← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 127

Sashe 84

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ya min dadi, sai ta taimakamin na isa gida cikin salama, Mama na tambayar dalilin dadewa a islamiya yau gashi har an kira sallah nace mata haddata ce ban iya ba. Ana gama sallah Isha'i sai na dauko wando da riga da nake bachi da su na dauki tufafina mai datti na saka a ciki yayi kamar ni din ce a kwance na lullube shi da zane, daman yau ba a dakin Mama zan kwana ba saboda yau girkinta ne Baba a dakinta zai kwana ni kuma na kwana a dayan daki. Ina ganin Mama ta fara sallah na fara samame na fito gidan cikin tsanda. Ina yin nisa na falfala da gudu sai da na kusa isa gidan Ammy sannan na fara tafiya normal. Na dan dade a gurin sannan Abiey ya fito da motarshi ina ganin ya faka na nufi motar sai ya bude min na shiga shi kuma ya fito waje a cikin motar na shirya shiri irin na canja tufafi ba na kwalliya ba domin ko man ban shafa ba balle hoda haka kuma be hana kyau na haska blue lace din ba.
Shi kanshi sai da ya yaba da yadda kayan suka karbe ni, be san garin sosai ba dan haka ni na taimaka mashi gurin kwatance har muka isa unguwar da ba ni da tabbacin ita din ce.

“But Zahra i feel like kamar ba abun kirki muke ba, i don't ko Mamanki tace ba zaki je ba”

“Already na zo kara kawai ayi hakuri sai na dawo”

Ni kaina na san ba karamin duka zan sha ba idan na dawo, sai dai a lokacin ina ganin idan bukata ta biya komai zai faru ya faru ba matsala ba ce.

“No gaskiya be kamata ba lemme take you back”

Ganin zai canja shawara na bude motar da sauri na sauka, kamin ya bude side dinshi ya zagayo ha shige wata corner da na gani a kusa da gurin, ashe hanya ce sai dai mota ba zata iya bi ba, hadawa na yi da gudu ta yadda zan mashi nisa ko da ya biyo sawuna, wata budurwa da taci kwalliya na gani na bita ina tambayarta gidan Dattijo.

“Ke dan Allah kin san gidan Dattijo inda ake bikin dinner yau”

“Biki?”

“Eh”

“Biyo ni muje”

Ba musu na bita har ina mata godiya, kamar abun arziki tun ana tafiya ina da saurana har na fara gajiya sannan muka iso wani katon guri da aka kawata ga mutane sosai a gurin sai rawa ake ta yi ana cashewa. A lokacin da na duba da kyau sai na ga ba Amaryar da nake nema ba ce wata Amaryar ce, sai dai babu yadda na iya aci kada kudi ya bace inji buzu da ya cinye lipton din shayi, gefe na koma na tsaya wata zuciyar na raya min na koma na nemi amaryar sai dai ina jin kamar ba zan gane hanya ba ga shi kafafuwan sun fara ciwo. Budurwar da muka zo tare da ita ce ta zo ta ja ni muka shiga tsakiyar filin da ake rawa ni ma na fara takawa domin har ga Allah kidan yayi min dadi, da rawa ta yi rawa ni ana baje na fara takawa da karfi can na fara hango kafafuwan masu rawa suna komawa kamar kafafuwan doki wato da kofoto amman jiki da kai na mutane, tun ina gani daidaiku har abun ya fara yawa.

Abun ka da mai yawo sai na janyo hannun budurwa na fito da ita filin.

“Ke zo mu tafi, ba wannan amaryar nake nema ba”

Bata musa min ba ta biyo ni, ina ganin mun yi nisa kadan na rike hannunta gam na jata muka fara gudu sai da muka yi nisa sosai sannan na sake ta ina fadin.

“Ke wannan bikin fa ba na mutane ba ne, Wallahi bikin Aljanune ke baki ga kafafuwansu ba irin na dawakai da kofotai”

Dariya ta yi ta dago min kafarta daya sai na yi arba da kafar dokin ita ma.

“Irin wannan?”

Ziippppp fisari suka zubo min, hanji suka fara kuka hawaye sallama alaikum jiki sai rawar sanyi yake, dukawa na yi a gurin na rike kafar na fashe mata da kuka.

“Ki taimaka dan Allah ki yi hakuri, Wallahi kuskure aka samu ba bikinku na zo ba bikinmu ne zan zo, kuma subutar baki na yi, ki yafe min ya ke wannan aljana”

Kamar na rike doke haka na ke jin fatar kafarta da gashi da kofoto, kamar ance na dago sai na hango Abiey yana haske inda muke da waya.

“Zahra gurin nan fa daji ne miya kawo ku nan? Na kasa na natsuwa na tafi na barki ne, na tambaya aka ce an ganki da wata kun biyo hanyar nan”

Waiga na yi ina karewa gurin kallo ashe kuwa daji ne mai kama da tsohuwar unguwa, yana karaso kusa da ni na mike tsaye da sauri hawaye sharrr.

“Miya same ki? Shiyasa na kasa tafiya idan wani abun ya faru ni za a dorawa laifi, baiwar Allah miya faru”

Ya karasa yana kallon budurwar sai na ji wani sanyi sanyi a raina, ashe ba ni kadai nake ganinta ba, matsawa na yi baya ina son fada mashi cewar ba mutum ba ce kuma bana son ta gane.

“Kofotosss kofotossss kofotossss”

“Minene wai? Are you okay?”

Da na fahimci ba ganewa zai yi ba, sai na risina cikin hikima na cire talkamina na saka hannuna na dauka na mike tsaye na watsa da gudu.

“Wallahi ba mutum ba ce kofoto gareta kafafuwan doki, ka shiga uku Abiey....”

Na fada da karfi ina gudu kamar mai gasan tsere, wata kila ya kalli kafafuwan nata wata kila kuma kalamai na ne suka tsorata shi sai hango shi na yi ya wuce ni a guje @360 ko waigo ni be yi ba, a nan ni ma na watsar da talkamin hannuna na ce kafa miye na ci ban baki ba, yau ga ranarki.
[11/20, 9:09 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣4️⃣

Murnushi yake kamin dariya ta subuce masa sai ya saka hannunshi ya kare bakinshi yana girgiza kai, ni ma murmushin na yi na sauke kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna, jin karar taba kofa ya saka na dago na kalli kofar, Hajiya Jamila ce ta shigo rike da Amir tsaye ta yi cirko tana kallonmu musamman ma mijinta da har yanzu yake dariya, a take murmushin da ke fuskata ya gushe na nemi natsuwata na maida ta a jikina.

“Lafiya kuke dariya?”

“Na ke yi dai...”

Ya amsa mata still dariyar bata gama saukar masa ba, sai ta shigo tana kallona.

“Miya ya saka dariya Hubby?”

Ya daidaita natsuwarshi ya nuna mata wayarsa dake kusa da shi.

“Wani labari na karanta”

Ta kalli wayar ta sake kallona kamar mai zargi ta nufo ni da Amir.

“Karbi yaron nan Zahra”

Na mika hannu biyu na karba shi sannan na mike tsaye.

“Yaron nan yana kama da Zahra ko kin kula da haka”

Da sauri ta kalleshi da duba irin na firgici da tashin hankali.

“Kama kama kama da Zahra kuma? Miye hadinshi da ita da zai yi kama da ita?”

Yayi murmushi yana kallona hankali kwance.

“Kin ga ita ma fara ce da ta dauki yaron nan sai ma yayi mata kyau”

Ta sake kallona ta dauki lokaci tana ba idonta abinci a jikina sannan ta ce min.

“Zahra ki tafi falo ki rarrashi Amir yayi bachi”

“Toh”

Na amsa mata sannan na juya na fice zuwa falonta, safa da marwa nake ta yi a falon ina shafa bayan Amir, tunawa da Abiey ya saka ni murmushi. Ina zaune a dakin har Amir yayi bachi sai na haura sama na shiga dakinta na kwantar da shi a hankali na sumbaci goshin ina kokarin kai hannu na shafa kanshi na ji ta ce.

“Karki sake, sumbartansa ko shafa jikinshi ko yi masa duk wani abu da zai sanya kusanci a tsakaninku aikinki a gidan nan bashi nono ne kawai, abu na gaba kuma karki sake kebewa da mijina ya zama na farko kuma na karshe, ke mai kula da yaro ce kawai ki saka wannan a zuciyarki”

Mikewa na yi tsaye cike da mamakin furucinta da yanayinta ta ya sauya a take.

“Lafiya Hajiya?”

“Lafiyar ce ta kawo haka you can go”

Da mamaki na fito dakin har na isa bq tunanin be ayyana min komai daga canjin fuskar Hajiya Jamila ba, zuciyata bata raya min kishi take ba domin ban ga dalilinta na kishi ba ta fi ni nesa ba kusa ba, ita a yanzu matarshi ce tana da kudi kuma tana da jiki mai kyau, ni kuwa idan aka cire kyaun fuska miye na ke da shi da Alhaji Bashir zai duba yace yana so na, domin ko yar kibar nan ta matan aure ni Allah be bani ba yadda na ke lokacin da ina budurwa a yanzu ma haka nake a bushe musamman kwana biyun nan da nake cikin tashin hankali da rashin natsuwa. Mama ma tayi mamakin furucinta a domin da na labarta mata abun da Hajiya Jamila ta yi min, sai dai ita ta dora awon a misalin kishi ne, ni kuma ina ganin kamar ba kishi ba ne bakin hali ne kawai irin nata, daman can farko ta nuna min daga baya kuma ta dawo neman taimakona har tana rokona tana kuka, wata kila tana ganin a yanzu ta wadatu da abun da take nema a gurin shiyasa ta fara neman hanyar wulakanta ni, a daren na kwana da begen Abiey a raina labarin da na tsakurawa Alhaji Bashir ya saka ni nisawa a duniyar begenshi.
Washe garin bayan na yi sallah na yi karatun kur'ane rana ta fito sai na kwanta kamin mu kulla alaka da bachi wayata ta yi ringing, kiran Sauban ne kai tsaye for the first time na ji ina bukatar amsa kiran cike da nishadi.

“Zahra”

“Na'am An tashi lafiya”

“Ba lafiya ba, domin ban san yadda kika kwana ba, shiyasa na ce ba zan turo miki sako ba sai dai na kira na ji muryarki”

“Na kwana cikin tunani da begen abokinka, Sauban kana da hotonshi ka turo min”
Chapter 84 · 0% Book details