Sashe 36
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tambayar da yayi ma kansa kenan har lokacin be daina mamaki ba. Few minutes later Sauban ya turo masa sakon address din, da hannu daya Abiey yake driving dayan hannunsa kuma rike da waya har ya isa unguwar.
Tun daga yanayin area kasan area ce da manyan mutane masu fada aji kuma wandanda suka taka nesa da kafafuwansu suka tsaya, babu gidan da be nuna isar mai shi a unguwar titi ma tsif yake kamar an yi ruwa an dauke baka jin komai sai motsi dogayen itatuwan dake kadawa saboda hadarin da ha hadu a samaniya har ya rufe taurari. Police din da ya gani a kofar gidan da ya banbanta da saura ya tabbatar masa da cewar gidan ne, kai tsaye ya isa gaban gate din ya danna horn sai police suka taso shi kuma ya sauke glass din motarsa.
“Sannu da zuwa”
“Yauwa Mai gidan yana ciki?”
Police dake son tantance fuskar Abiey ya ce.
“Kana da appointment da shi?”
“Yeah ka fada masa Abiey ne Mai Martaba ya turo ni”
“Allah sarki ni kam na ce kamar Abiey sannu da zuwa ranka ya dade”
A take suka bude masa gate din ya kunna kai cikin gidan mai kama da wata masarauta a gurin da aka tanada domin aje motoci ya nufa ya faka motarsa yana tsara yadda zai amsawa Mai gidan idan ya tambaye dalilin zuwansa, mutumen da ya gani a kusa da motarsa ya saka ya sauke gilashin motar.
“Ya aka yi?”
“Sai ka juyo da motar ranka ya dade masaukin bakin ta can yake”
Abiey ya bude gurin da yake ajiyar kudi a cikin motar ya dauko bandir din 500 ya mika masa.
“Shiga cikin gidan nan gurin matansa ka ce Abiey yana sallama da Zahra”
Mutumen ya saka hannu biyu ya karba jiki na rawa yawu ma magana.
“To ranka ya dade”
ZAHRA POV.
Da hannu Ummiter ta nuna min ďakin Hajiya Jamila sannan ta juya tayi tafiyarta, a lokacin falon babu komai amman gudun yin laifi ya saka ban hau stairs din ba na dawo na zauna a kasa har na tsawon lokaci. Ganin bata fito ba kuma wani wanda zan iya cewa yayi mata magana be fito ba yasa na tashi na fara taka stairs din har na haye sama tsintar kaina na yi a wani guri mai kama da karamin falon sai dai wannan dakunan ne a jere wasu kuma suna kalon juna, daki na biyu na nufa kamar yadda ta fada sannan na kwankwasa ban ji an amsa ba, hakan kuma be saka na kasa kwankwsawa a karo na biyu ba haka na kwankwasa har sau uku jin ba a amsa min ba ya saka na murda kofar dakin na shiga da sallama.
“Ba a shigo min ďaki Zahra sai na bada izini”
“Na yi ta kwankwasawa ba amsa min ba”
“Tun da kika ji ban amsa miki ba ai kin sa ina uzuri”
Na yi shiru ban ce mata komai ba, a yadda na lura Hajiya Jamila na da wani irin izza da nuna isa da son wulakanta mutane. Haka ta bar ni a tsaye a jikin kofar har sai da na gaji da tsayuwa na juya zan fice sannan ta yi min magana.
“Ina zaki je? Ki zo ki ba shi nono mana”
Na juyo na dawo kusa da inda take zaune, na karbi yaron na zauna kan kujera na bude nono na saka masa rigar baki tare da Bismillah, wani irin dadi ne ya ziyarce ni sam yau ko ciwon da nake ji idan ina matsa nono ban ji ba, tashi ta yi ta rufe dakin da key sannan ta juyo ta kalleni
“Idan kin gama bashi nono ki dora shi akan gado, ga blanket nan a kasa ki shimfida ki kwanta”
Na kalli blanket din dake aje a kasa na kalleta.
“Ko dai baki san inda na fito ba be kamata ki wulakanta ni ba”
“Au to da miye nufinki? Ki hau saman gadon miliyan uku ki kwanta? Ni na kwanta ke ki kwanta?”
“Kudi ba hauka ba ne Hajiya Jamila, kuma ni ba aiki na zo yi miki ba taimako kika nema kuma na yi miki, na fi karfin wulakanci”
“Alhamdulillah tun da har kin san ina da kudin, taimako kuma ke ake yi ma alfamar”
“Ni dai na ke muku alfamar ko ba komai kin ci amfanina tun da na baki abun da kudin da kika takama da su ba su ba ki ba”
Ina ganin yadda ta bata fuska na san kalamaina ba su yi mata dadi ba.
“Kudi sun biya bukata domin sun siya min abun da baki san kimarsa ba, kin zubar da darajarki ta uwa, kara ni neman haihu ya saka ni aikata abun da na aikata ke kuma fa?”
Na sauke kaina kasa ina jin rashin kyautawar abun da na aikata.
“Ba a haife ki ba Zahra, ba ayi wata ďiya mace da zata tako har cikin ďakina ta fada min bakar magana ba, aje min yaro karki shayar da shi bakin nononki”
Ta furta da karfi sannan ta nufi wayarta ta dauka ta kira Dr Hamid tana ta masifa a waya har da su rantsuwar ba zan kwana a gidan ba. Ni ko sai na ji kamar na ce ta yi hakuri saboda na samu kasancewa da ďana. Tana gama wayar ta jefar da ita kan gadonta ta nufo ni ta karbe yaron da karfi bana son na yi kokuwa da ita ďana ya ji ciwo hakan yasa na sakar mata ta cire bakinsa daga nono sai ya fashe da kuka.
“Fice daga ďaki.. Wawuyar banza kazama”
“Kazamar da ta yi miki amfani ba, wawuya kuma bata wuce ki ba wanda ke wulakanta matar da ta taimaki rayuwarta ta rufa mata asiri”
Na fada a fusace sannan na juyo na nufi kofar na bude na fito, ban san miyasa Hajiya Jamila ta son wulakanta ni ba, daga taimako sai kuma abu ya koma da cin mutunci kamar wata Kishiyarta. Falo na dawo na zauna sai da na zabi kujerar da nake kyautata zaton tafi sauran tsada sannan na zauna zuciyata har bugawa take saboda bacin rai, ba dan kura ta yi lafiya ba karnuka har sun isa su yi mata haushi. Ina zaune akan danna door bell din falon sai na tashi da sauri na isa gurin kofar a zatona Dr Hamid din na da ta kira ya iso, sai dai ina budewa sai na yi arba da wani mutumen da ban sani ba.
“Barka da dare dan Allah ki ce ma Hajiya wai Abiey yana sallama da Zahra”
Da mamaki na kalli bayan mutumen sai dai ban hango kowa ba.
“Ina yake?”
“Yana ta can gurin motoci”
Na kara bude kofar na saka takalmina na fito ina da mamakin waya fada masa ina? Miya zo? Anya ni Zahra? Kuma Abiey dai wanda na sani ko wani. Bayam mutumen na bi sai ya nuna min inda wata bakar mota take fake, tsaye yayi na ki na karasa ina ta kallon motar sai gashi ya bude motar ya fito fuska ba yabo ba fallasa ya doso inda nake, be karaso ba yaja ya tsaya yana kallona.
“Da gaske ke ce?”
Na kalli ko'ina na gidan tunawa da na yi da Dr Hamid yace min akwai camera a gida na karasa kusa da shi.
“Me kake yi a nan?”
“Ke zan tambaya? Miya kawo ki nan?”
“Ba ruwanka, ka fita sabga ta”
Na juya sai na ji an riko dantsen hannuna an jiyo da ni da karfi.
“Zahra saurareni mana, mi zai saka ki zo aiki a gidan nan? Me kika rasa?”
“Ban sani ba, and for your information karka sake zuwa gidan nan”
“Sai kuma me?”
Na kalleshi da kyau sannan na furta.
“I hate you”
“And...”
“I hate you na tsane ka”
“And...”
Na rasa kalmomin da zan hada na fada masa maganar da zata masa zafi domin na lurar wadandan basu jika shi yadda na ke so ba. Muna cikin wannan halin aka haske mu da mota kamin daga bisa aka kashe fitilar motar mai motar wanda Dr Hamid ne ya faka a kusa da inda muke tsaye har lokacin Abiey na rike da cinyar hannuna dake cikin hijabi.
“Lafiya?”
Shi ne abun da Dr Hamid ya fara tambaya a lokacin da ya fito motar, sai Abiey ya sake ni ya kalleshi.
“Okay kai ka kawo ta nan kenan?”
Dr Hamid ya kalleshi irin duba na tsanaki sannan ya kalleni.
“Wuce mu je ciki Zahra”
“To ta shiga mu gani”
Abiey ya fada yana hade fuska kamar ba shi ba, haka nan kuwa na samu kaina da masa juyawa na koma cikin gidan kamar yadda Dr Hamid ya bukata.
“Shiga mota”
Dr Hamid ya fada, nan ma ina cira kafa Abiey ya ce.
“Karki shiga motar nan”
Ni dai kam na yau san Abiey ba a banza ya zo min ba, sai da yayi min asiri domin umarninsa na bi na kasa shiga motar.
“Miye tsakaninki da shi?”
Dr Hamid ya tambaya.
“Karka sake tambayar abun da yake tsakanina da ita, and karna sake ganin inuwarka a inuwarta, ke kuma tun har kin fi son haka mu zuba zuwa ni da ke i will show you my other side”
Ya karasa yana kallona babu wasa a maganar shi kamar yadda fuskarsa ma ta nuna.
“Shiga mota mu je”
A nan kam Allah ya ba ni ikon karya sihirinsa na ki bin umarninsa amman ban iya furtawa ba sai hade hannu da na yi na juya na nufi gate ina takawa da kafafuwana a lokacin har an fara yayyafi, haka na isa gate din suka bude min na yi tafiyata na bar su can a tsaye sai da na yi nisa na fara jin tsoro ga ruwa ya fara karfi kamar na juya na koma sai ga motar Abiey ta faka gabana, bude motar yayi ya fito ya nufi bayan motar ya bude ya dauko hula da wata jacket ganin haka yasa na ja na tsaya ina kallonsa har ya karaso kusa da ni ya dora min jacket din saman hijab hular sanyin dake kansa hannunsa ya saka min a kai.
“Wuce mu tafi Malama”
“Ni ba zan shiga motar ba”
“Waya ce ki shiga?”