← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 127

Sashe 13

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban ga laifinta ba, domin ko nice a halin sa take ciki abun da zan aikata kenan.

“Na ma dauka haihuwa ce sai suka ce ba haihuwa ba ce wai matsala dai kika samu”

Na koma na kwanta na lumshe ido sai hawaye suka ce sallamu alaiki, idon da ban sake budewa ba kenan har safe, shi ma saboda na ji ana kokarin cire robar jinin dake hannuna ne.

“Sannu Madam”

Likitan ya fada yana sakar min murmushi sai na amsa masa da kai na tashi zaune.

“Likita za a iya sallamata a yau?”

“Aa gaskiya muna bukatar mu tabbatar da kin samu lafiya sosai”

“Ba ni da kowa a nan likita ina son na koma Kano gurin mahaifiyata a can ma za a iya kula da ni”

“Baki da wanda zai zo zaria yayi jinyarki?”

“A zaria nake?”

Na tambaya ina kallon Hafsat sai ta daga min kai.

“Eh ke da shi nan aka kawo ku saboda a baku taimakon gaggauwa, amman shi mutune na ji ance ya koma kano tun jiya saboda ba wani ji rauni sosai ba”

Na kalli likitan.

“Ka taimaka min da Allah, hankalin mahaifiyata zai tashi idan ba a kano nake ba”

“Toh indai haka ne sai dai mu miki transfer daga nan zuwa asibitin dake Kano”

“Eh na yarda hakan zai fi min sauki ma”

Da wannan ya yarda sai ya fita ya bar wata nurse tana balla magani ta bani, sai na karba na aje har sai da na karya da lafiyayyen abinci da aka kawo mana daga wata babbar hotel dake zaria sannan na sha maganin, ina gama sha likitan ya shigo tare da Nurse din dazun ya mika min takardar transfer.

“Gashi sannan maganinki idan aka miki allura ba zaki sha magani ba, kuma ki tabbatar kije aaibitin da muka turaki, sannan Alhaji Bashir yace idan kika farka a asanar masa, na fada masa kin farka har kin nemi transfer yace a miki kuma ya vada umarnin daukar nauyin duk wani ciwo na ki, saboda haka na kira likitan dake Aminu Kano na sanar da shi komai idan kin isa sai ki nemi Dr Hassan ki ba shi wannan file din wannan kuma number wayarshi ce”

Ya karasa yana miko min number da kuma file dina.

“Na gode Likita”

Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleni.

“Uhm yace ki dan jira za a kawo miki sako kamin ki tafi”

Na daga masa kai.

“Allah ya bada lafiya, ko da yake dai mun yi solving din komai sai dai dan a kara tabbatarwa”

Wannan karon Hafsat ce ta yi masa godiya, ya fice tare da nurse din yana murmushi, kana ganinsa kasan irin likitocin nan ne masu saukin kai. Yana fucewa na kalli Hafsat na ce.

“Ina jakata?”

“Gata nan na aje miki karkashin gado, daman na zo da ita ne da tunanin ko za a kashe kudin magani sai gashi mutumen ya dauki nauyin komai ba a taba kudinki ba”

“Dan Allah ki raka ni na hau mota kin ji”

“Kin ji fa abun da likitan ya fada yace mutumen yace ki jira za a kawo miki sako, kuma ba ki sani ba ko su Mama suna hanya”

“Mama ba zata zo nan”

“Saboda me?”

“Na san wacece mahaifiyata Hafsat, ba zata zo nan ba, muje ki raka ni na hau mota”

Na share hawayena na tashi tsaye tare da gyara daurin zanen dake jikina.

“Tufafinki fa suna gida na bada a wanke saboda zanen duk ya lalace da jini, amman ga hijab dina nan na kawo miki”

“Na gode”

Na furta ina jin wani abu kamar kwallo yana min yawo a zuciya, duk yadda Hafsat ta so na tsaya dan karban sakon da likitan yace za a kawo ban tsaya ba, saboda zuciyata ba a can take ba, kuma ban san wane kalar sakon ba ne. Ina takawa a hankali har muka fito cikin asbitin tun daga yanayi da tsarin aaibitin ya isa ya sanar maka cewar asibitin ta kudi ce irin wannan mai zaman kanta, domin an tsara asibitin da kyau kai kace ma a garin Abuja kake ba Zaria ba, muna fitowa Hafsat ta tare min mai Napep ta saka yan komatsan data kwaso na tabarma da sauran abincin da muka rage da kuma yan kayanta, sannan na shiga ita ma ta shiga ta fadawa mai Napep din inda zai kaimu, yana fara tafiya na bude jakata na kirga 5k a cikin kudina na mika mata.

“Ga wannan ki bawa Inna”

Na sake kirga 5k na mika mata.

“Wannan kuma na ki”

“Haba Uwani ni ban baki ba kuma zan karba?”

“Da bani da su ai ba zan baki ba”

“Na gode Allah ya saka da alheri, kuma dan Allah ki yi hakuri da kiran Mama da na yi na rikice ne shiyasa”

“Ba ki yi laifi ba ni ma abun da zan aikata kenan idan kika samu kanki a cikin wannan halin na gode da kulawa kuma ki min godiya a gurin Inna”

“Me muka miki na godiya, ai kin fi haka idan ma mun yi”

Muna isa tashar na fita, sai ita ma ta fito.

“Ki koma Hafsa ai zan iya shiga mota da kaina na gode”

Bata ce komai ba sai ta rumgume ni ta fashe da kuka.

“Allah ya yaye miki damuwarki kawata ya miki mafita”

“Ameen”

Na furta ni ma cikin kuka sannan na sake ta.

“Sai wata rana Hafsat idan muna da rabon ganawa”

“Nan da kwana biyu zan zo Kano na dubaki da yardar Allah, Allah ya kaiki lafiya”

Na ciro kudin mai napep na mika masa sannan na nufi gurin da aka faka motar Kano. Mun kusa awa daya a gurin sannan motarmu ta daga zuwa Kano, muka isa cikin lokaci ina fita motar sai gabana ya soma faduwa, sai na fito bakin tashar motar sannan na tari napep na hau na fada masa inda zai kai ni, kamin mu isa ina ta saka yadda zan fara yi ma Mama bayani amman na rasa mafita, domin har yanzu ban san me zan rika na yi amfani da shi a matsayin dalilina na guduwa ba, haka dai na fito Napep din ina jin kamar ace zan gudun ba, domin abun zai zame min matsala ne a yanzu, dari biyu na bashi sannan na juya ina tafiya kamar wanda bata son takawa na nufi kofar gidanmu, na kusan minti hudu a tsaye sannan na aga kafata na shiga cikin gidan cike da nauyin baki, ban san ta inda zan fara sallama ba.
Kamar rai ya ga mutuwa haka na ji lokacin da na yi arba da Mama a zaune tana gyaran wake, sai ta dago ta kalli kofar domin ganin wanda ya shigo muna yin ido hudu sai annurin fuskarta ya canja ya maida kanta gurin gyaran wanken da take ta cigaba ba tare da ta ce da ni komai ba. Ni kuwa na yi tsaye a gurin kamar an dasani na san halin Mama idan ta yi fushi bata da kyau ba kasafai take saukowa da wuri ba. Na cira kafata na fara takawa sai ta dakatar da ni.

“Tsaya nan karki karaso nan, me zaki zo ki min?”

“Ki yi hakuri Mama dan Allah”

Na furta hawaye na sauko min muryata kamar mai koyon magana.

“Kin san da hakuri kika tsallake kika bar dakinki zuwa wata uwa duniya? A tunaninki idan kin gudu mutuwa zan yi? Na rasa uwa ban mutu ba, na rasa uba ban mutu ba, na rasa mahaifinku tun kuna kanana na rayu da ku babu taimakon kowa sai Allah kuma ban mutu ba, sai dan kin gudu ke kaidai zai saka na fadi na mutu? To na yafe ki kije duk uwa duniyar da zaki je, abun magana ne daman kin ja ma kanki kina takaba kin gudu an rasa inda kika yi”

Na saki jakar hannuna ban damu da cikina ba na durkusa kasa na hade hannayena ina kuka.

“Mama dan Allah ki yafe min ban yi haka dan na bata miki rai ba, Mama baki san abun da ya saka na gudu ba...”

“Na sani, Maryam ta fada min komai tashi ki fita...”

Ta amsa min tana mikewa tsaye ta nuna min kofa.

“Mama dan Allah....”

“Ki fita na ce karki bari na maimaita kalmar nan a karo na uku Zahra...!”

Na tashi tsaye da sauri domin har yanzu ban daina tsoron dukan da Mama take min lokacin da ina budurwa ba idan ta fara bata min da sauki sai an kawo min agaji.

“Ki tafi duk inda zuciyarki ta raya miki ki gani ni mutuwa zan yi”

Na dauki jakata ina hawaye na fice daga gidan ina tafiya kamar zan fadi haka na nufi titi, wata zuciyar na raya min na tafi gurin Yaya Maryam ko Hajiya, sai dai me? Za su karbe ni ko kuma kyarata za su yi kamar Mama? Kara ma Yaya Maryam amman Hajiya da wane idon ma zan kalleta? Na yi tafiya mai nisa a fada ina tafe ina hawaye da nadamar abun da na aikata tun da fari, sannan na samu gindin wata bishiya na zauna na huta sannan na matsa kusa da wani mai shago na siye ruwa na sha na nufi titi na tari adaidata sahu na hau na fada masa unguwar da zai kai ni. Har kofar gidana ya sauke ni na bashi kudi ina ta jin kunya kar na gada ido da mutanen unguwar domin ban san ta ina zan fara amsa tambayoyinsu ba, bayan na sallame shi na karasa na taba kofar gidan sai na jita a rufe, ji na yi kamar na fadi a gurin saboda damuwa da ta taru ta tsaya min akai, sai dai babu dama saboda unguwarmu ne kuma mutanen unguwar za su sani za su fito su tambaye ni me yake faruwa. Haka na juya na koma titin na tari wani Mai Daidaita na hau ya mayar da ni gidan Mama, shi ma na sallame ni na nufi kofar gidan da tunani da kuma addu'ar Mama zata hakura ta yafe min ta karbe ni.

“Au dawowa kika yi?”

Shi ne abun da ya fara fitowa daga bakinta a lokacin da ta yi arba da ni.
Chapter 13 · 0% Book details