← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 127

Sashe 120

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kin tana ganin mace ta yi fushi da mijinta? Haba Yasmin ayi hakuri ma, mun shirya abun ne a boye ban yi tunanin abun zai zo mana da sauki har haka ba, Yasmin kin san ya so yake ba ki bukatar na fada miki komai ina jin da ace na rasa Zahra a karo na biyu ke ma da kin rasa ni, amman yanzu Alhamdulillah komai ya wuce”

“Sai a jarida na ni fa Abiey”

“Ban san an saka a jarida ba, ban kuma san waya saka ba bayan mun gama waya dake Mai Martaba ya kira ni yake fada min abun da yake faruwa kuma yace min yanzu haka ya saka a kawo masa wanda ya buga labarin daga nan gurinsa zan tafi, domin sun buga labarin ne da nufi bata suna, secondly sune wadanda suka wallafa wacan labarin na rushe gidan da aka yi, ban san inda suke samo labarin ba. Yanzu ni dai tuba nake a yafe min”

Ta dan saki fuska.

“Ina Zahra take?”

“Tana gidansu ko na kawo miki ita?”

“Aa na sani ni ko bata son gani na”

Ya wara ido.

“Saboda me?”

“Zata ce ina son mijinta mana”

“Kina son mijinki dai, babu zance ni mijin Zahra ne ko mijin Yasmin ni mijin mace biyu ne a yanzu da dai ace Zahra kawai nake aure to zan zama mijin Zahra ita kadai, amman Allah yayi min kyauta da kyawawan mata har biyu a lokaci daya”

Ta yi murmushin jindadi ta sauke kai kasa domin bata yi zaton jin haka daga gareshi ba. Ya maida hankalinsa gurin abincin ya fara ci.

“Uhhhh waya girka wannan?”

“Ni ce”

“Aa ban yarda Momy ce”

“Wallahi ni ce”

“Daman haka kika iya girki? I thought Islamiya bata barinki girki ai, i got lucky daman ina son macen da ta iya girki kuma ta iya tsabta”

Haka yayi ta zuba santi wani abun da gangan yake yinsa saboda ya saka ta nishadi kuma yayi nasarar yin haka domin ya tafi ya barta zuciyarta fes sai dariya take. Daga gurin Yasmin Abiey ya wuce gurin Mai Martaba kai tsaye bangarensa ya nufa babu tsayawa neman iso a gurin Anty duk kuwa da ya san yau din ba girkinta ba ne girkin Hajiya Kilishi ne. Yana shiga da sallama Mai Martaba ya amsa masa yana murmushi da jindadin ganinsa.

“Babana”

Hajiya Kilishi ta sake waigawa ta kalli Abiey da kyau domin tabbatarwa idan shi din ne ko waninsa, Abiey ya karasa gaban Mai Martaba ya kwashi gaisuwa sannan ya zauna Mai Martaba ya mika masa mug din tea dake hannunsa, sun tattauna abubuwa kadan a ciki har da abun da Mai Martaba yake son yayi handled, sai da Hajiya Kilishi ta fita sannan Abiey ya tambayi Mai Martaba.

“An gano maka shi?”

“Eh an gano shi, ai ba boyayyen mutum ba ne, kuma ba shi kadai na saka a kama ba har da wadanda suka buga wacan labarin, dole akwai hannun wani a ciki ko dai daga cikin gidan nan ko kuma daga bangaren abokanka ko kuma bangaren ita yarinyar”

“Ni ma na yi wannan tunanin, domin wacan karon ma ba ni na saka a rushe gidan ba amman aka rusa saboda a bata min suna kuma a ja min zagi”

“Za mu gane ko waye tsakanin yau da gobe, masara idan ta ji wuta ita ke daďo”

Daga haka Mai Martaba ya rufe babin maganar ya dauko zancen nadin sarautar da za ayi masa cikin satin nan.

“Mamanka ta kawo shawara wai tana ganin kamar ka tare kamin lokacin zai fi armashi a kafin nadin sarautar, tun da bayan nadin sarautar da wata daya za a daura aurenka da Yasmin, ina ganin mu dai daga bangarenmu babu wata matsala idan ka shirya”

Abiey ya sauke kansa kasa sosai ya jidadin shawarar da Anty Amarya ta kawo daman ta yi masa wannan maganar tun shekaranjiya.

“Eh to Mai Martaba idan haka yayi muku ni ma ta gurina babu matsala sai dai na tuntubi bangaren ita Zahra na ji”

“Allah ya bada iko, idan kana da matsala da ni ka tunkare ni kai tsaye ka fada min ba sai ka laba da wasu ba”

“Ameen, na gode Allah ya kara lafiya”

Bangaren Anty Amarya ya shiga ya labarta mata yadda suka yi da Mai Martaba, Anty ta numfasa cikin farinciki ta ce.

“Ni gani nake kamar Lami ta shirya wannan abun, domin wacan karon na kasan a gaban yarta aka yi ina tunanin ita ta bata labarin sai ta saka aka shirya wannan saboda ta kara bata tsakaninka da Mai Martaba sai gashi Allah be cika mata wannan nufin ba, a yanzun ma ta yi haka ne saboda ta ga Mai Martaba be dauki wani mataki a kanka a madadi hakan na sai Allah ya shirya tsakaninku”

“Ko ma dai wanene za mu ji Inshallah asirinsu zai tonu”

“Da yardar Allah kuwa, Mai Martaba yayi maka maganar tarewa?”

Abiey ya shafa kansa.

“Yayi min yace kin masa magana”

“Haka na ga ya dace, ace an nada maka sarautar matarka tana gidanka abun zai fi bada kala”

“Sai dai ban san ko ita Zahra zata yarda ba”

“Ban gane zata yarda ba? Kai ne fa mijin karka zama mijin tace mana kai da zaka bata umarni ta bi”

Abiey yayi dariya.

“Ai ni tun kan tace ne ma, Zahra haba Anty kamin tace ma na aikata”

Haka suka yi ta hira cikin nishadi har suna tunawa da baya Anty tana tsokanarsa. Sai azahar ya fita gidan ya bayan ya sake wanka ya feshe jikinsa da turare wai kar ya jewa amaryarsa yana karni kamar wanda be yi wanka safe ba. Baya ra'ayi shiga gidan a domin haka ya faka a wajen gidan ya kira wayarta ya sanar mata zuwanshi, ta kusan bata rabin awa tana shiryawa sannan ta fito tana taku kamar wata matar sarki, tun kamin ta karaso ya fito ya bude motar ta shiga ta zauna sannan ya zagaya ya zauna kai tsaye ya kai hannunsa ya riko nata sumbata ta biyo baya.

“How are you”

“Fine”

Ta amsa cikin yanayi na damuwa, yana ganin hakan ya san ba lafiya ba, matsawa yayi ya hade bakinsa da nata wani hot kiss ya sakar mata, kasancewar doguwar riga ce sai mayafi a jikinta hakan ya bashi access ya saka hannayensa yana lalabe iya inda ya dade yana sha'awar tabawa a jikinta, tun yana yi saman abayarta har ya kasa hakura ya zira hannunsa ta saman rigarta, sai da ta ga yana kokarin dago ta ta dawo saman jikinsa sannan ta yi saurin cire bakinta ya zare masa hannayensa, ta yi saurin maida fuskarta gefe shi kuma ya kwanta jikin kujerar yana wani tandar baki mean he need more domin be taba jin kansa a irin wannan yanayin da ya samu kansa a yanzu ba har wani ajiyar zuciya yake saukewa yana lumshe ido.

“Fada min waya taba min yar autar mata”

Ya fada murya kamar mai rada, ya dago ya mika hannunsa ya juyo da fuskarta.

“Hiayatee what happen?”

“Amir...”

“Miya same shi?”

“Ba komai, kawai dai ina jin kewarsa ne”

Tashi yayi zaune da kyau ta yadda zai fuskance ta da kyau, ya matso da ita ya kwanto da ita jikinsa.

“Hiayatee idan kin san zaki cutu ki karbo yaron mana, daman ni na san zai tsaya miki a zuciya kuma ina tsoron kar hakan ya haifa mana da matsala a gaba, kin ga ki daina tunanin abun da iyayen Deen za su yi na sha fada miki indai ina raye babu wanda ya isa ya taba ki”

“Bayan na riga da na kyauta da shi, har ya samo masa Nanny fa kuma tun shekaranjiya har yau ba su kawo shi ya sha nono na ba, ina tunanin madara suka bashi, kuma jiya ya kira Mama ya fada mata cewar yau za a kai ta, ta duba wani gida idan ya mata sai mu tare a can, ni daman ba saboda kaina kawai na yi ba saboda Mr Bashir din domin shi ma ya ce baya son duniya ta ji abun da matarsa ta yi masa”

“Abun da mataraa ta yi masa be shafe ki ba, matarsa ce rayuwarsa ce ke babu ruwanki a ciki, ke dai yaro suka siya kuma kin sai da yanzu kuma ta gaskiya ta fito an dawo miki da abunki, Zahra kakanin yaron nan ma fa suna da hakki da shi, idan ba ki son ya zauna a gurinsu ne zan dawo da shi gurinmu ya zauna ayi masa duk abun da yake bukata”

“Amman shi Mr Bashir ai zai ce ban kyauta ba, kuma duniya zata ji”

“Zan masa bayani, kowa ma zan masa bayanin da zai fahimta”

“Aa ni dai yaron ma ai baya so na kuka yake min idan na dauke shi”

‘Ai kara haka so that mu zamu rayuwa cikin farinciki da aminci’

Ya fada a ransa daman bayan Mr Bashir Abiey ya fi kowa farinciki da hukunci da Zahra ta yanke not because of baya son Amir din but because of yana dan Deen kuma yana tunanin kamar idan Amir ya fito a matsayin ďan Zahra kai tsaye zai iya haifar musu da matsala a zamantakewarsu, idan har yace yana son Amir yayi karya, sai dai baya tsanarsa kuma zai iya yi masa komai saboda ďan Zahra ne, ba na Deen shi kadai ba, and since da sanin mahaifiyarta ta yanke wannan shawarar ba zai iya hanata ko saka ta ba, da ace dai ita akaran kanta ta yi haka to da zai hanata, gudun kar hakan ya haifar mata da matsala a gaba.

“Yanzu Shikenan, tun da haka kika zaba amman ya zama karo na karshe da zan sake ganin hawayenki akan yaron nan”

Kamar jira take sai ta fashe masa da kuka.

“Ni ba wai bana son shi ba ne, ai ina son shi ai”

Uffan be sake ce mata ba, har ta yi kuka ta gama, sannan ya zaro tissue ya goge mata hanci ya share mata hawaye.

“Kukan ya isa haka, i promise you muna fara haihuwar yayanmu saki samu sukunin kewar Amir zata rage miki, who's know ko gobe ma mu samu yaya ko kuma yau ma”
Chapter 120 · 0% Book details