← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 127

Sashe 87

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karasa yana kallonta wata uwar harara da ta jefo masa ni kaina sai da na nemi natsuwata na rasa, Ummiter kam abun da take nema ne ya bude mata kofa wato gulma har bakin Alhaji Bashir dake motsi kallon take balle kuma reaction dina da na Hajiya Jamila.

“Hubby ina son magana da kai”

Tana fadar haka ta mike tsaye har wani hura hanci take kallo daya zaka yi mata ka fahimci ranta a bace yake, daman kuma na lura da hakan tun a jiya.

“Okay gani nan shigowa”

Amsa mata yake amman idonshi akai yake kamar zata wulgar da kujerar data zauna haka ta jata baya ta bar dinning a matukar fusace, a take na karanci jindadi a fuskar Ummiter sai kallona take da mamaki.

“Ummiter shiga kitchen ki shirya mana wani abun da zamu ci”

“Okay dan'uwana Yayana”

Ya mike tsaye tare da jan kujerar a baya a hankali ta sauka dinning din ta shiga kitchen.

“Zauna”

Yayi min nuna da kujerar da Hajiya Jamila ta tashi.

“Yallabai...”

Ban karasa fadar abun da zan fada ba ya daga min hannu.

“Ki ce Bashir idan yayi miki nauyi ki kira da Mr Bashir”

Sai da na ji faduwar gaba for no reason.

“Hajiya Jamila zata iya fada, tace kar na sake kebewa da kai”

Murmushi yayi ya dauki dankalin ya kai bakinshi.

“Ina ta karanta abubuwa akanki, har yanzu akwai kurciya da wauta irin ta yan auta a tare da ke, taya Jamila zata yi miki magana cewar karki sake kebewa da mijinta kuma ki fada min? Dazun ma zuciyarki bata raya miki da sanina na bar wayata akan kujera ba? Ba ki yi mamakin wayar babu password ba? I expect ki dauka ki duba wani abu kuma kin yi”

Risinawa na yi kasa ina kuka.

“Wallahi ba bincike na yi maka ba video kawai na duba na abinci”

Da hannu yayi alama da na tashi tsaye.

“Kina tauye kanki kuma ba ki iya tsayawa ki yi tunani Mai Kyau kamin aikata abu, ya kamata ki fito kai tsaye ki fada min ban iya girki ba, daman na saka ran haka yara irin da basa jin magana ba komai suka iya ba, sai kuka da shagwaba, i wonder how mijinki ya iya zama da ke?”

Yanayin yadda ya karashe maganar ya nuna tambaya yake da neman sani, sai na share hawayena.

“Daman ai ya saba da halina tun a gida”

“Shi Abiey?”

“Aa Deen”

Yayi murmushi.

“Shi ma kin taba masa kenan? Zauna ki tsakura min ya kuka kare da Abiey?”

Na kalli hanyar stairs yan hanjin cikina na kadawa ba dan tsoron Hajiya Jamila ba sai dan gudun bacin rai, kallon stairs din yayi ya kalleni

“Look Zahra daga Jamila har abun da yake karkashinta iko na ne mallakina na ne, saboda haka ki natsu kuma ki bi duk umarnin da zan baki wata kila hakan zai goge shafukan laifukan da kike da su a gurina”

Zaunawa na yi idona na kanshi irin na marasa gaskiya.

“Waya ce na ni wani abu? Wani laifin aka ce na maka? Ko kuma na aikata cikin rashin sani ne?”

Kallona yake yana zagaye fuskata da idonshi can ya sauke gurin bakina yana kallon lips dina.

“Fada min ya kuke kare da Abiey? Ina son sani abubuwa akanki, saboda ina son zuciyata kara natsuwa da ke”

Na ware hannuna ina tabawa sai idonshi ya koma gurin tsiraran yatsun hannuna.

-Gudu muka rika yi ina ta kiranshi amman be juyo ba kuma ba tsaya min ba har sai da ya ji na fara kuka, na fadi a gurin ina ta kiran Babana da Mama sannan Abiey ya dawo ya kama hannuna yace

“Ki tashi mu gudu mana, bana tunanin a nigeria muke fa, duba wannan dajin babu kowa babu haske, kuma tafiyar da na yi be wuce daga nan zuwa can ba ina nemanki sai hango ki na yi a tare da matar nan amman duba gudun da muke amman har yanzu ba mu kai gurin mutane ban ga alamar titi ba”

Kuka na fara yi domin na gaji sosai.

“Ni ba zan iya gudi ba na gaji da yawa”

“Haka zaki daure waya ce ki kawo mu nan, tun da nake a rayuwata ban taba shiga hatsari irin wannan”

“Ai kai ka kawo mu kai ka yi min dinki da baka dinka min wannan lace din ba da yanzu ina can gida ina bachina, amman kai ka dinka min ka kuma ka kawo nan”

“Laifin ki ke kika ji maganar iyaye ki ai, da kin ji maganarsu da duk haka be faru ba”

“To waya ce na bijire musu ba kai ba, kai ka dinka min kaya kuma ka dauko ni ka kawo gurin bikin aljana Allah ka dai ya sani gaskiya wata kila kai ma aljanin ne”

“Amman da na kawo ki ai na ce ki tashi mu tafi kika ki ko? Kuma da kin fada min cewar Mamanki ta hana ki zuwa ba zan yarda na kawo ki ba, gashi nan abun da kika ja mana ai”

Na fisge hannuna.

“Abiey mu ga kafarka”

Tsaki yayi ya mike tsaye ya fara tafiya, sai na saka kuka ina ihu idan na yi ihun sai murta ta amsa amo, da sauri ya dawo ya fara kokarin rufe min baki.

“Ki yi shiru Zahra karki ja mana wata matsalar haba, kina jin yadda muryarki take amsawa kin san ba a duniyar mutane muke ba”

“Ban yarda da kai ba, mu ga kafanka”

Ya daga wandonshi da sauri ya haska kafar da wayarshi, farar fata na gani irin ta mutane amman ban gansu ba har sai da na kai hannu na taba, ban ji gashi irin wanda na ji a gurin wacan yarinyar Aljanar mai kafafuwan doki ba, hakan kuma be kara gamsar da ni ba sai da na dankara mashi kwanta har sai da yayi kara.

“Miye haka?”

“Tabbatarwa na yi, yanzu me zan fadawa Mama? Kuma na san Deen sai ya kusa kashe ni idan na koma gidan”

Na fada cikin kuka ina tuna irin azabar da Deen yake ba ni idan ya ga na tsaya da wani balle kuma ace na bi namiji na shiga motarshi. Ya sake kama hannuna.

“Yi hakuri ta so mu tafi”

Na mike tsaye muka cigaba da tafiya cikin tsoro yana rike da hannuna gam.

“Karki juya, ba a son tafiya ana juyawa”

Da dukan alama shi ma tsoron be gama fita cikinshi ba, idan ba haka ba taya zai ce min wai kar na waige ba a son waige idan ana tafiya. Kyalkyalewa na yi da dariya sai yayi saurin sakin hannuna.

“Zahra ke ce?”

Ina jin haka na san tsoro yake ji sai dariyar ta kara taho min.

“Ban taba ganin namiji mai tsoro ba irinka, ashe ma kai matsora ci ne”

“It's not funny Zahra baki da hankali ashe, now i understand why ake dukanki a gidanku taya zaki fara mana dariya muna cikin wannan halin”

“Haka ka wuce ni fiuuuuuu kamar iska”

Na nuna yadda yake gudun ina cigaba da dariya, sai gashi shi ma yana dariyar, tafiya muka cigaba da yi har muka gaji muka samu gindin wani ice muka zauna ni da shi, sai ya jinginar da wayar tsakiyar mu nan tsoron ya sake dawo min.

“Ka kira waya mana ka fadawa Babanka ko Ammy, ni tsoro nake ji”

“Network din ya dauke ai, da tun kamin ki fada na kira”

“Yanzu ya zamu yi?”

“Waya sani kin janyo mu kin kawo a nan, Allah yasa idan kika koma gida ayi miki shegen doka”

“Kai ma Allah yasa idan ka koma Babanka yayi maka shegen duka”

Ya kalleni.

“Da ace Babana zai doke ni ko ya hukunta idan na yi masa laifi da zan fi kowa farinciki da jindadin haka”

“Saboda?”

“Saboda mahaifina ba kamar mahaifinki ba ne, ni nawa mahaifin babu ruwanshi da ni, idan na ci ko ban ci ba, ba damuwarshi ba ne idan wani abun zai same na fadi na mutu ma ba zai damu ba”

“Ka masa laifi ne?”

“Ban masa laifin komai ba domin na tashi ban san wani abu soyayyar mahaifi ba, ko riga daya be taba siya min na saka ba, a gidan Ammy na bude ido ita ce uwata ita ce ubana, ita take hukunta ni idan na yi laifi kuma ita take cilasta min zuwa gidan mahaifina daga ita sai matarshi ta uku Anty Amarya ita ma tana so na sosai kuma tana nuna min kulawa tana neman duk wata hanya da zata shirya tsakanina da mahaifina”

“Fada kuka yi?”

“Ba mu yi fada ba Zahra, ko da na bude ido haka na samu kaina cikin tsanar mahaifina ban san dalili ba, amman abun nan yana min ciwo sosai, amman kin yi dace ba kamar ni ba Babanki yana son ki”

“Ka fini sa'a domin kai ka ga mahaifinka, ni kuma ban san nawa uban ba, Mama ta fada min tun ina ciki ya rasu ban taba ganinshi ba sai a hoto, sai abokin shi na sani wanda shi yake auren Mama ta a yanzu”

Kamin na karasa maganar hawaye regen regen sauko min yake, domin ni ma ina da wannan tabon na rashin sanin mahaifin ko sau daya ban taba jin muryarshi ba, balle na yi rayuwa da shi.

“Allah ya mishi Rahma”

“Ameen”

Na share hawayen sai ya rika kaina yana kokarin kwantar da ni kan kafadarshi na buge masa hannu.

“Kai wai miyasa kake taba ni be kamata ba fa, ni dai ba yar iska ba ce”

“Ni kuma dan iska ne ga iskanci nan rubuce a goshina, daga taimako, ai gashi nan kin jefa mu cikin wannan halin”

“Ai nima bana son taimakonka daga yau, ba ni ba kai daman ba san haka za a fada min a gida, kuma zan fada musu cewar sace ni ka yi?”

“Ya aka yi na sace ki? Ai babu wanda ya gan ni gidanku kuma ban san hanyar gidanku ba”

Ina ganin ya mike tsaye ni ma na tashi sai ya dauki wayarsa ya matsa daga kusa da ni, binsa na yi da saurina.

“Kin ce ba ni ba ke”
Chapter 87 · 0% Book details