Sashe 83
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“To ina ruwanshi da ita wai? Haka fa yake dukanta idan ya ganta da wani bana son wannan halin na shi Wallahi, Zahra bata isa ta tsaya da saurayi ba ne? Ko kuma baiwar gidamsu ce ita, kuma idan ma haka ne shi ma ai sai a hana shi tsayuwa da ita”
Na karbe ina kara karfafa abun.
“Kuma Wallahi Mama Bahijja tana hira da samari har sallama ake mata, amman ni sai ya riga min fada yana dukana saboda baya kaunata be son cigabana, hassada yake min so yake kanwarshi ta yi aure ta bar ni a nan”
Dariya Mama ta yi, Yaya Maryam tace.
“Mama Gaskiya ki yi mishi magana ko kuma ki saka Baba yayi mashi magana tsakani da Allah be dace yana saka mata hannu yana dukanta ba ba fa yarshi ba ce”
Na yamutsa fuska
“Har da wani cewa ba zan je biki ba”
“Aifa ba zaki je ba saboda yace ba zaki ba, ba zan barki ki tafi ba sai ace na goyi bayanki ai, daman can ba son zuwanki nake bikin nan ba”
Na tashi kamar buzuzu na shige daki ina fatali da uniform din makarantar.
“Wallahi sai na je”
Na fadawa kaina ina jaddada zuwan nawa, musamman da na ji Yaya Maryam a zancen yau ake dinner. Ima fita gidan da sunan zuwa islamiya gidan Ammy na wuce, wannan karon ban tsaya kula wasa da Mai gadin yake min ba, na karasa harabar gidan da Ammy take zaune tare da Anty Zainab da Aliyu fuska kamar ace min kyas na fashe da kuka.
“To Autar Ammy yau da me aka zo?”
Anty Zainab ta fada tana tsokana, daman can ta saba tsokanata tun ba yau sake da ita ba har na saba, saboda girmamawa an zauna a kasa gurin kafafuwan Ammy ina ta tabe baki.
“Ammy barka da yamma”
“Barka dai Autata kwana biyu na daina ganinki miya faru?”
“Ai ranar da kika ba Aliyu kudi ya ba ni, ina nunawa a gida shi kenan sai Ya Deen ya mare ni ya saka Mama ta dake ni kuma aka ce ba zan je bikin ba”
Aliyun da tun da na shigo idonshi yake kan wayarshi ya dago ya kalleni.
“Saboda me?”
Anty Zainab ta tambaya.
“Wai miyasa zan karba kudi hannum wanda ban sani ba, kalli idona har yanzu akwai jini a ciki”
Na kwale mata ido ina nuna mata gurin da tabon jini ya kwanta a ciki.
“Waye wannan Deen din Yayanki?”
Aliyu ya tambaya, sai na girgiza mashi kai.
“Aa komai ba mu hada ba fa, agola mu ne”
Ya kalli Mahaifiyarsa.
“Ammy miye agola?”
“Step brother”
“Just”
Ya tashi zaune da kyau yana mamaki.
“Ya saka mata hannu ya dake ta? Ji yadda jini ya kwanta a idonta fa? I swear da a waje wannan sai an kai shi Kotu, katon banza da shi ba zai doke maza ba sai ya samu karamar yarinya ya saka mata hannu, gaskiya ya kamata ki yi magana da iyayenta wannan ya tsaba doka ai”
Daga Ammy har yayarshi da nake kira da Anty Zainab dariyarshi suke.
“Abiey nan fa ba kasar waje ba ne, mu a nan musulmai ne kuma musulman ma a arewa, iyayenta da duk wanda ke da iko da ita zai iya hukuntata idan ta yi ba daidai ba”
“Amman wannan ko a musulunci be dace ba, ta ina aka yarda namiji ya saka hannu ya doke mace, ke kina ganin jikin wannan kin san ba irin wanda ake duka ba ne idan suka mata wani dukan ai za su iya karyata ma, i can talk to her parents”
Ammy ta mike tsaye tana fadin.
“Babu ruwanka Aliyu sai ka je gidansu mutane ka ce cewa iyayenta kai ne wa? Ni din dai ya kamata na shirya na shiga na gaisa da iyayenta su san ni na sansu, amman kai ina dalili”
“Hakkin makotaka mana ai tana da hakki, matsalar Africa kenan ba ku sam hakkin dan'adam ba sam idan ba haka ba taya step brother zai dake yarinya a saka mashi ido”
A bakin gaskiyarsa yake magana domin alamun shi sun nuna haka, Ammy dariya kawai ta yi ta shiga cikin gidan ta bar mu wajen.
“Kin dinka ankon?”
Aliyun ya tambaya sai na girgaza mashi kai.
“Kina so?”
“Eh amman yau ake dinner ba zai yiyu na saka ba”
Ya kalli Anty Zainab.
“Wane tela kika san zai iya dinka mana kaya yanzun nan”
Anty Zainab ta rausayar da kai.
“Kana ji fa ance ba zata je bikin na ba”
“Ba Mamanta ga hana ba fa, shi ya hana ta imagine”
“Idan ka janyo mata wani dukan fa?”
“Zaki min ko na kira Sauban?”
“Babu ruwana a ciki”
Ta mike tsaye ni da shi muka bita da kallo har ta shige, sannan muka dawo kallon junanmu kusan a tare muka sakarwa juna murmushi na sauke kaina masa ina jin nauyinshi shi kuma ya maida idonsa gurin wayarshi can kuma ya kara wayar a kunne ya kira macen da na ke kyautata zaton budurwashi ce.
“Safeena kina kusa?”
Ban san me wanda aka kira da Safeenar tace ba na ji ya amsa da.
“Da yauwa lace zan siyo mai kyau please ina son ki bada a dinka min shi yanzu nan karki damu da ko nawa za'ayi”
“Okay”
Ya sake amsawa kana ya mike tsaye ya nuna min mota, da sauri na tashi na nufi motar, shi kuma ya shiga cikin gidan be dade ba ya fito rike da keys kamin ya karaso har na gama kallon fuska a jikin madubin motar, front seat ya bude min na shiga motar ta alfarmar na zauna shiga kuma na zagaya mazaunin direba yayi ma motar key, wani kalar rawa nake takawa a cikin zuciyata na dade ina addu'ar shiga kahirar mota amman bata karbu ba sai yanzu, ga sanyin ac ga motar tayi sama sauran motocin sai hangosu nake kamar kananan motoci tsabar dadin zama da sanin drajar naira baka jin motsin tafiya sai dai ka ga mutane ta cikin gilashi da kuma camerar dake cikin motar. Shopping mall ya faka ya bude ya fita ni kuwa na hakimce a cikin motar har sai da ya bude min sannan na fito na bar jakar makarantar a cikin motar muka jera muka shiga ciki, line masu lace muka tsaya ya bani damar zabe mi kuwa sai da na duba na dubo na ga dan ubansu sannan na dauko, ya shiga da ni gurin masu mayafai na dauko wanda zai shiga da lace din, talkami ma zabowa na yi sannan muka nufi gurin biya kudi. ATM dinshi ya mika ina gafe tsaye dadi kamar ya kasheni tsabar murna bakina baya rufuwa.
“Yarinyar can kallona kawai take ko ta san ki ne?”
Bakinshi kusa da kunnena yake fadin haka, na kalli saitin gun da yarinyar take tsaye, tabbas shi take kallo kallo kuma bana wasa ba.
“Aa ni ban taba zuwa nan ba, bata san ni ba sai dai ko idan tana sonka ne”
Na fada kaina tsaye domin haka zuciyata ta raya min kamar yadda idanuwana suka gani, murmushi yayi ya mike tsaye straight ya saka hannayenshi aljihu.
“Je ki min magana da ita”
Na daga kai na kalleshi sai na ga shi ma ita yake kallo, tafiya na fara sai da ma yi rabi sai kuma na dawo da gudu ina tambayarshi.
“Ya sunanka Abiey ko Aliyu? Na ji Anty Zainab tace Abiey Ammy tace Aliyu”
“Ammy ce kawai take kirana da Aliyu amman kowa Abiey yake ce min”
Na juya na koma ina ta tsara yadda zan yi magana da budurwar har na isa.
“Sannu sis”
“Yauwa sannu”
“Wacan Yayana ne sunanshi Abiey yace na karbo masa number ki”
“Ni da gaske Abiey ne? Wallahi I'm confused ashe shi din ne”
Ta fada tana daka tsalle sai ta bar ni tsaye a gurin ta tafi gurinshi ta gaisa da shi ta dauki hoto da shi, ina nan tsaye wasu mazan ma suka zo suka yi hoto da shi, ni kam kadan ya rage mamaki be kashe ni ba. Bayan mun shiga mota na kalleshi na ce.
“Miyasa mutane suka daukar hoto kai?”
Sai yaja zirin hancina
“Saboda ina tare da ke mana, ina yarinyar da na ce ki min magana da ita”
“Ba ta zo ba miyasa baka mata magana”
“Ban iya magana da mata ba, ban san yadda zanyi na yi hira da su ba irin na saurayi da budurwa”
“Da gaske?”
“Yes zaki koya min”
“Eh mana idan zaka je gurin budurwarka ka rika kirana zan fada maka me ake cewa”
“An gama”
Matar dazun ya sake kira ta kwakwanta mashi wani gurin muka dauki hanyar janbulo. Wani shagon dinki ne ko da muka isa mun tararda wata mace a gurin daga ita sai karamin mayafi tana ganin motar Abiey ya bar motarta ta nufo mu suka gaisa sannan ta karbi lace din ta ce na fito muka shiga ciki aka auna ni, sannan na dawo cikin motar na zauna ita kuma ta shiga gidan baya, ina jin suna ta hirar kasashen duniya tun ina saurarensu har na fara jin bachi, kwantar min da kujerar motar yayi na kwanta abina kamar ina cikin motar ubana. Cikin kankanen lokaci aka gama dinka lace din doguwar riga aka yi min ba mai mai doguwar kwaliya ba a wuya kawai aka saka bakin lace din sai a hannu. Tsabar farinciki ji na yi kamar na rumgume shi. A motar da muka tafi muka dawo ita kuma Safeena ta shiga motarta dabam, ban bari ya shiga cikin gidansu ba na ce ya sauke ganin magariba ta gabato.
“Amman Mamanki tace ba zaki je ba ko shi step brother dinki”
Na yi kamar ban ji ba na bude motar na fita.
“Kin gurin da ake dinner ne?”
“Eh na sani gidan Baba Dattijo aka saka”
“Akwai wanda zai kaiki?”
“Aa”
“Idan kin shirya ki zo na kaiki”
“Toh na gode sosai Abiey”
Na dauki jakata ta makaranta sai kuma na juyo na kalleshi.
“Ko dai na bar kayan a nan kar Mama ta yi min fada? Kuma Ammy zata maka fada kai ko?”
“Karfe nawa zaki je?”
“8:30pm”
“Zan jira ki a kofar gate”