← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 127

Sashe 95

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban yi zaton wata matsalar zata bullon min a bayan wannan da nake ciki ba, da san abun da Sauban zai zo min da shi kenan da ban yarda na kira shi ba, kuma a lokacin da ya zo da ban yarda mun hadu ba. Ko da Mama ta dawo ta tararda ni kwance galala na ci kuka har na gode Allah idanuwana sun yi sundun sundun, daman can bana dauka abu da wasa balle kuma wannan, yaushe Sauban ya lalace ya fara gurbata tunaninsa har zuciyarsa ta daya masa yayi min bazarana da wannan, da gaske zai aikata abun da yake da kudiri akai idan na ki amincewa ko kuma dai ya fada ne! Na rasa amsar tambayar tunani da tashin hankali suka ki sakin kwakwalwata, duk juyin duniyar da Mama ta yi na fada mata dalilin kuka ban fada mata ba, a lokacin da na lura da ta damu sai na fake da cewar korar da Jamila ta yi mana ne ya saka ni kuka, Mama ta yi ta tausasar zuciyata sannan ta yi min albishir da cewar gobe zamu koma gidansu da zama wato family house dinsu da muka baro, kamin a samu gidan haya.
Ana gama sallah Magariba sai ga Dr Hamid ya shigo gidan, kamin ya shiga bangaren Hajiya Jamila ya kira ya sanar da ni yana waje kuma yana son na nema masa izini gurin Mama zai shigo yayi magana da ita. Na sanar da Mama ta bada umarni sannan na fada masa sai yace na fito na yi masa iso, ba tare da tunanin komai ba na saka mayafina na fito, sai na same shi a inda ya saba tsayawa, cikin rashin kuzari irin na wadanda suka rasa madafa na karasa gurin na yi sallama ya amsa min, muka gaisa sannan ya mika min ledar hannunsa.

“Aa na gode”

“Allah yasa ba laifin da kanwata ta yi zai shafe ni, na kira na sanar da ita cewar ina nan zuwa sai ta fada min irin kwabar da ta yi”

“Tana da gaskiya wani gurin ai, ko ni ce ba zan yarda mijina ya kula wasu ba”

“Ashe ke ma kina da kishi kenan, ki ce na shirya wa kishinki ba sauke kenan”

Na sauke kai kasa cike da tunanin manufar furucinsa, dariya ce ta biyon bayan maganar da yayi sannan ya dara da cewa.

“Ko ma dai minene bata kyauta ba, kuma ba ta yi abun da ya dace ba, ai hallacin da kika yi mata ko da mijinta kika ce kina son auren be kamata ta daga ido ta kalleki ba balle har ta nuna kishinta akai, amman dai na yi mata fada sosai kuma na nuna mata illar abun da ta aikata, na kwantar mata da hankali na fada mata cewar kina da wanda zaki aura Allah yasa ban yi karanbani ba”

Wannan karon da kamar zolaya yake maganar, ni kam tawa ma ta isheni yanzu ba zancen tashin gidan ko wulakancin Jamila ne a gabana ba, matsalar Sauban ce data kunno min take chaja min kwakwalwa a yanzu.

“Zahra kamar akwai damuwa sosai a tare da ke”

“Ba komai”

Na amsa ina saka hannu na share hawayena.

“Ki kwantar da hankalinki ba, zamu cigaba da zama nan na wani lokaci kawai ba sai an dade ba”

“Ba zai yiyu mu zauna ba, Mama ta riga ta yi magana da Yan'uwanta za su sama mata gurin da zamu zauna na gode da kulawa”

“Shiyasa nake son na yi magana da ita, wata kila zata fiki fahimta da saurin saukowa”

Na daga kai na kalleshi a kaikaice.

“Na yi nadamar duk wani abu da na yi Dr Hamid, da ban yarda zan iya ceton rayuwar da ba a hannuna take ba da yanzu ban shiga duk wannan halin ba, na kasa ganewa talauci ya saka na aikata abun da na aikata ko kuma wauta da rashin yardar da kaddara”

“Idan har magana kike ta yarda da kaddara to ya kamata wannan kadarrar ma ki yarda da ita ki watsar da komai ki dauka haka Allah ya hukunta miki a yanzu ma ki rumgumi komai da hannu biyu, kuma ina mai tabbatar miki komai zai wuce nan ba da jimawa ba”

“Ina fatar haka, ni kadai na san abun da nake ji a zuciyata, ji kadai na san halin da nake ciki, na rasa abubuwa da suka kamata su kasance da ni, na ruguza farincikina da kaina, na rasa makama, da ban aikara abun dan na aikata ba da kanwarka bata zarge ni akan mijinta ba”

Na durkushe a gurin ina jin zuciyata na mini wani irin zafi da zogi na azabar bakincikin da nake ciki.

“Ba ke kika bukaci zama a gidan nan ba, Jamila ta janyo ki saboda haka babu laifinki idan mijinta ya nuna miki kulawa, kuma ai ita da bakinta ta fada cewar mijinta yana neman hanyar da zai saka miki da abun da kika masa, shin tana tunanin zai rika daure miki fuska ne ko kuma ya kareki? Daman can Mr Bashir mutum ne mai son mutane, kar abun da ta yi ya dame ki”

A tunaninsa ina kuka ne saboda abun da Jamila ta yi min ne kawai, na haka na kaune kashina daya tsaya min a wuya na share hawayena na masa iso gurin Mama, a gaban ya aje ledar hannunsa sannan na durkusa har kasa yana bata hakurin abun da kanwarsa ta yi, wata kila ya cilasta shigowa bangarenmu ne domin yana tsaka da bata hakurin Hajiya Jamila ta shigo ita na ta soma bata hakuri sannan ta dawo kaina tana neman yafiyar abun da ta yi min. Uffan ban ce mata ba domin bata da kimar da zan iya yi mata wani furucin a yanzu, Mama ma ina tunanin ta hakura ne kawai saboda Dr Hamid dake ta yi mata magiya, sai dai hakurin da ta yi ba yarda ta zauna a gidan ba ne ta tabbatar musu da cewar ta hakura amman zancen tashi yana nan domin ta sanar da yan'uwanta.

“To ko dai sai na kira Mijina ya baku hakuri ne”

“Baki bukutar haka ranki ya dade, ai na riga da na hakura, amman idan na ce zan zauna a yanzu ai abun ya zama da rainin hankali yan'uwana ma za su ga kamar na mayar da su kananan mutane”

“Zan iya zuwa da mijina mu ba su hakuri”

“Hajiya ba sai kun yi haka ba, zuwan ku zai kara bata lamarin ne kawai domin ban fada musu cewar kin kore mu ba, kawai dai na fake da cewar ina son na bar gidan ne saboda tsare tsaren gidan basa min dadi”

“Mama idan haka ne ai zamu iya zuwa mu baku hakuri mu ce su lallaba ku zu zauna, ni kaina ba wai ina son ku zauna na lokaci mai tsawo ba ne, zaman ku a nan ba zai wuce wata daya ba, na miki alkawari Mama zan sama muku gidan da zaku zauna na kanku, ko bayan ni Mr Bashir ma bana tunanin zai barku haka”

Da ďaďan kalamai da kallamewa da komai suka tirsasa Mama da amince da zama a gidan, bayan Dr Hamid yayi alkawarin zai dauki yar'uwarsa su tafi har gurin dangin Mama su ba su hakuri da neman su barsu su cigaba da zaman gidan.
Kamar yadda ya fada washe garin ranar Dr Hamid da Hajiya Jamila suka saka mu a mota ni da Mama zuwa family house dinsu, su kansu su yi na'am da Dr Hamid da kuma kanwarsa a tunaninsa tana son mu ne tsakani da Allah ba dan wata manufa ba, sai bawa suke suna saka musu albarka. Goma ta arziki Dr Hamid yayi musu sannan muka fito gidan, a hanyar mu ta dawowa gida na ke jin Jamila na fadawa Dr Hamid cewar mijinta yayi balaguron wani aiki na kwana biyu, da muka dawo gidan yana ta kara bawa Mama hakuri, ni kam na zama kamar wani hoto domin babu wata wadatacciyar walwala a tare da ni, hirar da zan iya cewa ma tursasa ni yayi ma tsaya ina yinta ba dadi take min ba.

Ban dauka da gaske Sauban yake ba har sai da na lurar da barazanarsa na kokarin yin yawa, domin kullum sai ya turo min sako yana kara jaddada min kudirinsa, idan na koshe wannan line sai ya aiko min da wani, daga baya sai na kashe wayar gaba daya na aje, da ya fahimci na daina amfani da wayar sai ya koma aiko min sako ta hanyar masu gadin gidan, kamar wani dan'adan haka Sauban ya rikide min ina ta mamakin abun da ya same shi har haka.
[11/24, 10:14 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣0️⃣

Na dauki damuwa da tunanin abun na saka a raina har ta kai bana iya zaunawa na ci abinci yadda ya kamata, ga kuma tsutsata da Amir yake sai ya kara sakawa na zama wata yar tsana daman can ba wani abun kwarai ke a jikin ba balle kuma yanzu da bana da wani abun yi sai tunani da neman mafita, idan kuma na nemi shawarar zuciyata sai ta fada min na amince da kudirin Sauban gudun kar na sake jefa kaina da mahaifiyata a cikin wata damuwar, Dr Hamid ma yayi ta neman sanin abun da yake damuna amman na gagara sanar da Mama ma balle kuma shi da nake ganin ba shi da wata alaka da ni. Sati daya na sakwana bana komai sai addu'a da raya dare da sallah nafila ina neman Allah ya kawo min mafita sai dai ban ga alamar bullowar wata hanyar ba.
Ranar da muka cika kwana takwas da maganar Sauban ya sake zuwa gidan ya faka a harabar gidan ya aiko yana min sallama, ina jin sunansa gabana ya fadi domin na san ba alheri ne ka kawo shi a yanzu ba, tun daga wacan lokacin da yayi min barazana zuwa yau idan ya sallamo a gidan sai na ji kamar na haka rame na binne kaina na huta, a yau sai na kekashe kasa na ce ba zan fito ba.
Chapter 95 · 0% Book details