← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 127

Sashe 28

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Na san me na ke yi Anty, kuma ke ma kin san babu irin wulakancin da Abiey be yi min ba”

Na juya gurin Abiey

“And lemme warn you karka sake fadin wata mummunar kalma akan Mijina, Deen ya gama lafiya ya rabu da kowa lafiya, karka sake samun yar'uwarta da wani zancen banza akan mijina, macuci mayaudari kawai azzalumi so kake ka bata kanka Deen a gurin mutane? To Allah ya fika kuma Deen yayi maka nisa Abiey kuma ka karasa kanka tsana a zuciyata ka yafawa kanka bakin fentin da ba zai taba goguwa ba”

Ima kai aya Mama ta daka min tsawa.

“Aa... Zahra kanki ďaya kuwa?”

Ya dago ya kalleni ya fara min magana kamar da rarrashi.

“Barta ta fadi abun da take ra'ayi Mama, saboda Deen ya dorata a gadar da ba zata iya fahimtar komai ba, amman ki yi tunani Zahra a Wallahi tallahi ban guje ki haka nan kawai dam na yaudareki ba Deen ne ya shirya komai...”

Ban san lokacin da na yunkura daga inda nake zaune har tafin hannuna ya kai a fuskarshi ba.

“Allah ya waddaranka Abiey, ka zo da sunan gaisuwa kuma ka zauna a cikin gidanmu kana aibanta mijina...”

Ji na yi an taba ni ina juyowa kanwarshi da suke uba daya Aisha ta dauke ni da mari.

“Kazama dake har kin isa ki daga hannu ki mari Babban mutun kamar ďan'uwana, kin san yadda yake fama saboda ke amman yau ki siffanta shi da wasu munanan kalmomi kuma ki daga hannu ki mare shi? Waye ubanki duk garin nan? Kiyayya ba hauka ba bace Zahra ďan'uwana baya neman komai a gurinki ba ki da abun da zai saka ya yaudareki, macucin mijinki ne ya shirya komai ke kuma da yake wawuyace kin kasa fahimta, Anty tashi mu tafi”

Ta mike tsaye ni kuma na bita da kallo baki sake hawaye na sauko min na zafin kalaman da ta jefeni da su.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Anty ta fada Mama kam zaunenta take tana kallon ikon Allah, kuma na san ba zata rasa dora min laifi ba wata kila shi ya saka bata ce komai ba. Abiey ya mike tsaye idonsa har sun kada sun yi ja kamar ba na shi ba cikin wata irin muryar da ban taba sanin yana da ita ba ya fisgo Aisha ya dawo da ita baya.

“Duka ki bata hakuri Aisha”

“Amman....”

Kasa karasawa ta yi sakamakon wani mugun kallo da ya watsa mata.

“I'm sorry”

Ta furta.

“Kneel down”

Ya fada tsabar bacin rai jikinsa har rawa yake, sai da ta aje numfashi da karfi sannan ta durkusa kasa guiyoyinta tana watsa min harara ta ce

“Sorry”

Tsakamin mikewarta tsaye da wanke mata fuska da yayi da mari biyu ma su kyau ban san wanda ya riga wani ba.

“How dare you raise your hand on her face? How dare you Aisha...”

D muryar dake nuna tsananin bacin ransa ya furta hakan yana kallon Aisha dake dafe da gefen fuskarta tana kuka domin a gefe daya ya sauke mata marin har biyu. Sannan ya kalli ya Mama ya ce

“Mama ayi hakuri dan Allah”

Ya juya ya fice Aisha ta bi bayansa tana kuka.

“An yi na farko an yi na karshe Zahra da yardar Allah indai akan Abiey ne”

Shi ne abun da Anty ta fada min sannan ta mike tsaye ta fice daga gidan Narjis na take mata baya, ni kuma kalli Mama ina kuka.

“A gaishe ki dai Juliet, matar Deen ma'asumin da ba shi laifi, ke ke ke Zahra ba wata ba sai Ciwon son Deen ya kashe ki, mahaukaciyar banza marar tunani ai ni Wallahi wannan bata burge ni da bata miki mugun duka na fitar hankali ba”

Runtse ido na yi jin kalaman dake fita daga bakin Mama, sai kuka yace min ta ho mu hade, tashi na yi da sauri na shige daki na kwanta saman katifa rike da hannun da na mari Abiey, marinsa da na yi a yau ya fi komai yi min zafi har ga Allah ban jidadin aikata abun da ban taba zaton ko a mafarki zan aikatawa Abiey shi ba, duk kuwa na san da cewa ya cancanci haka.
[10/16, 5:39 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣7️⃣

Sauban dake driver side ya bude motar ya fito hango Aisha da yayi ta fito tana kuka kamar karamar yarinya, kamin ya kalli Abiey dake gabanta fuskarsa babu annuri.

“Miya faru?”

Abiey ya jingina da motar yana sauke ajiyar zuciya ba tare da ya amsa masa ba, cikin kuka Aisha ta ce

“Marina yayi”

Sauban ya kalli Abiey da sauri.

“Marinta ka yi?”

Abiey be ce komai ba ya zagaya dayan side din ya shigo, Aisha ta bude back seat ta shiga Sauban na kokarin komawa cikin motar ya zauna sai ga Anty ta fito tare da Narjis, wannan karon be ce uffan ba har sai da suka shiga motar shi kuma ya fara driving.

“Abiey indai na isa da kai... In dai zan fada maka magana ka ji to daga yau kar na sake jin sunan yarinyar a bakinka, kuma karka sake takurawa kanka da tunaninta”

Abiey ya juyo ya kalli Anty dake maganar.

“Amman Anty ba zaki ga laifin Aisha ba? Ita ta fara marinta fa? Akan me zata daga hannu ta mari Zahra tsakani fa da Allah”

“Lallai so hana ganin laifi, yanzu duk darajarka da kimarka da yarinyar ta keta ta daga hannu a gaban kanenka kuma a gabana ta mareka baka ga laifinta ba? Abiey ka girmi yarinyar a shekaru a matsayin ba dan kaddara ta so ba da babu abun da zai saka ka kalleta ma, amman a haka ta daga hannu ta mareka, ta kiraka da kalmomi marar dadi a gaban idona agaban kanenaka saboda abun da bata san gaskiyarsa ba? Ai ko karya kake yi ba zaka zauna a gaban mahaifiyarta ka zagi Deen ba”

“Anty dan Allah maganar nan zata iya tsayawa a tsakaminmu?”

“Ba zata tsaya ba”

“Anty kin fi kowa sanin Ammy bata da hakuri”

“Dole sai ta ji abun da ya faru, kuma ni da ace zaka ji magana ta Wallahi da ka yafe yarinyar domin ta fice min a rai, kuma baikonka da Yasmin ba za a fasa ba”

Uffan Abiey be sake cewa ba, balle kuma Sauban da tun da aka fara maganar ba saka bakinsa ba, Anty kuma bata fasa fada ba tana ta munana masa Zahra, har suka isa masarautar Sauban ya faka daidai entrance din shiga part din Anty, Narjis ta bude ta fita tare da Aisha da fuskarta ta kumbura saboda marin da Abiey yayi mata da kuma kukan da ta sha. Sai da suka shige ciki sannan Abiey ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ta runtse ido, Sauban na ganin haka yayi reverse ya bar gidan yana tukin a hankali.

“Abiey I'm your friend, dole ne na fada maka gaskiya ko da zata maka daci”

Abiey yayi saurin bude idonsa ya kalli Sauban.

“Karka fadi wata magana da zata bata min rai a kan Zahra, ina son yarinyar Sauban ko da zata saka wuka ta yanyanka ni, ina sonta kuma ina son na tabbatar mata da haka”

“Amman ka daina zuwa da yan'uwanka a gurinta”

“Zan kiyaye, sauke ni gurin Ammy”

Sauban ya kalleshi cike da tausayi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Babu wanda ya sake magana a cikinsu har aka suka isa gidan Ammy, Abiey ya bude motar ya fita, a hankali yake takawa har ya isa bakin kofar falon hannunsa ya kai ya tura kofar ya shiga. At first yayi tunanin zai same ta a falo, domin tana jiransa a duk lokacin zata yi masa fada ko kuma wata magana. Sai dai be samu kowa a falon ba cikin har da Jummai mai aikin Ammy, kai tsaye ya nufi upstairs yayi knocking kofar ďakin sannan ya tura ya shiga, Ammy da plate din zogale ki kan cinyarta ta dago ta kalleshi, sai ya tsaya jikin kofar kamar mai jin tsoron karasowa.

“Anty ta kira ki?”

Ta tambaya yana ala ala tace masa aa sai ya fara tarar abun tun kamin Anty ta shimfida mata komai.

“Eh yanzu muka gama waya, kuma ta fada duk abun da Zahra ta yi daman ďan talaka be iya samun guri ba, saboda ka kai kanka ka nuna kana son ta shi zai saka ta daga hannu ta mareka? Waye ubanta duk garin nan....”

Da fari cikin lalama Ammy ta fara maganar kamar abun arziki sai kuma ta karasa a tsawace alamar ta fusata sosai. Abiey yayi saurin sakin kofar ya karaso kusa da ita ya zauna.

“Ammy karki zafafafa please”

“Kar na zafafa? Wata banza yar banza da bata wuce auren direban gidana ba ta daga hannu ta mareka? Saboda ta samu dama ka furta kana sonta?”

“Ammy tana cikin bacin rai ne bata gama fahimta ba”

“Bata gama fahimta ba? Mi zata fahimta? Kana sonta? Idan baka somta zaka koma gurinta ne? Ka kwana ka tashi da son yarinyar nan kamar ibada yanzu kana zuwa yi mata gaisuwa ta mare ka kuma ta kira da azzalumi macuci ai ko dan sanin Zuwaira matar Mai Martaba ce ya kamata ta daga maka kafa ta ji kunyar wulakanta ka, balle kuma har ta san da cewa kai ma ďan Sarkin ne, ta manta yadda take zuwa ta hau saman gadona ta kwanta? Yau zata daga hannu ta mari ďana? Alhamdulillah da baka aureta ba, kuma ko ita kadai ta rage ya mace ka hakura da ita kenan”

A razane ya mike tsaye.

“Ammy? No no no no no no! No please na san ranki daman zai bace amman bana son ki sake cewa komai zamu yi magana daga baya”

Be jira abun da zata fada ba ya fice daga dakin da saurinsa, jikinaa har rawa yake numfashinsa na fita da karfi tsabar tashin hankali kansa har tsarawa yake.

ZAHRA POV.
Chapter 28 · 0% Book details