← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 127

Sashe 40

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abiey ni ma da zaka dauki shawarata da ka hakura da yarinyar nan ko da na dan lokaci ne, domin abun da ta yi bata kyauta ba yanzu kuma ace duk bayan cin mutuncin da ta yi maka a can gidansu kuma ta biyo Ammy har gida ta fada mata haka? Tsakani da Allah ko wace uwa ce dole ranta ya bace, and yes ni da Ammy duk ba zamu fada maka abun da zai cutar da kai ba so nima shawarar da zan baka ka auri Yasmin idan ya so Zahra sai ta zo a ta biyu”

“Ko na auri Yasmin ba zata jidadin zama da ni ba, saboda zuciyata kwata kwata bata gurinta”

“Koya zaka yi har ka saba, Abiey ya kamata ka tausayawa yarinyar nan, kai ka jefata a cikin wannan halin idan baka aureta baka mata adalci ba, yanzu kuma ni na zan baka shawarar ka ce ma Mai Martaba cewar baka son yarinyar nan ba”

Ya shafa kansa ya jingina jikin motarshi yana sauke ajiyar zuciya.

“Me zan yi Sauban? Na yi shiru kawai na saka ido ina kallon yadda abubuwa suke wucewa?”

“Abiey ba ko yaushe ake kwana akan gado ba, be zama lallai abun da kake so ka samu ba, baka san tsarin da Allah yake maka ba”

“Duk da haka dai i need to talk to Zahra maybe zata ba ni dama ta saurareni”

“Allah yasa ta saurareka din”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya sauke wayar ya bude motar ya shiga, be tsaya ko'ina ba sai da ya isa unguwar su Zahra, da fari nisa da gidan ya faka kamin ya karaso gaban gidan daidai inda ake gina masa nasa gidan ya faka motarsa yana kallon kofar gidansu, tunanin yake yadda zai fuskanci Zahra, ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da kujera ya jingina. Daga kwance da yake ya hangota ta sauka Napep ta shiga cikin gidan sai kuma ta fito ta sallami Mai Napep din ta koma ciki, ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na barkatai.

ZAHRA POV.

Jin hawayen ba za su kare min ba yasa na bude ido na aje hotunan da suke hannuna na mike tsaye.

“Zahra tafiya zaki yi?”

Hajiya ta tambaya sai na daga mata kai har lokacin hawaye nake.

“Ba zaki ce komai ba?”

“Da ace Deen yana raye da na yi magana da yawa har sai kalamaina sun kare, amman a yanzu babu abun da zan fada domin ba shi da muhimmanci, sai dai ki sani ke da Deen kun cutar da ni cutarwa mai girma, kin san abun da ďanki ya aikata amman kika rufe baki fada min ba”

“Wace uwar ce zata so ďan wani fiye da nata? Zahra duk abun da Margayi ya aikata ya aikata ne saboda yana sonki kuma yana ganin ba shi da wata hanya da zai mallakeki sai wannan”

“Wannan ba so ba ne, miyasa be fada min ba? Ko da zan ki shi ya kamata ya furta min, ba ya lalata soyayyar wani ba, kuma da kazafi mafi muni ya kuma saka na tsani wanda shi yake da Gaskiya”

Na furta ina jin kamar na dora hannu a kai na yi ihu. Bahijja dake kuka ta taso ta rike hannayena.

“Dan Allah karki furta wata mummunar kalma akan yayana, da kin san yadda yake son ki da baki ji haushin abun da ya aikata ba”

“Gaskiya ne, saboda baki taba soyayya ba, baki san zafin da ake ji idan aka rabu da masoyi na gaskiya ba”

Na fisge hannayena na fice daga gidan ina jin wani irin kuka da bacin rai, lokaci zuwa lokaci nake yarfar da hannun da na saka na mari Abiey da shi.

“Ka yafe min Abiey ka yafe min dan Allah”

Na furta ina jin kamar ace yana tsaye a gabana na durkusa har kasa na nemu yafiyarsa, sai kuma maganar Ammy ta dawo min a zuciya gargadin da ta yi min da kuma irin fusatar da ta yi, yanzu na fahimta tana da gaskiya abun da na yi ban kyauta ba sai dai na aikata hakan ne a cikin rashin sani, na bata hakuri? No ba lallai ne ta fahimta ba wata kila idan na nunawa Abiey na fahimci gaskiya zai iya fasa auren Yasmin matar da Mai Martaba ya zaba masa hakan kuma zai haifar da matsala a tsakaninsu, bayan kuma na san da akwai rashin jituwa a tsakaninsa da Mai Martaba.

Har na iso gida tunani nake kala kala wata zuciyar na ce min na nemi yafiyar Abiey a yayinda yar'uwarta take kokarin hana ni. Sai da na shiga gida na karbi kudi gurin Mama sannan na bawa mai napep din na koma jiki babu karfi idon kam idan akwai abun da ya fi kumbura yayi ga wani ja da yayi min kana ganina kasan na yi kuka. Dakin Mama na shiga na zauna akan ledar tsakar dakin na sauke kaina kasa for the first time na ke jin wani irin kunyar Yaya Maryam da kuma jin rashin kyautawar abun da na yi, hannuna na hadu na saka ina matsa na daman.

“Me ya faru?”

Mama ta tambaya sai na dago na kalleta wasu hawayen na taruwa a idona.

“Ammy ta min gargadi akan Abiey, tace Mai Martaba ya masa mata bata son na zama silar rusa auren kuma ta ce idan har zata masa magana ya ji ba zai sake zuwa gurina ba”

Ina rufe baki Mama ta taba hannayenta.

“Haka na ke so, ta kyauta yanzu kan ba kare bin dabo, kin ga kin hita wulakanta mutumen da ya fiki komai kuma ya dawo yana bibiyarki saboda Deen”

Na runtse ido sosai ina jin kamar kuka zai kubuce min.

“Mama na yi magana da Hajiya kuma ta tabbatar min da abun da Abiey ya fada min da gaske ne Deen ya shirya komai saboda ya bata alakata da Abiey”

Yaya Maryam ta kai hannu ta dafa ni.

“Mahaifiyarsa ta sani kenan?”

Na daga mata kai sai na rika hannun nata da ta dafa ni da shi.

“Ki yafe min na aikata furta miki kalmomin da ba su dace na yi ba saboda ina cikin fushi kuma ban fahimci komai ba”

Na fada ciki kuka na tausayawa kaina da kaina.

“Tun tuni ina ta nuna miki baki fahimta ba, tun da daga lokacin da likitoci suka ce ya kebe kansa ya boye miki ya kamata ki fahimci cewar ba son gaskiya yake miki ba”

“Ban gane ba, saboda ina masa kallom jarumin da ya ceci rayuwata a lokacin da Abiey ya yaudare ni, yanzu ban san abun da zan yi ba Tsanar Deen ko kuma kaunarsa? Na nemi yafiyar Abiey? Ko kuma na nuna masa cewar na fahimci ba shi da laifi? Kaina a kulle yake”

Na furta ina fashewa da kuka.

“Karki tsani Deen Zahra, shi a yanzu baya raye kuma akwai ďa a tsakaninku, kuma bayan Deen ya aureki be cutar da ke ba, be taba dukanki ba, be tana hanaki abinci ba, be taba son bata ranki ba, ba zai aikata miki wani abu da gangan saboda ki shiga damuwa ba, wani lokacin zuciya tana kai bawa ga halaka domin tana raya masa abubuwan da aikata su haramun ne ko kuma saka kai a damuwa ko kunci, saboda kar hankalinki ya tashi ya saka ya boye miki ciwonsa, mahaifiyarsa ma bata taba nuna miki kiyayya ba sai kauna, Deen yana sonki so mai tsanani wanda ya haddasa kishi mai zafi a zuciyarsa da har yake ganin idan kika dauki cutar zaki mutu da wuri ba tare da kin rayu da wani namiji ba, sannan mutum ne mai tsananin son kanshi shiyasa ya aikata abun da ya aikata saboda ya same ki, tabbas da ya nemi aurenki a halin da yake ciki ba zan taba bashi ba, ko da kuwa kin nuna kina sonsa amman ya canja saboda ke Zahra, idan har ba zaki iya yafe masa ba be cancanci tsana daga gurinki”

Na daga kai na kalli Mama da ta jero min kanli da bad'adin da ya kamata ya hana zuciyata tsanar Deen.

Shiru ne ya ciki ďakin baka jin tashin komai sai sautin kukana.

“Allah ya kyauta”

Mama ta fada sannan ta tashi ta fice daga dakin, sai na saka hannayena na dafe kaina ina jin yadda yake sara min kamar zai cire. 

“Ki yi hakuri Zahra, ta kuka kuma yanzu ai ta kare tun da Deen baya raye, godiya ya kamata ki yi ma Allah da ya saka Abiey be daina kaunarki ba har yanzu”

Kallonta na yi zuciyata nayi mini wani irin zafi.

“Yaya Maryam kin san zafin da mace take ji idan mijin da bata so ya kusance ta? Kin san yadda na sha wahala kamin na koyawa kaina iya zama da Deen? Ba karamin yaki na yi ba na yi ba da zuciyata kamin ta aminta da Deen a matsayin mijina, a duk tsawon zaman da muka yi ban taba jin son Abiey ya fita a rayuwata ba sai dai na ji na tsane shi saboda abun da ya aikata ba, a duk tsawon lokacin nan ina kallon Deen ne a matsayin mai gaskiya Abiey kuma mayaudari, ban taba jin ina kaunar Deen ba ko da na rana daya amman a haka na koyawa kaina sonsa har nake jin na fi ko wace mace dace da miji, miyasa ba zai gina tashi soyayyar a muhallinsa na dabam ba? Miya zai saka na tsani mutum da zuciyata bata san kaunar kowa ba sai shi? Akan me zai bar ni ina kallon wani a matsayin mayaudari? Wane irin kalami ne ban yi ma Abiey? Wane irin cin mutunci ne ban yi ma yan'uwansa ba? A kowace sallah sai na roki Allah ya saka min akan abun da Abiey yayi min duk saboda abun da Deen ya shirya Yaya Maryam, rayuwar da nake mafarkin ginawa da Abiey ta rushe saboda Deen...!”

Yaya Maryam ta sauko ta zauna kusa da ni ta rumgume ni sai na kwanta a kafadarta ina kukan da nake jin kamar na mayar da zuciyata na huta. Muna haka yaro ya shigo da sallama Mama dake waje ta amsa.

“Wai ance ana sallama da Zahra a waje”
Chapter 40 · 0% Book details