← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 127

Sashe 44

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba za a ayi ba, kuma na fada miki idan ya sallamo Zahra ta sake fita ta fita kenan sai dai ta nemi wani gidan”

“Zahra kam ba, bata da inda ya fiye mata gurin da nake zaune, idan har ta bar gidan nan to aure ta yi ko kuma ta bar shi tare da ni, domin idan bana har kace zaka kori Zahra a gidan nan to kamar ka kareni ne tare zamu tafi”

“Ruwanki, ni dai kin ji na fada miki gidan ba ta sha ba ne da za a rika zuwa ana faka min da motoci ban san su waye ba, ai duk abun da kuke a bayan idona mutanen unguwa suna fada min”

Ya fada yana daga kafadunsa, Mama ta kalleni.

“Saka Hijab ki tafi”

Na juya ina jin yadda zuciyata ke tafarfasa na shiga dakin na dauki Hijab dina na saka na fita, kasancewar babu wuta a line kuma motar tashi baka ce ban iya fahimtar inda ya faka motar ba har sai da ya kunna hasken motar, sannan na karasa sai ya bude motar ya fito ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata.

“I miss this face, da a kebe muke Zahra da na rumgume ki na ji sanyi”

Na sauke kaina kasa ina murmushi.

“Ji annurin fuskarki the smile your pretty face i miss you a lot”

Na dago na kalleshi duk da kasancewar bana ganin fuskarsa da kyau saboda hudun yau da babu ko farin wata.

“I miss you more Abiey”

Ya jingina da motarshi ya daga kanshi sama yana murmushi mai sauti.

“Wow....”

Na kuma na gyara tsayuwata hango Baba tsaye kofar gida, yana ďan haske haske da fitilarshi.

“Abiey...”

Ya dago kamar zai kai bakinsa saitin kunnensa.

“Hiayatee...”

Na dan matsa baya kadan.

“Ina son zan saka maka number Mama idan zaka zo ka kira ni sai a fada maka inda zamu hadu”

“Miyasa?”

“Ba komai mutane suna saka ido a nan kuma Baba baya son haka”

“Amman akwai inda zamu hadu da ne da yafi kofar gidanku?”

“Akwai dalili, yanzu ma ina son na koma ciki”

Na karbi wayarsa na saka mishi number Mama sannan na mika nasa sai ya hada da hannuna ya karba.

“Look Zahra idan akwai wata matsala ki fada min, karki boye min komai, ina son na yi magana mai yawa mai tsawo da ke amman na lura kamar baki cikin natsuwa, ki fada min idan akwai wata matsala”

Na zare hannuna.

“Ba komai, zan shiga ciki sai da safe”

Na fara tafiya da sauri gabana sai faduwa yake gani nake kamar Baba zai iya zuwa yayi masa cin mutunci, ni kuma ba zan yi farinciki da hakan ba domin ko kadan a yanzu bana son abun da zai bata ran Abiey.
[10/30, 11:42 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣3️⃣

A kofar gida na wuce Baba na shigo ciki, sai ya biyo bayana.

“Na fada miki ko? Kar na sake ganinsa kofar gidan nan, idan kuma ya sake zuwa kuma kika fita to kin fita kenan”

Na dan juyo kadan na kalleshi sai dai ban ce na nufi dakin da nake kwana, ina shiga sai na jingina na lumshe ido har lokacin kamshin turaren Abiey be fita a hancina ba, samun kaina na yi da murmushi ya lumshe ido ina jin wani irin kewarsa da annashuwa da na dade ban ji irinta ba.

“Zahra”

Kiran Mama ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi sai na amsa na fito.

“Karbi ga waya”

Na karaso na mika hannu na karba, da fari na yi zaton number Dr Hamid zan gani sai dai ganin number da na kasa cireta a kaina ya saka na kara jin wani farinciki ya lullube ni, sai da na shigo cikin ďakin sannan na kara wayar a kunnena.

“Hello”

“Hiayatee...”

Na yi murmushi ina jin sunan har cikin raina.

“Murmushi kike yi”

Na yi saurin daga maishi kai kamar yana gabana.

“Yanzu kuma kin daga kai...”

“Ka fara duba”

Na tambaya ina nufar katifar na zauna.

“No na san ki dai in and out me kike yi yanzu?”

“Komai kawai ina zaune dai”

“Kawai ina zaune dai...”

Bayan kalmar farkon ta karshen a tare muka karasa ta saboda ya san abun da zan fada kenan, mun saba idan ya kira ni zai tambaye me na ke yi, idan ina wani aiki na kam fada masa, amman da zarar na ce komai to kalmar da zata biyo bayan kawai ina zaune dai...

“I know everything about you Zahra, abun da kike so da wanda baki so, abun da yake saka ki a cikin bacin rai ko damuwa da kuma wanda ke faranta miki rai, ban manta komai ba kuma ban goge komai daga rayuwar da muka yi a baya ba”

Yayi shiru yana sauraren numfashi dake sauka a sauri sakamakon zuciyata dake bugawa da karfi.

“I miss you i mean i miss you so much, ban yi zaton wata rana zata zo min da wuri haka da zan sauraren muryarki ko na yi magana ki saurareni ba, kyautar ganin fuskarki da kika min a dazu ta fi duk wata kyauta da za ayi min a duniyar”

Ya sake yin shiru sai kuma yayi murmushin da sai da na ji sautinsa a kunnensa na dama.

“Rayuwa bata da sauki idan babu ke Zahra, na saka budewa ko wace mace zuciyata na kasa yarda akwai wata mace da tafi kyau natsuwa hankali, balle har zuciyata ta raya min na so ta, ba zan ce na gaji ba, amman jiki yai sanyi kuma zuciyata ta yi rauni bayan na rasa ki, har nake ganin kamar ba zaki dawo a gareni ba, but wani abu ya tsayar da ni cak kuma ya kasan zaka ni farinciki idan na tuna shi, kin san me ye?”

“Aa Abiey...”

Na fada da sautin dake karantar da shi kuka nake kamar kama da na farinciki da kuma kewar juna.

“Idan na tuna cewar kina farinciki a inda kike, wannan abun ya kan saka na ji hankali ya kwanta, as long as zaki samu farinciki zan iya jure ko wace kalar rayuwa, matukar ke zaki samu farinciki, but Zahra duk tsawon kwanakin nan zuciyata soya take ni kadai na san halin da nake ciki, na kasa daina dorawa Dr Laifi, every minutes every seconds yana tuna min da ke, idan na ga wata mace ke kike fado min a rai, kuma a haka ban tana kawowa a raina wata rana zaki tsaya ki saurareni ba”

Na runtse ido ina kai hannuna saitin zuciyata na hawaye na sauko min wasu kan wasu.

“Rayuwata bata da sauki Zahra, ga tsanar Mai Martaba ga rashinki na sha wahala a zuciyata ban san wani lokaci da na yi farinciki na tsawon sati ba, ban san wani abu da ya faranta min rai irin yau ba, Allah da ya dora min kaunarki shi kadai ya san yadda nake son ki Zahra, and i know kin yi rayuwa da tsanata a ranki and that's the most painful part”

Ya karasa yana dariyarsa mai kyau sai ya kai hannu na share hawayena, sannan na bude ido ina shan jan dake taruwa a hancina.

“Kuka kike yi? Don't make make me cry, if not i will knock your head saboda kin san hawaye ya fara taruwa a idona”

Kusan a tare muka numfasa sai dariyar data fito bakina da wanda ta fito bakinsa suka yi tarayya da juna gurin fitar a tare.

“Ni ma na wahala kamin na saba, na sha da ci kamin na fara dandanar zakin zaman aure, da fari na yi zaton ba zan iya ba, duk wani motsi da Deen zai yi zai tuna min da kai ne, wani lokacin na kan kirashi da sunanka, a haka dai har ya koya min yadda zan manta da kai, bayan zuciyata ta dade da karbar tsanarka, amman na kasa goge komai naka duk da kasancewar na sabawa zuciyata tsanarka”

Ina jin lokacin da ya busar da iskar bakinshi.

“Ya aka yi kika aminta da ni a yanzu Zahra? Taya kika gane gaskiya?”

“Ta hanyar fada min da ka yi, miyasa baka fada min haka ba tun da?”

“Ada can ba ni da hurumin magana da ke balle na fada miki ki fahimta, secondly ba mu da wani evidence da zan iya yin shari'a da Deen akansa, thirdly na san idan na maka shi kotu zan daga miki hankali ne kuma zan karawa kaina tsana a zuciyarki ne, amman kin ga yadda Allah yake ikonsa”

Na yi shiru zuciyata na min wani iri.

“Hiayatee...?”

“Na'am”

Na amsa da wani irin siga da ban san taya lafazin bakina na sallace da shagwaba ba, duk kuwa da irin nauyinsa da nake ji na abubuwan da suka faru.

“Ahhh Awwww i miss this Shagwababbiyar yarinya ji fuskarta”

Na yi dariya shi ma dariyar yake.

“Na zo na ganki?”

“Ba yanzu ka tafi ba?”

“Ban isa gida ba ai, na kasa hakuri ne shiyasa na kira na sake jin muryarki and i need to see again and again and again and again and again”

“No ka ga yanzu ina bukatar hutu, kuma mutanen unguwa za su fara saka mana ido, shiyasa bana son ka zo har sai ka kirani, after that yaushe na haihu? Ai ya kamata na dauki lokaci kamin ace ina tsayuwa da wasu”

“Okay Babe amman Wallahi i need to see your face again ga wannan wayar babbar waya ce da zan iya kiranki mu yi video call”

“No karamar waya ce”

“Na siyo miki babban wayar yanzu?”

“No wannan ma ta isa zamu iya magana ai”

“Okay Zahra duk yadda kika ce haka zan yi, kamin na manta Safeena tace na gaisheki”

“Safeena na duniya daman?”

Daga haka muka shantake da labarin rayuwar baya, daga bisani ya bijiro min da tambayar yadda aka yi na fahimci gaskiya, sai na fada masa sai dai ban yarda na labarta masa abun da Baba da Hajiya suka min ba. A daren ranar da waya na kwana a kunnena tun yana min magana ina iya ji na amsa wata na yi murmushi ki dariya a wata maganar har bachi ya sace ne.

ABIEY POV.

Murmushi yayi yana sauraren yadda take shigar da numfashi da fitarwa irin na wanda bachi yayi masa nauyi.
Chapter 44 · 0% Book details