← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 127

Sashe 29

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannuna na dora akan filo ina da rutsar kuka, ina jin kamar wani ya zo ya bani hakuri ya fada min cewar abun da na yi daidai ne. Amman ko Mama da muke gida daya bata shigo dakin ba ta kyale na ci kuka har na kusa cinye kaina ina ta jin kamar na yanke hannun nawa da na mari Abiey da shi na jefar.
Can bayan sallah Magariba na fito waje na zauna na rumgume hannayena ina ta kallon tsakar gidanmu, har lokacin Mama bata ce da ni na yi daidai abun da na aikata ko akasin haka ba, ina jin yadda wayarta ke ta ringing bata daga ba kuma bata ce min na zo na karba ba, har sai da na gaji na tashi na nufi inda take zaune tana cin tuwon da bata min tayi ba na dauki wayar na duba sai na yi arba da ni number Dr Hamid.

“Dr ne yake kira”

Na fada mata kamin na amsa sai ta amsa min da kamar tana fushi.

“To ni yake kira ko ke?”

Na juya ya shiga dakinta sannan na amsa kiran, bayan mun gaisa ya fada min bukatarsa na cewar sai dai na koma gidan da aiki.

“Ba zai yiyu ba, ina danyen jego na tare a gidan wasu dole mutane za su yi zargi kawai idan kana bukatar nonon a rika kawo shi yana sha”

“Gaskiya Mahaifinsa ba zai yarda a fitar da shi ba”

“Ai ba dole sai kun yi yadda zai gane ba”

“Idan har kina gudun tonon asirinki ne, ai kawo shi a gurinki yana shan nono shi ne babban tonon asirin ma, idan har ba zaki yarda da zama a can gaba daya ba zaki iya zuwa kina ba shi nono kina dawowa a matsayin kina kula da shi, amman babu wanda zai san da hakan sai ni da ke”

Na yi shiru ina nazari, daman can babu wani dalili da zai saka ni yin yin haka sai dan na rika ganin ďana, kuma yana da gaskiya yawan kawo shi zai janyo min matsala.

“Na amince”

“Good, zan zo na dauke ki a yau kin ga dare ne ma babu wanda zai sani sai ki shayar da shi zuwa safe sai na dawo da ke ko kuma cikin daren ma idan kina so”

“Shikenan”

“Ki shirya kamin na zo”

“Toh”

Na amsa sannan na kashe wayar na fito waje ina labartawa Mama yadda muka yi amman ban yarda na fada mata cewar zan kwana a can ba domin na san ba zata aminta ba.

“To ai sai ki yi yadda kika ga dama saboda ke kike da iko da kanki, da ubanki na raye zaki yi abubuwan da kike yi ne yanzu? Ni ai saboda kin rai na ni ina mace ko?”

Na kalleta da mamakin furucinta.

“Mama sai da fa muka yi magana dake kamin na aminta zan rika shayar da shi”

“Toh Allah ya baki sa'a, kin san ke yanzu idan mutum ya hana ki yin abu makiyinki yake zama”

“Mama saboda na mari Abiey ne kike ta wannan fushin da ni? Shi baki ji abun da yake fada akan Deen ba”

Na fada cikin kuka daman bani da wahalar kuka ko da bana da gaskiya balle a inda na san ina da ita.

“To waya sani ko gaskiya yake fada, ai da karya da yanzu ya kama gabansa kamar yadda Maryam ta fada, ke kuma baki tsaya kin yi bincike ba kawai ki daga hannu ki mareshi ke ga matar Deen”

“Amman taya Deen zai hana aurenmu Mama? Taya? Yayarsa fa da kanta ta zo ta mana gwaji ta ce ni nake dauke da cuta mai karya garkuwa jiki saboda a fasa auren kuma akan karya, a gaban kowa mahaifiyarsa ta ce ba zai aureni ba, idan ya aureni sai ta tsine masa albarka, ba dan Deen ya aure ni a ranar ba wata kila da bakinciki be bar ni na kawo yau ba, Deen be duba ciwon da aka ce ina dauke da shi ba, be duba kowa ba be damu da komai ba ya amince ya aureni, idan har da gaske ne Deen shi ya shirya haka miyasa ba su fada ba tun a wacan lokacin sai yanxu? Kuma taya Deen zai shiryawa Anty Zainab haka ina ma zata gan shi, daman tun gabatowar auren na lura gaba daya sun canja min, amman duk baki gani ba Mama sai ni kike ganin laifi na”

“Ko miye yayi miki be cancanci ki dauki hannunki ki mareshi ba, ko ďanki sai abun da ya kai ya kawo ake duka balle babban mutum kamar wannan wanda a yau idan suka so mu bar garin nan Wallahi dole mu bar shi”

“Mama ko lokacin da Deen ba shi da lafiya Hajiya tace na je na nemi taimako a gurinsa kuma na je da ace ya taimaka min da yanzu ban rasa ďana ba, ko da kuwa ace Deen din ya rasu, amman be taimaka min ba, kuma a haka yake ikirarin yana so na”

“To wai idan ba sonki yake ba, yanzu me ya dawo da shi gurinki? Rai kike da shi da zaki ba shi? Ko kuma gafara zaki masa ki yaye masa zunubai”

“Amana ta ce ta kama shi, waya sani ma ko yayi aure matar ta yaudare kamar yadda yayi min shiyasa ya dawo neman gafarata”

Duk a cikin kuka nake maganar, sai dariyar Mama na ji ta tsude hannunta ta mike tsaye..

“Kuma sai yayi ma Deen shari? Akwai kamshin gaskiya a maganar shi kuma ba mu saurare shi ba balle mu ji, dan haka ni ba zan iya yanke hukunci ba”

“Ai saboda ba shi da rai zai iya fadar komai akansa”

“To Allah ya sauwake, indai har abun da yake fada gaskiya to ina ji miki tausayin ranar da zaki gane haka, domin lokaci ya kure miki a wannan lokacin”

Na share hawayena.

“Dr yace zai zo ya dauke ni”

“Allah ya kiyaye”

Na mike tsaye na shiga daki na canja tufafina na saka hijab, sannan na fito waje na zauna Dr Hamid be zo ba sai tara da rabi, ya kira Mama ta miko min wayar na karba ya sanar min yana waje, sai na aje mata wayar na fita jikina har rawa yake saboda na san zan je na ga ďana ne ban taba sanin haka uwa take ji idan ta rasa ďanta a kusa da ita ba sai a yanzu da na matsu na yi arba da fuskar ďana.
Nesa da gidanmu ya aje motarta saboda kaucewa idon mutane, ina isa na bude front seat na shiga da sauri na zauna shi kuma yaja motar kamar mun yi sata haka ya fita daga unguwar, sai da muka hau titi sannan ya kalleni yana murmushi.

“Ya gida”

“Lafiya Kalau”

Na amsa ba tare da na kalleshi ba.

“Dan za aje ganin baby har da kwalliya ake?”

Na dan dago na kalleshi kadan na maida kaina kasa, domin na san ban yi kwalliya ba bayan tufafin dana canja ko man shafi ban shafa ba balle na hoda, da ma dai cewa yayi ina da kyau wannan kam ba zan musa ba, bana bukatar ma a fada min haka ni kaina na san ina da kyau irin kyau na yi mai daukar hankali hakan yasa nake da farinjini ko a lokacin da ina budurwa har Deen ya kan ce duk masu so na saboda ina da kyau ne, da ace ni mummuna ce da ba za su so ni ba, na kuma gasgata hakan domin shi kadai ne ya aure ni ba tare da ya taba furta min kalmar so ba, kuma ba dan komai ba sai dan ya cire ni daga kunyar da Abiey ya zo jefani, to taya wai ba zan so Deen?

“Kin yi shiru Beauty”

Ya katse min tunanin da nake, wannan karon da mamaki na kalleshi domin na lura ya zo min da wasu bidi'o'in da ban san da su ba, domin babu wasa a tsakaninmu kuma be taba nuna min fuskar hakan ba.

“Gidan yana da nisa?”

Na tambaya domin na fara jin takura a zaman da na yi a motar ba dan babu enough space ba sai dan kallona da yake ta yi.

“Ko da tafiyar a kusa ne, ai tsawaita ta zan yi saboda na yi ta kallon kyakkyawar fuskar nan taki mai daukar hankali, tsakani da Allah kin yi kyau ba wasa nake miki ba”

“Na gode, amman zan fi ganin mutuncinka idan baka sake furta min kalamai irin wadannan ba”

Murmushi yayi mai sauti, sannan ya hanna horn a gaban wani katon gate, wasu mazaje majiya karfi suka leko sannan suka bude gate din. Da ace a bachi na farka na samu kaina a cikin gidan nan da babu abun da zai hana sake komawa domin zan yi zaton mafarki nake. Dare ne amman ba zaka iya gane hakan ba saboda fitilu da suka haske ko'ina na gidan sai idan ka daga kanka sama zaka ga hudu da tausarari, kowane bangare na furannin gidan fulfular da ruwa yake kamar wata kasar da ba nigeria ba. Harabar gidan ma ba interlock ba ne wani abu ne mai kama da tiles kuma kamar an zuba ruwa a kasa.
Lallai hausawa sun yi gaskiya suka ce masu layya na cin nama, wani wan wani, baba da babansa, yau na ga arzikin ko kuma na ce gyaran gidan da ya ci ubansu na Abiey. Anya mutanen cikin gidan nan sun yarda da mutuwa kuwa? Na tambayi kaina ina kallon windows din da suke sama na wani farin karfi mai kama da silver. Kofar da Dr ya dosa da ni ma kadai abar kallo ce ta cika idona ta ko'ina. Door bell ya fara dannawa babu jimawa aka bude mana kofar sai kamshi yayi mana lale marhabun ina kokarin cire talkamina sai Dr yace.

“Shigo da su, akwai gurin da ake aje talkami ai”
Chapter 29 · 0% Book details