← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 127

Sashe 116

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba su da Amir ba, na riga na sanar musu cewar ďan ya mutu, babu san dadinsa amman Mr Bashir ya saba da shi, kuma ya riga ya nunawa duniya Amir a matsayin ďansa, idan Amir ya zauna tare da su zai samu rayuwa mai kyau ya kamu karatu da tarbiya, kuma na tabbatar idan ya girma ya san abun da na aikata ba zai jidadi ba, musamman idan suka nuna masa irin soyayyar da suka nunawa Deen wanda ta saka ya lalace ya zama ba shi da aiki sai shaye shaye da abokanan banza, wanda ya zama silar faruwar komai a yanzu. Mama ki duba tun daga lokacin da abun nan ya faru har ta kai Baba ya sake ki be sake waiwayarmu ba, daga shi har Hajiya sun dauki abun nan da zafi, idan suka san abun da na aikata za su hukunta ni kuma za su sanar da duniya, wata kila ma hakan ya saka kallon da iyayen Abiey suke min ta kara tsami, har wadanda ba su san ni ba wata kila za su ji sun tsane ni, shi kuma Mr Bashir zai shiga damuwa kuma duniya zata san an siyar masa da ďan wata kila ko da iyayen Deen sun hakura hukuta tace zata hukunta ni, amman idan yaron ya zauna a hannun Mr Bashir duk hakan ba zai faru ba”

“Amman ke kina jin zaki iya jure rashinsa Zahra?”

Na daga mata kai ina kallon Amir din dake ta kuka har da hawaye.

“Zan iya, na rayu ba tare da uba ba, na kuma rasa mijina na rayu balle ďan da na san zai kasance a kyakkyawar rayuwa kuma zan iya samun wasu yaya a gaba”

Na mika hannu na karbi Amir din dake hannun Mama na cire hijabina na saka hannuna na ciro Nono na saka masa a baki, sai ya ki karba sai kara fashewa da kuka yayi kamar ya san abunuwan da suke faruwa. Sai da na dorashi a kafata na fara yawo da shi a dakin ina jijjigashi wai ko zai yi shiru amman a banza kamar ma na kara masa, Mama ta karbeshi ta goya tana rarrashinsa nan ma a banza, kuka yake sosai har wani shakkuwa yake kamar zai tsude, a take hankalina yayi matukar tashi, cikin fargaba na saka hijab dina Mama ta saka nata muka fito daga BQ din muka nufi gate domin kai shi asibiti, gurin masu gadi na nufa daman can asali su suke bude min gate idan zan fita domin ban iya bude kofar ba saboda nauyinta.

“Dan Allah ku bude min gate asibiti zan kai Amir”

“Aa Mai gidan yace kar mu bari a fita da yaron nan daga gidan nan yace ko da matar gidan ce”

Cike da mamaki nake kallonsu.

“Shi ya fada muku haka?”

“Eh”

“Asibiti zan kai shi ba ku ga yadda yake numfashi ba”

“Umarni ne aka ba mu, kuma idan za a kai shi asibiti ai ba ke ya kamata ki kai shi ba iyayensa”

Kamar ya san cewa zan yi ya kira Mai gidan ya fada masa sai ganin na yi ya kara waya yana karanta masa abun da ya faru.

“Gata nan a bakin gate”

Wata kila cewa yayi a bani wayar sai ya miko min, ni kuma ba karba na kara a kunne.

“Hello...”

“Zahra... Miya samu Amir?”

“Kuka yake tun da na karbo shi, na bashi nono ya ki ya karba, ina tunanin kukansa yayi yawa ne shi ne numfashinsa yake yin sama, su kuma sun hana na fita wai ka ce kar a bari kowa ya fita da Amir”

“Eh ba fada musu haka ne saboda na yi tunanin ko Jamila zata yi kokarin guduwa da shi ne, zan fito yanzu nan”

Na mikawa mutumen wayarsa sannan na juya na kalli Mama na fada mata yadda muka yi sai muka koma gurin kofar bangarensa muna jiran fitowarsa kamin ya fito har na matsu na dauko da Amir a bayana ina kallonsa gani nake kamar mutuwa zai yi domin abun karuwa yake har wani lumshe ido yake kamar mai bankwana da duniya.

“Mama kalli mutuwa zai yi”

“Wane irin mutuwa kuma, kawo shi a nan”

Amaimakon na mika mata shi kamar yadda ta bukata sai na tura kofar shiga falon Mr Bashir na shiga da gudu ina kuka, karo muka kusa yi da shi domin shi ma ya fito da saurinsa ne sanye da sabuwar shadda.

“Subhanallahi miya same shi ne”

“Tun da na karbo shi yake kuka har yanzu be daina ba, kalli numfashinsa cirewa yake”

Ya mika hannu ya karbe shi, Sai Amir ya bude ido ya kalleshi ya sauke ajiyar zuciya a take kukansa ya yanke, har sai da na yi zaton ko an zare numfashinsa ne.

“Ko ya mutu ne”

“Aa”

Ya amsa ni yana kallon Amir din da shi ma kallonsa yake.

“Karbe shi zan musu magana, direba zai kai ku asibitin yanzu”

Ina mika hannu na karbe shi sai ya sake fashewa da kuka da sauri Mr Bashir ya janye shi ya fara jijjigashi.

“Sorry sorry”

Sai kuma yayi shiru, ba shi Mr Bashir din ba har ni har ni da Mama mamaki muke, domin jariri mai wata uku zuwa hudu be isa zaben uwa ko uba ba, haka kuma be yi wayon da zai ce da Mr Bashir yake son ya zauna ba balle na ce zaba yayi, idan ma shakuwa ce ina tunanin zai fi shakuwa da ni da nake shayar da shi fiye da Mr Bashir da yake a matsayin ubansa a yanzu, akan kafadarsa ya dorashi ya wuce gaba ni da Mama muka bi bayansa kamin mu isa gurin Motar Ummiter ta fito da shirinta idonta a kumbure kana ganinta ka san kukan da ta yi ba kadan ba ne, kamar ita aka yi ma laifin ba Mr Bashir ba.

“Ina zaku je?”

“Asibiti Amir za a kai”

“Me ya same shi?”

“Kuka yake yi yaki yayi shiru numfashina har sama yake kamar zai suma”

Yayanta take tambaya amman ni nake amsa mata, tsaye ta yi a gurin har muka shiga motar da Mr Bashir ya nuna mana direba ya nufo motar da sauri ya shiga, Mama ce ta fara shiga sannan na mika hannu na karbe shi sai ya fashe da kuka, ina kokarin shiga motar Mr Bashir ya dakatar da ni.

“Zahra kawo shi”

Na mika masa shi, a nan ma yana karbar sai yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, mun dade a tsaye yana rumgume da shi yana shafa kansa, sannan ya sake miko min shi yana fadawa Direban asibitin da zai kai mu, ya juya da sauri ya koma ciki, a take Amir ya sake fashewa da kuka, kukan da be daina ba kenan har muka isa asibitin da take ta kudi ce, wata kila Mr Bashir ya sanar da ma'aikatan gurin tun kamin mu iso, domin mun same su suna jiran isowarmu, a asibitin muka wuni har yamma sun dauki hotonsa an auna jininsa sai dai ba su fada mana komai ba har dare, wata a wannan asbitin ba su sanar da abun da yake damun yaro da wuri ko kuma ba su gama binciken su ba ne, Amir kuma be fasa kuka ba har garin Allah ya waye idan na bashi nono ba zai sha ba sai kukan kawai yake ta yi har sai da likitan safe ya shigo yayi masa allurar bachi sannan muka samu yayi bachi, muna tare da Mama har lokacin domin bata son ta tafi ta bar ni kadai, ni kuma hankali ya kasu gida biyu daya a nan daya kuma a gurin Abiey ina tunanin ko a wane hali yake a yanzu, idan iyayensa suka gane abun da ya aikata ko wane irin hukunci za su yanke masa? Gashi na bar wayata a gida balle na kira shi na tambayi halin da yake ciki.
Dawowar likita ne ya yanke min tunanin da nake sai na gyara zamana na kalli Amir dake bachi.

“Madam ya mai jiki?”

“Gashi nan yana bachi, amman Dr baka fada mana abun da yake damunsa ba”

“A iya bincike da muka ji na jiya be nuna akwai wata matsala ko wani ciwon a tare da shi ba, amman za mu sake yin wasu waje wajen a yau Inshallah”

“To miya yake kukan?”

“Shi muke kokarin mu gano, domin be kamata a rubuta masa maganin komai ba har sai mun gano abun da yake saka shi kuka, kar ya zamana mun yi magani dabam cuta dabam to yaro ne karami ba shi da baki balle ya iya fada mana matsalarsa”

Na juya a hankali na kalleshi.

“A da can yana ciwon cikin idan ya sha nonon da bawa nawa ba, ban sani ba ko matsalar ce har yanzu, amman shi ma ya daina daga baya domin bayan nono akan hada masa da madara kuma ya sha bata masa komai ba”

“Eh Alhaji Bashir yayi mana wannan bayanin tun a jiya da na sanar da shi ba mu ga wata matsala ba, to amman kin bashi wani abun ne?”

“Aa madarar dai ko jiya ya shekaranjiya ya shata ban san ko ita ce ta haifa masa da matsala ba a yanzu”

“Dole a kawo mana madarar mu gani kuma zamu son gwada ruwan nono na ki so that mu gano idan ta wata matsala, sannan za a sake yi masa wani hoton da wasu manyan gwaje gwaje Inshallah”

“Toh”

Na amsa jiki a sanyaye ina jin wani yanayi na rashin jindadi, sai da likitan yayi abun da zai yi ya fita sannan na kalli Mama cikin damuwa na ce.

“Mama ko dai shi ma mutuwa zai yi?”

“Ko kuma dai Allah mai hikima yana nufin shirya wani abu a tsakanin bayin nan nasa”

“Ban gane ba”

“Tsakanin Alhaji Bashir da Amir din mana, baki lura ba idan ya dauke shi ya kan yi shiru?”

Na zaro ido sai kuma na juya da sauri na kalli Amir din.
Chapter 116 · 0% Book details