← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 127

Sashe 79

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Babu alakar komai yake zuwa gurinki?”

Na nuna bayana.

“Abokin Abiey ne, Abiey tsohon Saurayina”

“Kin taba fada min haka”

Na yi shiru na bata fuska sosai alamar ina daf da fashewa da kuka.

“Wannan ne karo na biyu da zan tambaye ki wacece ke Zahra, ina son sanin wani abu daga tahirin rayuwarki wata kila hakan zai amintar da ni ga wani abun da nake ji a zuciyata game da ke, kin yi min abun da ba kowa yake iya yi ba, kuma har gobe ba zan manta da ceton rayuwata da kika yi ba ko kadan bana son na saka miki da mummunan abu”

Na hade hannayena guri daya ina yawo da su hawaye na sauko min, to ni na ina zan fadi wace ce ni.

“Ni.... Ni... Ni kawai wata yarinya ce da bata jin magana, na ta so a hannun Mamana na bude ido da ita ban san mahaifina ba, Mama ta fada min cewar tun ina ciki ya rasu, sai dai na san abokinshi domin shi ya auri mahaifiyarmu bayan rasuwar babanmu ya rike mu ni da yar'uwarta Maryam kuma shi yake juya mana duniyar da mahaifinmu ya bar mana, yana da wata mata daya muna kiranta da sunan Hajiya tun daga lokacin da dan'uwanta ya kaita makka tana da yara biyu Zaharadeen da muke kira da Yaya Deen a wacan lokacin da kuma Bahijja da ba zata wuce sa'a ta ba, haka na taso na gan mu kamar yan'uwa, Hajiya bata nuna mana banbanci da yarta wani lokacin ma sai ta yi min abu ba ta yi ma yarta ba, idan kuma muka yi laifi ni da ita Deen ne yake mana hukunci musamman ma ni domin ita tana jin magana ba kamar ni ba, mu biyu Mama ta haifa sai dai ni ce marar jin magana idan an hana ni abu sai na aikata idan kuma aka ce na yi ba zan yi ba. Ba ni da kawa sai Hafsat wata yar Kaduna ce kanwar makociyarmu ce da yayarta ke rikonta a gidanta da take a aure a nan Kano, a rayuwata na tsani zuwa makaranta sai dole sai dai Hafsat tana cilasta min zuwa domin ita tana son zuwa makaranta ba kamar ni ba, wani lokacin sai Deen ya ba ni kudi ko kuma ya kai ni makarantar wani lokacin kuma zai je ya dauko ni, wani lokacin kuma idan na dawo daga makaranta gidansu nake tafi na wuni idan na yi wani laifin ma can na ke guduwa sab, wata rana mun dawo daga makaranta muna tafiya tare da Hafsat muka biyo ta gurin masu siyar da kayan marmari, daman mun saba mu kan biyo ta gurin mu tsinci wanda suka zubar wanda zamu iya sha mu sha wanda ba zamu iya ba kuma sai mu zubar.

Bayan mun gama tsinta muka nufi gida muna tafe ina sha ita dai Hafsat bata sha saboda tan mata fada a gida cewar ta daina cin abun a hanya, ni ma kuma an yi min hudubar sai dai bana jin magana balle na daina kuma ni a ganina ba komai ba ne cin abinci a hanya, sai da muka shiga unguwar sannan kowa ya nufi gidansu, a zauren gidan mu na ci karo da Deen ya fito daga cikin gidan, ina ganinshi na yi saurin boye lalatacciyar kwakwar dake hannuna a bayana na turo baki gaba.

“Zahra me kike ci?”

“Ba komai”

Na amsa a shagwabe ina kara cinno bakin gaba kamar zai fado.

“Sau nawa za a fada miki cin abinci a hanya babu kyau?”

“Da na shigo cikin gida ne nake ci”

Hannunshi ya saka ya kama bakin Hijab dina ya goge min bakina da fuskata.

“Dan Allah ki zaina cin abinci a hanya Zahra ba kyau, kuma wannan fruit din da kuke tsinta fa ya lalace wanda ba a so ne kike dauka kina sakawa a cikinki, irin shi sai ya saka miki ciwon ciki ai”

“Ni dai ina so haka nan”

Na fada a shagwabe ina karasa taune kwakwar dake bakina.

“To Allah ya sauwake”

Ban damu da na amsa da Ameen ba na wuce cikin gidan shi kuma ya bini da kallo har na shige, da sallama na shiga Mama ta amsa min waya a kunnenta tana watsar hakora da alama da mutum mai muhimmanci take wayar, hannunta na rike da iv da ledar cingan, hannu na saka na karbi cingan din na bare na fara ci na zuba ragowar a jakata tare da kwakwar dake hannuna.

“Mama bikin waye za'ayi”

“Karanta ki ga ni mana ba yar bako ba ce ke?”

Na karbi katin na fada dubawa sai gani tsaye ina tsalle da murna bikin da muka dade muna jira ya zo wato bikin yar wan babanmu.

“Mama kin ga har bikin ya zo amman baki min ankon ba”

“Ai na fada miki ba ni da kudin yi miki ankon yanzu, kina da tufafinki goge ki saka, mutanen da ba su damu da ku ba, bikin ma sai da ya rage sauran kwana uku sannan aka kawo iv, ina cingan din ma”

“Gashi nan na zuba a jakata amman gaskiya Mama sai kin min ankon nan”

Na dauko cingan daya na mika mata.

“Ba fa ke kadai aka kawowa, ke da yar'uwarki kara ma ita sai ta shirya ta tafi tun da tana da aure ke ko ba kije ba baki da laifi ai”

“Mama bari na shirya na tafi na kai mata ko?”

“Ga abincin ki can”

Na tashi na shiga dakin da saurina daman akan yawo ba ni da na biyu, a gaggauce na ci abinci na shirya na sai na dauki hijabin Mama na boye a cikin nawa hijabin sai da na kai zaure sannan na cire hijab dina na jefo cikin gida na saka nata ina jin tana kirana na fice a 90 ina dariya, na san idan na dawo karbe Hijab din zata yi domin sabo ne ta dinka bata taba saka shi ba, ina isa titi na yi sa'ar samun abu hawa na hau, dan napep din da na hau mai far'a ne da son mutane abu ka da mace mai farin jini sai hira ta kaure tsakanina da shi, can na hango wani tsaye a gefen titi yana siyen kayan marmari a gurin da na saba cintar na kasa.

“Wallahi idan zan samu sa'a sai na sace ledar can”

Na fada ba tare da tunanin komai ba, mai Napep din dake jana ya juyo ya kalleni sannan ya kalli gurin da nake kallo.

“Idan har zaki iya satowa ni kuma zan kaiki”

“To idan aka kamamu fa?”

“Ba za a kama mu, gudu zan yi da Napep din kuma kamin ya shiga mota ai mun nisa”

“Ai to mu bar gurin”

Na fada ina lakawa domin mun yi nisa sosai da gurin.

“Zan iya komawa ai”

“Koma dan Allah”

Kamar wasa sai rage gudu ya yi kwana muka juya, sai dai mun yi latti muna dawowa mutumen na shiga motarshi.

“Ba mu yi sa'a ba”

Na fada ina dariya shi ma dariyar yayi, muka juya motar na gaban mu muka cigaba da hirarmu, kwatsan muka ka hango Mai Motar yana kokarin fakawa a gaban wani katon super market, aiko sai mai Napep din ya bishi muka faka bayan motarshi, muna zaune a ciki har sai da ya fito sai Mai Napep din ya juya Napep dinshi zuwa titi ni kuma na fita daga cikin Napep din na doshi inda yake tsaye yana kokarin bude motarshi ina ta saka yadda zan fisge ledar na gudu sai dai ina isa gurin sai zuciyata ta karaya na kasa yin komai sai tsaye na yi ina kallonshi ina kallon ledar hannunshi, fasa shiga motar yayi sai ya juyo yana kallona can kuma ya daga kai yana kallon harabar ko zai hango idan ina tare da wani ne.

“Kina son wani abu ne?”

Ya tambaya da muryarshi mai dadi sauraro, kai na girgiza mashi sai yayi murmushi ni ma na mayar mashi da murmushin na juya na fara tafiya.

“Excuse me kina bukatar wani taimako ne?”

“Aa kawai dai na ga kamar na san ka ashe ba wanda na sani ba ne”

Na amsa ba tare da na juyo ba, bina yayi da kallo har na shige Napep din na leko shi sai ya dago min hannu ni ma na daga mashi ina jin kunya, can kuma na kyalkyale da dariya.

“Ba ki karbo ba?”

“Ai ina ganin zubanshin na san da cewar idan na mashi sata ba zan kwanshe lafiya ba, kai kana ganin wacan ka san ďan masu kudi ne”

“Indai haka ne ai ba zai biyoki dan kin karbo ledar hannunshi ba, ni sai yayi min kama da wani dan kwallo ma Wallahi”

Na yi dariya, muka cigaba da hira har ya kai ni kofar gidansu Yaya Maryam, sai da na fita cikin napep din sannan na tambaye shi nawa zan bashi.

“Bana son ko asisi amman dai ina son ki taimaka min da number wayarki”

“Wallahi ba ni da waya”

“Kina budurwa ace baki da waya ba zan yarda ba”

A take na daga mishi hannuna na nuna mishi.

“Ka gani da gaske na ke Wallahi babu waya a hannuna”

“To ta ina samari suke kiranki”

“Wasu dai ina ba su number Mamana amman tana min fada”

“To ki ba ni a haka ko kuma ni na baki tawa”

“Aa sai dai na baka ta Yayana idan ka kira sai kace mashi Zahra kake nema”

Ya miko min wayar na karba na saka number Deen daman ina da number a kaina na saka mashi number yayi saving.

“Allah yasa dai idan na kira ki dauka kin san masu kyau ba kowa suke sulawa ba”

Na yi dariya.

“Wallahi zan dauka”

Da haka muka yi sallama sannan na shiga cikin gidan, na tafi sa'a ko da na shiga tana gurin wanka gashi yaronta baya nan domin a lokacin danta daya tana da cikin na biyu, kulolin abincinta na bude na dauki plate na zuba na fara ci dan naman miyar na tsame na cinye ina ta sauri na cinye kamin ta fito, sai dariyarta na ci.
Chapter 79 · 0% Book details