Sashe 65
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Zan yi ta zuwa Zahra har zuwa lokacin da zuciyata zata samu natsuwa cewar kin samu kwanciyar hankali, ke din abar tausayi ce duk wata kulawa da zan baki ko na nuna akanki zan yi saboda Abiey i know you need him”
Ya dauke numfashi na tsawon dakika biyar sannan na numfasa na kwanta saman gadon.
“Karka fadawa Abiey ka zo nan”
“Kamin na zo nan sai na fada mashi zan zo, ba ce karka je ba kuma be ce ka je ba sai dai na san ya jidadi saboda ba zai iya komai a kai ba, ke kanki kin sani da ace babu wata matsala da ta shiga tsakaninku da yanzu yana nan tare da ke, please let me do his duty ko ba komai hakan zai san yaya mashi”
Ban san me zan sake ce mashi ba, a iyakar sanina akwai alaka mai karfi a tsakaninsu wanda ta wuce da aboka sai dai a kirata da yan'uwanta domin tun kamin na san Abiey ko na hadu da shi suke tare da Sauban Abiey ya taba fada min a tare suka ta so, saboda bana tunanin Sauban zai nuna min kulawa da wata manufa sai dan tausayi kamar yadda ya fada da kuma nunawa Abiey ya damu da damuwarshi.
“Karki cika kanki da tunani kuma idan kina bukatar wani abun ki fada min”
“Na gode”
Na fada ba tare sa na sake kallonshi ba har ya bude kofar ya fice. Sai tunanin Abiey ya dawo min sabo na san a duk inda yake a yanzu baya cikin kwanciyar hankali da natsuwa domin ni ma na kasa jurewa balle kuma shi, sai dai ina addu'a da fatan hakan ya zame mana alheri a tsakaninmu.
Wata kila a cikin maganin da Dr Hamid ya ba ni akwai na bachi domin fitar Sauban da kamar minti goma bachi yayi gaba da ni ban farka ba sai da aka kira sallah La'asar shi ma kuma hayaniyar hirar da Mama take da Hajiya Jamila ne ya tashe ni, kamar zata hadeye haka ta rika murna da farkawata tana ta min sannu da jiki idan Mama ta dauko abu zata ba ni sai ta karba ta mika min, abinci kadan na ci ina ta kallon Amir dake dunkule a cikin kayan sanyin a hannun Mama, bayan na gama ta karba ta aje ta dauki ruwa ta miko min na karba na sha, sannan ta matso kusa ni tana kallona kamar mai tsoron yi min magana, sai kallon Mama take hakan ya karantar da ni akwai magana a bakinta.
“Mama lafiya?”
“Wai so take ki bawa yaron Nono”
Na kallin yaron.
“Muna asibiti fa wani zai iya gani”
“Zan tsaya jikin kofar sai ki ba shi idan na ga wani sai na fada miki, wallahi rabon shi da abinci tun jiya madarar nan tsoron ba shi ita nake saboda tana saka shi ciwon ciki kuma Dr yayi magana da likitan da mijina ya kawo tace ta ba shi kwana biyu idan ya samu lafiya shikenan idan kuma be samu ba zata fara nata bincike, Dr Hamid na fada mata cewar yana kan wani aikin ne na magani kuma ba wani magani da yake kawai dai mun dogara da ke, jiya ma na yi magana da Dr Hamid yace min za a iya sallamarki a yau saboda jikin na ki da sauki albashi sai a cigaba da kula da ke a gida”
Hausawa suka ce ďan halak kaki ambato tana rufe baki Dr Hamid ya shigo dakin rike da wasu files.
“Yauwa gashi nan ma ya zo”
Ya kalleta sannan ya kalleni.
“Minene?”
Ta kora mishi bayani da kamar magiya.
“Na ce za a iya sallamarta amman ban ce ki yi magana da ita ba”
Ya fada yana kallona.
“Na ji ka ce ta ji sauki, zuwan nan ma saboda ta bashi nono ne idan Hubby ya san na fita zai yi fada saboda baya son ana fita da yaron nan”
“Eh ta ji sauki hakan ba yana nufin ta cigaba da abun da kike so ba, ki tafi gida zan yi magana da ita”
Ya fada a tsawace ba ita ba ko na na yi mamakin yadda ya yi fusata har yake daga murya ranshi a bace. Bata sake cewa komai ba ta mika hannu ta karbi Amir ta fice.
[11/10, 9:30 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣4️⃣
Bayan ta fice daga ďakin ya juya shi ma ya fita be dade ba ya dawo ya kama hannuna ya saka min abun auna jini sai Mama ta ce.
“Doctor idan Zahra ta samu lafiya zamu iya komawa gida ta cigaba da bashi nonon saboda ita ma ta cigaba da wankan ruwan zafinta kar jikinta ya danyence”
Cikin mutuntawa Dr Hamid ya ce.
“Amman Zahra ta samu lafiya, amman ba za a cigaba da yi mata suraci ba, wankan ruwan zafi ne dai ba zan hana ba, kuma zancen ta koma a gidan nan wannan ra'ayin Zahra mu bar ta har sai ta zaba”
“Ba ni da matsala Dr indai zan iya komawa ni a shirye nake”
“Karki yi wani abu saboda ni ko saboda Jamila ko saboda wani dabam, always listen to your heart, baki san kina da hakkin ki ba? Karki gina kanki da rayuwarki akan ra'ayin wasu”
Ya fada bayan ya duba jinin nawa ya cire min abun a hannu.
“Ba ni da matsala ni akwai wanda bana son ya sake zuwa ya same ni a nan indai zan iya cigaba da shan maganina ina son a sallame ni”
Murmushi yayi.
“Mutumen dazun ko? Any way daman idan abun ya zo da sauki ba ma rike mutum a asibiti mu kan sallame mutum mu dora shi akan magani da kuma dokoki idan zaki iya kiyaye zamu iya sallamarki, kuma abun ya zama na gida zan cigaba da dubaki”
“Inshallah zan kiyaye”
“Good, idan zan wuce gida zan tafi da ku”
He said with light smile on his face. Na amsa mishi da kai sai da yayi wasu rubuce rubuce sannan ya dauki kayanshi ya fice. Yaya Maryam duk abun da ake bata ce komai kamar bata cikin dakin, ta taso ta dawo kusa da ni ta zauna.
“Wai Zahra anya Likitan ba ďan'uwan matar nan ba ne, suna yanayi sosai kuma yanayin yadda ya daka mata tsawa idan be isa da ita ba ba zai mata haka ba, saboda kawai yana likitanta ba zata dauki wannan daga gareshi ba”
“Yace min kanwarshi ce uwa daya uba daya”
“Ah no wonder ni kam abun ya ba ni mamaki sosai na ga kama a fuskarsu yau”
Mama ma ta cika da Mamaki ita da Yaya Maryam, kamin daga bisani Yaya Maryam ta dauko zancen abun da ya faru ciki har da rabuwar mu da Abiey da kuma zancen komawarmu gidan Hajiya Jamila. Har suka ci suka sude ban ce komai ba domin hankalina da tunanina ya tafi wata duniyar, muna haka yan'uwan Mama suka yi ta shigowa duba ji suna min ya jiki na bangare Baba na na sun shigo sai dai ba su kai na Mama ba, Dr Zainab ma ta shigo sai dai bata dade ba ta fita.
Misalin 6 na yamma Dr Hamid ya dawo ďakin bayan ya kammala aikinshi, sai da ya kara auna ni sannan ya saka ma'aikatan asibitin dake share share suka kwashi kayanmi zuwa gurin motarshi. Mama da Yaya Maryam da babban ďanta Abdulkareem suka take musu baya mi kuma na jero tare da shi ina takawa a hankali yana ta yi min hirar asibitin yadda aka tsara gurin da ya fara aiki kamin daga bisani ya dawo nan.
Muna isa yayi saurin bude min gaban motar.
“Bismillah Zahra”
Ban kawo komai a raina ba na shiga na zauna ya rufe, sannan su Mama suka bude baya suka shiga, tun da muka kama hanya ban kalli inda yake ba balle wata kalmar ta fito daga bakina zuwa gurinshi, shi ma kuma be sake ce min komai ba wata kila saboda su Mama suna cikin motar ne. Sai da muka isa bakin gate din gidan sannan ya kira Hajiya Jamila ya sanar da ita cewar mun iso sannan ya danna horn masu gadin suka leko ganinshi ne yasa suka koma suka bude gate din shi kuma yaja motar zuwa cikin gidan, na yi zaton a harabar gidanta zai faka gurin da nake hango manyan motoci na alfarma, sai ya faka a gurin da na ke kyautata zaton BQ ne domin yanayin gurin ya nuna haka, Mama ta fara budewa sannan na bude na fito sai hango Hajiya Jamila muka yi ta nufo inda muke da saurinta.
“Maa Shaa Allah kun dawo”
“Allah ya nufa”
Mama ta amsa mata, sai ta wuce gaba muka bi bayanta zuwa cikin bq din mai kama da wani karamin gidan Mai kudi domin har da ac aka saka a dakunan gudan biyar bayan an kawata ko wace kofar ďaki da fulawoyi, yadda gurin yake tass sai ka rantse da Allah akwai mutane a gurin domin an share ko'ina an goge ba datti ko kadan.
“Wane ďakin kuke so?”
Dr Hamid ya tambaya yana kallona da murmushi a fuskarsa.
“Ba mu da zabi”
Na amsa mishi ina dauke kaina daga barin kallonshi.
“Duka ďakunan iri daya ne babu banbanci, sai dai na ga kamar kuma da kaya da yawa zaku iya rabawa ku saka wasu kayana a dayan dakin dayan kuma sai ya zama na kwanaku”
Cewar Hajiya Jamila, Mama kam tuni ta fara duba ďakunan har zuwa kitchen din dake can gefe, bandakin kuma yana cikin ďakunan tare da su, dakin farko muka zaba mai binsa kuma Mama tace zai zama na saka sauran kayanta.
“Amman dai ba dake za ayi aikin nan ba Zahra ki shiga ciki ki zauna idan gama gyara sai ki dawo”
Dr Hamid ya fada ganin Mama da Yaya Maryam sun fara daukar wasu kayan suna sakawa ciki.
“Ba wani gyara zamu yi sosai ba saboda dare ya fara, sai dai mu saka wasu mu bar wasu”
“Kamar gado da katifa da wardrobe ku bar masu aikin gidan nan su saka muku sai ku nuna musu gurin da za su aje bari na musu magana”