← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 127

Sashe 113

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai Hajiya Jamila take iya girgizawa bakinta ya kasa furta komai, kamar ambaliyar kogi haka idanuwanta ke zubar da ruwan hawaye. Ummiter ta bi bayan ďan'uwanta a dakinsa na karatu ta same shi yana zaune ya daga kansa sama yana kallon ceiling sai tausayinsa ya kara kamata, ta zauna a kujerar dake kusa da shi sai ya dago ta kalleta cikin karfi irin na babban yaya ya sakar mata murmushi. A nan ta samu kwarin guiwar tambayarsa yadda aka yi ya gane gaskiya, sai ya karanta mata komai ciki har da kudinsa na auren Zahra da yayi.

“Tafi ki kirata”

“Amman Yaya ai Jamila siyen ďan ta yi, da ka bar mana shi ko dan rufin asirinmu”

“Mu da muka tsinceshi daga sama muka jin zafin rabuwa da shi, balle ita da ta dauki cikin wata tara ta yi nakudarsa ta haifi ďanta, karki biye Jamila ki aikata son kai mana Ummiter”

Ta share hawayenta ta mike tsaye, ta kofar waje ta fita harabar gidan ta doshi BQ, kamin ta karasa ta hango motar da ta tabbatar few people ne suke da kudin mallakar irinta fake nesa da BQ din kadan, Zahra dake kwance kafadar Abiey ta daga sakamakon hango Ummiter da ta yi, sai ta raba yatsunta da nasa. Abiey ya bude ido ya kalleta.

“Miya faru?”

“Ummiter ce Maybe magana zata yi da ni”

Ya kalli gaban motar, yana ganin Ummiter ya tuna inda ya san ta wato a Masarauta gurin Mama Lami, bude motar yayi ya fita ya zagaya ya budewa Zahra side dinta ya mika mata hannunsa ta rika ta fito. Cak Ummiter ta tsaya domin ba ta yi zaton Abiey ne a cikin motar ba, can kuma ta cira kafa ta karasa inda suke tsaye, ko kadan Abiey be kalleta ba domin kallon da yayi mata a mota ya wadatar da shi, idonsa na kan Matarsa wanda kallonta baya kundirar da shi. Zahra ta taka ta matsa daga inda suke tsaye da Abiey ta tsaya da Ummiter tana kallonta ta san Ummiter ba karamin kuka ta yi ba, kamar yadda Ummiter ma ta karanci damuwa a fuskar Zahra.

“Yaya yana son ganinki yanzu”

Zahra ta juyo ta dawo gurin Abiey sai dai shi bata fada masa cewar Mr Bashir ne yake son ganinta ba, domin ta san halin angonta.

“Hajiya Jamila ce take son magana da ni”

Ya mika hannayensa ya rika fuskarta yana shafawa a hankali daman can ba jin zai taba jin kunyar rika hannunta ko taba jikinta a bayyanar jama'a, balle a yanzu da take halak malak dinsa.

“Da safen na yi Hiayatee? Bata san kin kwanta asibiti ba ne jiya? Bata ma zo ta duba ki ba ko?”

Magana yake mata yana kallon kwayar idonta kamar zai maida su cikin nasa.

“Ta zo, bari na je wata kila magana ce mai muhimmanci”

“Okay”

Ya amsa mata ne kawai dan baya son musa mata, domin baya son rabuwa da ita, shi ya dauko su daga asibiti ya dawo da su gidan jiya da darea, haka kuma be hana shi tarewa a kofar gidan bayan yayi sallah asuba ba har sai da rana ta fito sannan ya shiga cikin gidan ya kira a waya ta fito. Ya Sumbanci goshinta ya rika hannunta ya murza sirara kuma tatausan yastun hannunta.

“I love you...”

Ita din ce kunya ta lullube ta, ta san duk wani unkuri da zata yi ba zai hanu daga taba jikinta ko rumgumarta ko furta yana sonta a gaban kowa ba, hakan ya saka bata yi unkurin yin haka ba. Tsaye yayi yana kallonta har sai da ta shige sannan ya rufe motar ya zagaya ya shiga side dinsa ya kuna motar. Zahra na rufe kofar falon Ummiter ta juyo tana kallonta.

“Yayana mutum ne mai karamci ba dan haka ba, daga ke har Jamila sai ya rufe ku, domin yana da iko da kudin da zai iya yin haka, amman be yi ba duk da bakinciki da kika saka masa, muna kallon ďanki a matsayin jikinmu a yau na ga hawaye a idon yayana yayi kukan da ban taba ganin irinsa ba, kuma ni ma nayi, kuma na zo ya aureki saboda Jamila ta dandani dacin abun da ta aikata mana, ko da yake yaro babu ruwansa ba shi da hakkin kowa, sai dai ki tanadi amsoshin da za ki ba shi idan ya tambayeki”

Zahra ta daga idonta ta ya fara safa da marwar hawaye tana kallon Ummiter.

“Wata kila hakkinsa ne, zai fara bibiyata a yanzu ya hana ni farinciki a gaba ko ma ya hanani samun kwanciyar hankali a gidan aurena”

“Daman mutumen da Yaya ya fada min Jamila tace an daura miki aure da shi a jiya da ba Sauban ba Abiey? Shi ya saka kika suma?”

Zahra ta daga mata kai.

“Shi ne, an daura auren ne ba tare da sanina ba, kuma ba da sanin iyayensa ba, ina tsoron abun da zai biyo baya wata kila hakkin yayanki ne duk da ban aikata da niya ba”

Ummiter ta hade yawun bakinta ta nuna Zahra hanyar da zata bi.

“Yana dakinsa”

Fitowa ta yi daga bangaren ta dawo bangaren, Hajiya Jamila ta shiga dakin Amir inda ta bar wayarta a dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta nemo number kawar mahaifiyarta wato Mama Lami ta kira, cikin ikon da iyawarsa aka amsa wayar.

“Hello Mama an tashi lafiya”

“Lafiya Kalau Ummiter, ya aikin? Kuma ya yayanki da iyakinsa”

“Lafiya kalau Mama”

“Maa Shaa Allah, kwana biyu kin daina zuwa mana”

“Aiki ne yayi min yawa Mama, Mama Abiey na gani a gidanmu yanzu tare da Zahra Nannyn da Anty Jamila ta dauka ta rika kula mata da Amir”

Sai kuma ta yi shiru, a nan Mama Lami ta samu damar tambayar.

“Miya kawo Abiey a gidan?”

“Cewa ta yi mijinta ne a yanzu wai an daura musu aure a sirrance, ba tare da sani iyayensa shiyasa na kira na tambaya da gaske ne?”

“Abiey din aka daurawa aure? Abiey dai na mu?”

“Shi fa Mama har kissing dinta yayi gabana”

“Aa ba dai aure ba, sai dai idan falkarsa ce, wato duk abun nan da na saka aka yi masa be saka ya rabu da yarinyar nan ba? Ko a yanzu ya bude kofar wata hatsaniyar ce a tsakaninsa da mahaifinsa, ai tun da har ya ki bin zabina sai ya ga abun da baya so, na gode Ummiter”

Ta katse wayar, Ummiter ta juya tana kallon gadon Amir.

“Ai kara dai ta rike ďanta ko dan rufin asirinmu, da ace matar ďan'uwa ta kawo masa ďan ba nashi ba, kara acw ya aure Nannynta, wata kila ma sanadinta ya samu nashi yayan tun da ita tana haihuwa, shi ma kuma ba shi da wata matsala....”

Karasawa ta yi gurin gadon ta leka sai ta ga wayan babu Amir.
[12/5, 12:10 AM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣9️⃣

ABIEY POV

Sai da ya fara kallon Ammy sannan ya kalli Dr Zainab ta kanta ke kasa tukuna ya karaso cikin falon.

“Lafiya?”

Dr ta dago ta kalleshi sai dai bata ce komai ba ya maida kanta kasa. Ya ga damuwa karara a fuskarta, yanayin Ammy ya nuna fada ta yi domin yana karanta kowane irin hali mahaifiyarsa take ciki, damuwa ko bakinciki ko fada da murna da farikciki. A sanyaye ya zauna yana kallon Ammy.

“Ammy kar dai kin tsare Dr da fada ne”

“Idan ban nata fada ba wa zan yi ma? Da bata biye ka da yanzu komai be faru ba”

“Ko ta bi ra'ayina ko ta ki, ba zai sauya kaddarata ta auren Zahra ba, domin na shirya yin haka ko da amincewarta ko babu, sannan kamin komai ya faru sai da na gargadeta cewar kar ta fadawa kowa wannan ya zama tsakanin mu”

Ammy ta mike tsaye ta nufi dakinta ba tare da ta sake cewa komai ba. Dr ta dago ta dubi Abeiy idonta cike da kwalla.

“Idan ban aikata ba laifi, idan na aikata laifi kun saka ni a tsakiya”

Abiey ya bar kujerar da yake zaune ya dawo kusa da Dr ya zauna yana murmushi.

“Ammy tana jin tsoron Mai Martaba ne, ba wai tana wannan abun saboda bata son Zahra ko bata son aurena da ita ba, ta san irin tsamin dake tsakanina da mahaifina tana jin tsoron abun da zai biyo baya ne”

“Tana da gaskiya Abiey be kamata ka samu matsala da mahaifinki saboda mace ba, dole zai ji ba dadi na abun da ka aikata”

“Haka ne, kuma ina fatar ba zai cilasta min zabe tsakanin shi da Zahra ba”

Ya fada yana kallon wani bangare na dakin sannan ya mike tsaye ya shafa aljihun wandonsa ya nufi dinning, wayarsa ta yi vibration da sauri ya ciro wayar ganin number Sauban ya saka shi murmushi.

“Hello”

“Ango ina amaryar taka? Ya jikinta?”

“Ta ji sauki, tun jiya aka sallameta tana gidansu yanzu ma ban dade da dawo daga gidansu ba”

“Shikenan fa ba zaman lafiya, ka auri Zahra ko?”

“Har yanzu gani nake kamar ba gaske ba ne Sauban, kuma har yanzu ina tsoron kaddarar da zata raba tsakaninku”

“Mai Martaba?”

“Mutuwa idan aka raba ni da Zahra a yanzu ba makawa na san mutuwa zan yi, Sauban na kai stage din da bana iya sauraren kowa a yanzu a game da Zahra sai zuciyata”

“Zahra ta riga da ta zama taka a yanzu Abiey, ka aje wannan a gafe ka fuskaci matsalarku so that ka magance abun da wuri tun dare be maka ba”

Ya aje cup din da ya dauka da dayan hannunsa yana wani tunanin na dabam.

“I will”
Chapter 113 · 0% Book details