Sashe 56
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na goge sakon bayan na gama karantawa ni kaina ina bukatar magana da Abiey sai dai bana son silar daukar wayar Abiey ya tambaye ni inda nake balle har yace zai zo, bana son Mama ta sake ganin laifi hakan kuma ba yana nufin na hakura da Abiey ba, amman a halin yanzu ya kamata mu nisanci juna har zuwa lokacin da Mama da Baba za su huce.
Muna cikin wannan halin Kawu ya dawo yana samun labarin abun da ya faru ya rufe ni da fada kamar zai doke ni, ni dai ban da aikin kuka babu abun da nake yi Yaya Maryam na rarrashina ita ma ya rufe ta da fada yana fadin ita ke goyon bayana. Ina kwance jikinta wayar dake hannuna ta yi ringing kiran Dr Hamid ya shigo.
“Wayar waye? Waya kira ki?”
“Dr Hamid ne...”
Na amsa cikin kuka ina da tabbacin rashin amsawar zai iya saka Kawu ya doke ni ma domin ranshi ya bace sosai.
“Ba ni wayar”
Na miko min hannu sai na mika mashi wayar jiki na rawa, bude bayan wayar yayi ya cire karamin batir din ya cire line biyu daya Mama daya kuma na Surukarshi sai ya saka su duka biyun a baki ya taune ya jefo min wayar.
“Allah yasa na ga kin sake kiran shi ko kin kwatanta mashi kofar gidan nan ki ga yadda zan karyaki”
“Gaskiya kam yanzu ina amfanin haka auren uwa ya mutu, ke ma ai ba jindadinki ba ne”
Mama Sa'adatu ta kara da nata, aiko kamar ta sosawa Kawu inda yake mashi kai kayi sai ya ce.
“Bar marar hankali ko sunanshi na sake ji a bakinki sai na kusa halaka ki”
Haka dai na wuni cikin takura da fadan Kawu, bayan sallah Magariba Mama da ni muka kama hanyar zuwa family house dinsu, daman Yaya Maryam tun da yamma ta hau napep ta koma gidanta, ko da muka je can sai hankalinsu ya tashi, wai suna ta kiran wayar Mama ba su samu ba tun a lokacin da suka samu labarin abun da ya faru a media kuma sun je can ba su samu kowa ba, abun ka da gidan taro maganar kawai suke ta yi sai dai su ba kamar Kawu ba basa dora min laifi wasu ma basa ganin laifin Abiey sai na Baba, manyan gidan suka ce ai sasantawa za'ayi amman sai nan da kwana biyu idan ya huce tukuna. Dakin wani Yayanta muka zauna ni da ita suka kawo mana abinci, ni kam dai ko kallon abinci ban yi ba domin ba shi ne a gabana ba, Mama dai ta ci kadan ta wanke hannun sai na miko mata ruwan sha da aka aje mana ta karba ya sha.
“Mama na ce ko naje na ba Baba hakuri akan abun da ya faru?”
Shiru ta yi alamar nazari sannan ta kalleni.
“Idan kika ba shi hakuri a yanzu zai yi tunanin saboda ya maida aurena ne”
“Idan kuma aka dade ban san iya abun da zai biyo baya ba, kuma idan ma yayi wannan tunanin ba laifi ba ne, ko da na yi wayo na bude ido da aurenku na ganku be kamata saboda ni aurenku ya rabu ba, na san abun da Abiey yayi be kyauta ba amman na tabbatar be yi haka dan ya tozarta ni ko kuma ke ba a matsayinshi na mijinki sai dai ya kalli abun ne ta wata fuskar ta dabam wato ta bangaren Deen shiyasa ya aikata abun da ya aikata, Mama ki ba ni dama na je na bashi hakuri ai shi ubana ne kamar yadda kika ce”
“Shikenan amman ki bari sai da safe”
“Da dare ya fi sirri Mama, kara na tafi tun a yanzu ba sai gobe ba”
“To ki dawo da wuri kar a fara tanbayar ina kika je, idan kuma kin hadu da wani ya tambaye inda zaki je da dare ki ce kaya zaki dauko a gida”
“Toh, amman Mama ya zamu yi da gurin da aka rushe?”
“Haya zamu kama Zahra, wannan neman aure na Abiey ya zame mana fitina tun farkonshi har kawowa yanzu”
Na yi shiru ban ce komai ba, daman me zan ce kare Abiey zan yi? Ko kuma Mama zan shigarwa mu taru ni da ita mu zagi Abiey, idan har akwai mai laifi to Deen domin shi ya haddasa komai. Da sanďa na fita gidan da sunan zuwa gurin Baba sai dai ni zuciyata tana a gurin Abiey ne, musamman cewar da yayi zai saka a nemo ni kuma na san zai iya, ni kuwa ba jindadi ba ne ace ya zo gurin a wannan, shi kanshi ban san halin da yake ciki ba kuma ba san yadda yake so zai shiga damuwa be ji daga gareni ba, kamar yadda ni ma bake son tambayar shi wasu abubuwan. Amman ya zan yi? Gidan zanje?
‘No be kamata ki je ba, duk bayan gargadin da Ammy ta yi miki? Idan ma kin je me zaki ce? Gani kin zo ganin Abiey?’
Wata zuciyar ta fada min, hakan yasa na cire abun a rai na, ina isa titi na fara taron Napep biyu da suka wuce cike suke da mutane hakan yasa ba su tsaya ba, ina kokarin na tari ta ukun da zata wuce na ga wata mota da ta wuce ni ta dawo baya ta tsaya daidai inda nake, kokarin kaucewa na yi sai matukin motar ya sauke gilashin motar ya kira sunana.
“Zahra...”
Tsayawa na yi sai dai ban dawo ba, sai ya kara yin baya da motar ya tsaya daidai inda zan ganshi ya kunna wutar motar na ga fuskarshi sannan ya bude motar ya fito ya zagayo inda nake tsaye.
“Zahra ina zuwa haka cikin dare?”
“Wani guri zanje”
“Ina wayarki?”
“Daman ba ni da waya ta Mama ce nake saka line na kuma gini ya fado mata ta lalace”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Zahra na ji abun da ya faru abu be yi dadi ba, amman ina da tabbacin aboki ba zai saka a rushe muku muhallin ba, shi kanshi abun ya dame shi yanzu haka Ammy ta kira ni wai tun da ya shiga ďaki fito ba har yanzu and i know damuwarshi ba zata wuce abun da ya faru yanzu ba, kin yi magana da shi?”
Na girgiza kai alamar aa ina waige waige kar wani ya gan ni a gurin.
“Family house din Mamana a nan yake za a iya ganinmu”
“If ba matsala zamu iya shiga mota mu yi magana, na ga ma kamar fita zaki yi”
Ya sake waigawa ko'ina sannan na bude front seat na shiga na zauna shi kuma ya zagaya ya shiga side dinshi yayi ma motar key muka hau titi.
“Da zaki min dadin rai da na kira Abiey kun gaisa ko kuma na kai ki gidansu domin yana can kwance babu lafiya”
A take hankalina yayi matukar tashi.
“Ba sai na je gidan ba, amman ya jikinshi?”
“Da sauki za a ce, amman Zahra gidan ai ba bakonki ba ne, idan ma baki son shiga ciki zaki iya tsayawa a waje sai na kira shi, tsakani da Allah ba zai jidadi ba idan na fada mashi na hadu dake ban kawo ki ba, idan kuma kin yarda ki fada min gidan da kike zan dauko shi na kawo shi a halin rashin lafiyar da yake ciki”
“Aa bana son ya san gidan”
Na fada ina jin tausayinshi na kara cika min zuciya.
“Okay amman zaki yarda ki mu je gidan? Na san Abiey yana son magana da ke sosai, ke kanki ba zaki rasa abun da zaki tattauna da shi ba”
Na yi shuru ina nazari, wannan ce kadai damar da nake da ita da zan yi magana da Abiey, kuma idan ban aminta na hadu da shi a yanzu ba, wata kila Sauban zai iya takurawa sai ya san inda nake zama a yanzu, wanda hakan ba alheri ba ne a gareni a yanzu, domin Kawu da Mama da sauran yan'uwanta za su yi zaton kamar abun da ya faru be dame ni ba ne, ni ma kuma ina son ganinshi ko dan sanin halin da yake ciki so that na samu peace of mind.
“Amman ba zan shiga cikin gidan ba”
“Yeah ba sai kin shiga ba zan iya fada mashi sai ya fito”
Kusan zan iya cewa kamar Sauban yayi min dole ne, domin har muka isa gidan ban daina wasi wasin zuwa ko akasin haka ba, na samu kaina da tsananin faduwar gaba a lokacin da aka bude mana gate din gidan.
“Na ce maka ba zan shiga ciki ba”
“I thought can cikin gidan kike magana gurinsu Ammy, nan ai harabar gida ne, kuma zai fito sai ku zauna a mota ku yi magana”
Ya fada mini amman hakan be saukar min da natsuwa ba, sai a yanzu nake ganin rashin dacewar zuwa na, da dai a da ne da Ammy bata min cin mutunci ba, ko da yake wacan karon ma fusata ta yi na marin da na yi ma ďanta, na san kuma ko ba ita ba ko da wata uwar ce abun da zata aikata kenan. Wayarshi ya dauka ya fara kiran Abiey sai da ya jera mashi 3 Missed calls Abiey be daga ba, sannan ya kalleni.
“Bari na shiga na yi magana da shi”
“Amman dan Allah karka bari Ammy ta san muna tare”
“Okay amman saboda me?”
“Be dace na zo ba, kamin Ammy ta yi min gargi akan Abiey”
“Abiey ya fada min amman wacan lokacin ai saboda kin nunawa Abiey tsana ne yanzu kuma kauna kika nuna mashi, dadi ma zata ji kuma zata san a yanzu babu komai tsakaninku sai soyayya, Zahra yadda kike da Ammy be takama ace yanzu wani abu ya shigo ciki ba, ko da wani abun kika yi kamata yayi ki nemi yafiyarta”
“Na ji amman ba yanzu ba Sauban”
“Shikenan bari na shiga na yi mashi magana”
“Toh”