← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 127

Sashe 17

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fada da karfi ina kuka ji nake kamar na tashi na tafi har asibitin gurin likitan, wayarta ta dauka ta kira Yaya Maryam ta sanar da ita halin da muke ciki bata gama wayarba amai ya cika min baki na fara amai kamar ba gobe, lokacin na tabbatar da uwa uwa ce  babu kyama ta rike ni tana ta tausayina idan naje rufe kafafuwana sai ta bude, mikewa na yi tsari na fara yawo cikin dakin ina karanta duk addu'ar da ta zo kaina.

“Yanarukuna bardan wassalamu ala ibrahim.... Ya hayyu ya kayyun... Ya Allah na ya gwanina Allah ka kawo min sauki, wannan mutuwa da zan yi a yau ka kawo min saukinta”

Mama ta rike ni ta zaunar sai na kai kaina na leka ina kallon yadda na komai ya canja.

“Mama haka kika ji da zaki haifi Zahra? Mama ki yafe min Mama na yafe miki, da na san haka abun nan yake da ban yarda na raini cikin nan ba, na shiga uku na lalace, wayyo duniya wayyo lahira”

Sai da na yi awa daya a haka sannan Yaya Maryam ta zo, tana isowa ta sanar da Mama tare take da Dr Hamid sai na mike tsaye jiki ba tufafi zan fita na tafi waje gurin Dr Hamid din sai da Mama ta rike ni.

“Ke babu tufafi a jikin ba”

“Mama ina ruwana da tufafi wai? Kowa ya gan ni mana, ke dai baki san yadda nake ji ba”

Na fada ina son na kwace kaina domin jin nake kamar da naje gurin likitan cire min cikin zai yi an samu sukuni. Yaya Maryam ta daura min zane ta saka min Hijab.

“Yace a fito da ita ba a nan zata haihu ba?”

“To ina zai kaita?”

“Ni dai be fada min ba, amman yace na fito da ita mu tafi wani gurin”

“To kuwa da ni za a tafi, ba zan bari ku tafi ku ka dai ba da yata a wannan hali”

A take na sako fitsari mai tare da jini, Mama ta rika ni ta dayan bangaren Yaya Maryam ta rika dayan bangaren muka fito sai da aka sani ni motar Dr Hamid din sannan Mama ta koma ta rufe gidan sai Dr ya kalli Yaya Maryam.

“Da ita zamu je?”

“Eh”

Kamar yace wani abu sai kuma ya zagaya ya shiga mazaunin direba Mama ta shiga baya tare da ni yaja motar kamar zai tashi sama, kamin mu isa inda zai kai ni na fara rokon Mama yafiya ina bar mata wasiya.

“Zahra hakuri ake duk haka muka ji”

Yaya Maryam ta fada ban san lokacin da na kai mata duka ba.

“Karya kike ba haka kika ji ba, muguwa ni kadai na san me nake ji, Wayyo Babana Wayyo Deen”

Mama addu'a kawai take tana tofa min, wata private hospital muka nufa, ko da muka isa mun tararda an aje kujerar daukar marar lafiya, da alama ya shiryawa komai tun kamin a kawo ni, Mama da Yaya Maryam suka dora ni kan kujerar wata nurse ta turawa da gudunta, su Mama suna biye, wani katon daki aka shiga da ni, aka dora ni saman gado aka janyo wani karfe aka dora kafafuwana a kai. Matar ta cire zane na ta dauko wani ta dora ta rufe min kafafuwan zuwa cikina, sai ga Dr Hamid ya shigo cikin shiga irinta ta masu shiga tiyata ya rufe fuskarsa da mask hannayensa kuma da safa, ya daura drip ya saka min a hannu sannan yayi allurar a cikin ruwa, ya kalli Mama da Yaya Maryam yace su fita.

“Ku fita please”

“Aa ni babu inda zan je sai ta haihu”

“Mama babu abunda zai faru, dan Allah ki fita dan ma yana private hospital ne da asibitin gwannati ce ba za a bari ma ku shigo nan ba, dan Allah ki fita”

Daker da sudin goshi Yaya Maryam da nurse din suka lallaba Mama ta fita bayan ta bugawa Dr Hamid warning cewar idan na mutu ta rantse masa da Allah sai ta yi shari'a da shi. Hannunsa ya fara saka min a ciki sai wani ruwa ya fashe da karfi ya watso masa har a jiki da karfi yayi tsalle yayi baya sai dai haka be hana ruwan bata masa jiki ba.

“Sannu sannu”

Shi ne abun da yake ta fada.

“Ki yi nishi”

“Ya kare nishin”

“Be kare ba daure ki yi kin ga kan babynki yana kusa na fara jinsa”

Sai na yunkuro zan kai hannu na taba ni ma naji abun da ya ji sai nurse din ta maida ni ta kwantar.

“Push Zahra ki yi nishi”

Na yi nishin sai na ji kan wani abu ya tsaya min a gaba kamar ya tare kofar, ga wani azaba da nake ji a gurin kamar an yanka ni.

“Da kyau yi nishi”

Na sake gwada nishin sai na ji ba zan iya ba, gaba daya na gaji karfina ya kare, sai na kwanta a gadon kamar tsumma, duk wata dabara da Dr zai min na yi nishi yayi idan na yunkura na yi nishin sai na ji ba zan iya ba ko kuma na yi kadan.

“I can't breathe I'm so weak ”

Na furta ina tuna yadda Deen yace zai zo ya rike ni idan zan haihu, kuka nake sosai, can sai ga wani irin karfi ya zo min na nisa sai na ji abu ya fara fitowa ashe nishin haihuwa ba mutum yake yinsa karan kansa ba Allah ne yake kawo masa wannan karfin, ina sake nisawa a karo na biyu sai kukan abun da na haifa hawaye na sauko min Dr ya saka hannu ya karasa cire shi ya dago shi haka nan da jini ya doro min saman kirji.

“Kin haifi ďa namiji Zahra Congratulations”

Sai na fashe da wani irin kuka marar sauti ina kallon yadda idonsa yake rufe yana ta rusar kuka, fari ni sol kasancewata ni da mahaifinsa duka farare ne, sai dai ba zan iya shaida waya biyo ba domin babu kamanin kowa a fuskarsa, sai dai kyakkyawa ne mai dogon hanci sosai. Nurse din ta daga shi saman jikina ta yanke masa cibiya ta goge masa jiki ta mikawa Dr Hamid ita kuma ta fita ta karbo kayan jarirai, wasu tufafi ne ta shigo da su masu matukar kyau wadanda na san ba nawa ba ne domin ba mu zo da kayan jariri ko daya ba, ta saka masa ta dora shi akan wani tawul mai laushi sai Dr ya karba ya doro min saman jiki, ina ta kallon fuskarsa shi kuma yana ta aikin kwashe min jini, sai da suka gama komai suka tsabtace ni sannan ya kalli nurse din yace.

“You can go, ki ce Mama a yayarta su shigo”

Nurse din ta fice, sai ga Mama ta shigo tare da Yaya Maryam dukansu hawaye ne a fuskarsu sai ya mika musu ďan. Na tashi zaune ya cire drip din da ya saka min ina jin kamar ba zan iya zamaba saboda azabar ciwon da gurin yake min, audugar masu haihu ma da ya bani na saka sai na ke jin kamar ban zaka ta daidai ba. Ficewa yayi ya bar mu mu kadai a cikin dakin.

“Mama duk wannan wahalar da na sha bada ďan nan zan yi?”

Na tambaya ina kuka.

“To ya zaki yi da kaddara Zahra”

Mama ta amsa ni tana kallon yaron, sai ta mikawa Yaya Maryam da ita ma kuka take Yaya Maryam ta miko min shi na saka hannu biyu na karba na kai bakina na sumbanci goshinsa, na yi sauri na bude nono na zan saka masa a baki sai Mama tace.

“Zahra ana son a fara bawa yaro danino da ruwan zanzan kuma sai an wanke nono ake ba shi”

“Mama barta ta bashi dan Allah”

Yaya Maryam ta fada ta saka hijabinta ta goge min nono na saka masa a baki a take ya daina kuka ya kama ya fara sha, sai na ji wani irin ciwo kamar na cire nonon daga bakinsa.

“Rada mishi suna Zahra ki yi masa huduba a both kunensa ki rada masa sunansa”

Yaya Maryam ta fada, sai na cire nonon daga bakinsa na yi masa huduba sannan na rada masa nunan masoyina, na maida masa da nonon a bakina ina kuka. Dr Hamid ya turo kofar ya shigo rike da kwali yana ganin ina ba yarona nono sai yayi saurin dakatar da ni ya aje kwalin da sauri ya karaso ya karbe shi.

“You shouldn't”

Ya matsa da shi baya ya juya zai fita.

“Dan Allah ka bari na sake kallonshi”

Ya juyo ya dawo min da shi sai na kalleshi.

“Allah ya maka albarka”

Na furta sannan na sumbance shi, ya karbe shi na rumgume shi ina jin kamar kar a raba ni da shi.

“Wane suna kika zon a saka mashi Zahra?”

“Zaharadeen...”

Na fada muryarta na rawa saboda kukan da ke son ya ci karfina, sai ya karbe shi ya daga min kai hawaye na sauko masa ya fice da shi.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Shi ne abun da na ke ta furtawa na koma saman fadon na kwanta ya lumshe ido, sai Mama ta zo kusa da ni ta tsaya.

“Zahra”

Na bude idon na kalleta.

“Tashi”

Na tashi sai ta rumgume ni, wani irin sanyi na ji sai zuciyata ta samu sassauci na fashe da kuka da nake ta dannewa. Dr be dade ba ya dawo ya bude kwalin daya aje dazun ya dauko wata matacciyar jaririya a cikin zane ya mikawa Yaya Maryam.

“Nurse zata zo ta kaiki dakin hutawa, so that ki samu bachi kamin ku wuce gida”

Ya fada sannan ya karbi jaririyar ya maida cikin kwali ya dauki kwali gaba daya ya mikawa Yaya Maryam. Ina ji ina gani aka raba ni da ďana na fito dakin ina ta kuka zuwa wani dakin da aka tanadar min zuciyata kamar ta cire, ina jin kamar na yi ihu ga kukan da nake ma jin nake kamar be ishe ni ba, wani abu nake ji kamar na yi ihu.

“Zahra”

Muryar Anty Zainab muka ji wato yayar Abiey, sai Mama ta juya ta kalleta ita ma hawaye take haka ma Yaya Maryam.

“Lafiya?”
Chapter 17 · 0% Book details