ni da ita ban san me zan ce ba musamman ma shi wata kila zai ce sata na yi, sai dai cikin hikimar Allah babu wanda leko kitchen din har na gama girkin. Manyan kuloli na dauko na zuba komai a dabam dabam sannan na dauka na nufi dinning na jera sannan koma kitchen din na dauki wayar na da na aje bayan cups na yi clearing video din da na kalla na rufe data na fito ina ta kalle kalle har na yi nasarar aje wayar a gurin da na dauke ta, wani wawan tsalle na daka ina jindadin yadda na shirya komai ba tare da kowa ya gane komai ba, ba tare da tunanin komai ba na haura sama ba kwankwasa kofar dakinta tun kamin, daga inda nake tsaye ina jiyo sautin Ummiter, hakan ya fahimtar da ni hira suke mai cike da nishadi, ashe kuwa na canka a daidai domin dariyar dake take yi a yanzu ya tabbatar min da haka.
“Zahra”
“Na'am Hajiya tana ciki”
Na amsa ba tare da na gaishe ta ba daman can zuciyata bata taba raya min na gaishe ta ba, taya zan gaishe da matar da bata wuce sa'a ta ba.
“Eh tana ciki”
Ta bude kofar dakin gaba daya, hakan ya bani damar hango Alhaji Bashir dake zaune kan kujera Hajiya Jamila kuma tana zaune kusa da shi, sai dai na ga tsabanin abun da na gani a fuskar Ummiter da Alhaji Bashir, ita kam sam babu ko kufan murmushi a tare da ita balle dariya har ya kaita ga nishadi.
[11/21, 10:53 AM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣5️⃣
Bayan na sanar musu cewar na gama na sauko na daya a dayan set din cushion din domin bana son na tsaya a kusa da inda ya zauna dazun yayi zaton ko na taba mashi waya, babu mai iya sanin farincikina sai Allah da ya amince min na girka wannan breakfast a yau na shirya komai ba tare da sanin kowa ba, balle a gane cewar ban iya ba. Ummiter ce ta fara saukowa jikinta sanye da tufafin bachi wando da riga ta nade kanta da wani abun da nake kyautata zaton tawul ne. Alhaji Bashir ne na biyu sannan Hajiya Jamila, a duk lokacin da muka hada ido harara take aiko min da ita, mijinta kam ban da murmushi babu abun da yake, ba na ce ina ganinshi kullum ba balle na ba da shaidar kyakkyawan murmushin sake fita tsakanin kumatunshi amman tabbas tsakanin jiya da na fara bashi labarina zuwa yau na lura nishadin shi dabam yake.
“Kin cire na ki ko?”
“Aa ban zuba ba”
“Ke da girki, mu da fara ci zo ki zuba na ki mana”
Na dauki plate din da yake nan na bude cooler na zuba, na sake daukar dayan na zuba dankali da kwai, sannan na dauka zan tafi.
“Tea fa?”
Na juyo na kalleshi sai kuma na kalli Hajiya Jamila wacce ta hade min fuska.
“Aa wannan ya isa”
Ban jira ya sake cewa wani abu ba na fito falon da saurina, kamin na karasa bq na tsaya na dandana abinci domin tun a cikin yawuna ya tsinke, saranda na yi ina fidda ido waje, anyi ba'ayi ba kenan ni kaina ban taba cin girki marar dadi irin wannan gashi dai be nuna ba kuma ga rashin dadi wani gurin ma kamar gishiri ya zarce.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Na fada cikin tashin hankali, da gudu na karasa bq din a waje na aje plates din hannuna na dawo da gudu zuwa main house din jikina har mazari yake, ala ala nake idan ba su ci ba ina shiga cikin falon muryar Hajiya Jamila ta dira a kunne
“Ni gaskiya ba zan iya cin wannan abincin ba”
Ummiter kuma sai kwasar dariya take, tsaye na yi jikin kofar falon irin yadda yara suke idan sun yi laifi fuskana na bayyana rashin jindadin abun da na aikata, sai suka dago suna dubana, Alhaji Bashir da fuskarsa take sake har yanzu ya ce.
“Zahra karaso mana”
Kamar ance karasa ki jr ga ajalinki haka na ji, sai na samu kaina da kara matsawa baya na kwalla sharrr daman can haka nake zarar zan aikata laifi to kuka ne zai biyo baya tun kam ayi min hukunci.
“Dan iskanci kin san baki iya girki ba kika karba kika yi? Shi wannan abinci mai kama da guba da kika girka mana so kike mu ci mu mutu ne?”
Na girgiza kai daga inda nake tsaye, sai Alhaji Bashir yayi alama da na zo da hannu, cikin karfin hali na taka na karasa gurin ina mai tsananin jin kunya taya mace kamar ni ace ban iya girki ba, ai da kunya ba ma karama ba.
“Kiriniya bata barki kin tsaya kin ko yi girki ba ko Zahra?”
Na sauke kai na kasa ina jin sautin murmushinsa.
“Video da kika gani a waya suna tsallaken time ne ke kuma kin yi amfani da yadda suke kika girka mana wannan ba ki yi la'akari da haka ba”
Wata kunya ce ta kama ni, ya aka yi ya san na dauki wayar har na duba?ko dai akwai camera a falon da kitchen din ne? Wata kila Hajiya Jamila ta boye min ne saboda na saki jiki na aikata wani abun ta gani, wannan maganar da mijinta yayi ya tabbatar min da akwai camera a falon ba kamar yadda Hajiya Jamila tace min a waje kawai aka saka camerar tsaron ba. Yanayin yadda muryarsa ke fita ya isa ya karantar da ni cewar ranshi be bace ba, musamman da na daga kai na kalli fuskarsa sai na yi arba da murmushi irin na mazan dake da kokarin fin karfin zuciyarsu ko da an musu ba daidai ba su kasa nunawa. Ummiter kallon mamaki take min tana yi ma Alhaji Bashir sai kuma ta kalli Hajiya Jamila da ta kusa mutuwa tsaye.
“Ba ki iya girki ba Zahra?”
Ya tambaya, sai na daga masa kai ina dan turo baki ji nake kamar ya muzantani a bainar nasi.
“Ya kamata ki koya ko dan gaba, maza suna son mace da ta iya girki misali irina ina son mace mai girki kala kala, kuma ya kamata ki koyi amfani da wasu abubuwan like wannan dankali akwai inda ake soya shi ba sai an saka cikin ruwan mai ba, Wife ina tunanin catering school zamu nema mata what do you think?”