Sashe 18
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“An haihu ne abun da ta haifa be zo da rai ba”
Mama ta amsa mata.
“Ayyah Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Wayyo Allah”
Zuwa ta yi ta rumgume ta gabana tana sanye da rigar likitoci a iya sanina ba wannan asibitin Anty Zainab take aiki ba, wata kila wani abun ne ya kawo ta na dabam. Fashewa na yi da kuka sosai na kankame ta ina jin kamar na fada mata damuwata amman ba hali, sai kiran nake ďana ďana har ta kalli Mama tace.
“Namiji ne?”
“Mace ce”
Mama ta amsa sai ta sake ni ta bude kwali ta kalli jaririyar.
“Allah sarki”
Ta dawo ta sake rumgume ni, ita kai ni dakin da zan huta maimakon na zauna saman gadon sai na zauna a kasa na takure kuri daya ina jin wani jiri yana daukata. Ta yi bani hakuro har ta gaji ta fita ban daina kuka ba, bayan fitarta wata nurse ta shigo tare da magani ta Mama tace likita yace bani, Mama ta kalli Maryam.
“Ki tafi da jaririyar a gida a rufe ta, zan kira Hajiya na fada mata muna asibiti Zahra ta haihu abun da ta haifa be zo da rai ba, ki aje uwar sai na zo ayi gina a rufeta, zanen kuma ki wanke mata ki gyara gidan”
“Toh Mama”
Ni kuma na shura kafa a kasa ina kuka
“Ni mai rai na haifa....”
Mama ta yi saurin rufe min baki.
“Zahra ki dawo hayyacinki so kike ki jefa kanki a matsifa ne”
Na cije bakina ina kuka sosai, su Hajiya ma suna isowa kukan suka kasa Bahijja har da dora hannu akai, a tare da su kuma koma gida domin ban iya yi bachin da ake son na yi ba, ban kuma yarda na bari yayi min allurar da ya nufo ni da ita ba, shayin da aka hada min ma ban sha ba, bana bukatar komai a lokacin sai mutuwa, nakudar da na yi da wani azabar ciwon da na ji sai na manta da komai ďana kawai nake gani a idona, dama ace mutuwa yayi da hankali zai fi kwanciya fiye da ace yana hannun wata da bata san zafin daukar cikinsa ba balle haihuwa.
ABIEY POV.
Zaune yake kan machine din motsa jiki yana motsa jikin da be samu yayi da safe ba, Bluetooth a kunnensa yana kallon katuwar plasma dake gabansa, ya hada gudu kamar wanda yayi gudun fanfanlaki. Wayarsa dake kan dayan machine din a aje ta yi vibration sai ya danna Bluetooth din kunnensa.
“Hello”
“Abiey kana ina?”
“Ina gida gurin Ammy ya akai?”
“Na shiga ban ganka ba”
“Bari na fita ina dan motsa jiki ne”
Ya tsayar da machine din sannan ya sauka ya dauki wayarsa ya fito daga dakin na motsa jiki ya bullo cikin babban falon Ammy, be samu kowa a falon ba hakan yasa ya wuce kai tsaye dakinsa sai da yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito ya tura kofar bedroom din Ammy. Sai da ya fara karewa Dr Zainab kallo sannan ya kalli Ammy.
“Lafiya?”
“Wai Zahra ta haihu abun da ta haifa be zo da rai ba”
“Ohh....”
Ya furta not happy not sad, Dr ta juyo ta fuskance shi.
“Another news yaushe ka aika neman auren Yasmin ba ni da labari?”
“Plan ne kawai ba na gaske ba ne”
Ya amsa yana zaunawa kusa da ita wato kan doguwar kujerar da take zaune.
“Toh Momy ta kira ni tace Mai Martaba ya tura manyan mutane nema maka aurenta”
“Eh Anty ta yi waya da ni kamin su tafi ai yace a tambaya ko Ammy zata bada wani daga Familynta”
“Amman baku fada min Anty ta kira ba”
“Ba auren gaske ba ne kawai haka hakan ne saboda ya kare kansa, shiyasa ni ma ban bada kowa a cikin dangina ba”
Wannan karon Ammy ce ta amsa mata.
“To zai zama na gaske kuwa domin an tambayi yarinya ta amsa tana sonka kuma iyayenta sun baka, Momy ta kira ta fada yanzu nan ina kan hanyar zuwa”
Dr Zainab ta karasa tana murmushi, Abiey ya mike tsaye da sauri yana kallon yar'uwarsa, kusan a lokaci daya wayarsa ta yi ringing kiran Anty ya shigo ya amsa kiran da sauri.
“Hello Anty”
“Abiey ba ka yi magana da Yasmin ba ne?”
“What happen?”
“Toh iyayenta sun ce sun baka yarinya ta amsa tana sonka”
“What.....!!!?”
Ya furta da karfi baki sake zuciyarsa na bugawa da mugun karfi.
[10/9, 10:54 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣2️⃣
Ya cije lips dinsa ya sauke wayar ba tare da ya sake cewa Anty komai ba.
“Taya yarinyar nan zata min haka?”
“Miyasa ka saka ta a ciki tun farko?”
Dr ta tambaya, ya kalleta.
“Saboda ina tunanin mafita ce, i thought zata taimaka min”
“What if tana sonka?”
“No my body my wealth my heart is only for Zahra and her alone”
Ya fada yana nuna kansa, Ammy ta ce.
“Wata kila bata fahimci abun da kake nufi ba”
“Okay bari na same ta yanzu na yi magana da ita”
Yana fadar hakan ya nufi kofa kamin ya fita Dr ta ce.
“Yasmin is innocent Abiey ka yi magana da ita yadda zata fahimta don't hurt her feelings, tana zaman zamanta ka saka ta a cikin maganar nan yarinyar nan marainiya ce please ka bita a hankali”
Juyowa yayi yana mata kallon mamaki.
“Ita ta saka kanka, taya an tsara yadda za'ayi yarinya ta zo ta canja magana”
Ya juya ya fice rai a bace. Dr Zainab ta kalli Ammy tace.
“Ina ganin kamar Yasmin tana son Abiey”
“Na dade da fahimtar haka, taya mace zata ga kyakkyawan saurayi kamar ďana bata ce tana so ba, mutum ga kudi ga daukaka ga kyau ga sarauta”
“Yasmin ma ba zata duba wannan ba idan zata so shi, kawai dai tana sonsa ne, idan ba haka ba babu abun da zai saka ta amsa haka bayan yayi magana da ita”
“Kuma son Aliyu indai ba shi ya gani ya ce yana so ba, wahalar da kai ne, domin hankalinsa gaba daya baya gurin kowa sai Zahra”
Dr ta motsa kanta a hankali.
“Yeah she deserves Zahra And Zahra deserve someone like Abiey wanda ya kula da ita sosai domin yarinyar nan tana cikin damuwa sosai, ina tuna lokacin da aka yi wasa da rayuwar mijina yadda na ji balle kuma ace na rasa shi, ita kuma ta rasa mijin yanzu kuma ta rasa babynta so sad”
Ammy ta sauke ajiyar zuciya.
“Babu yadda Allah baya ikonsa, sai hakuri mutuwa babu yadda ba a ganta ba”
Mikewa tsaye Dr ta yi ta cire labcot din jikinta.
“Bari na sauka na ci abinci”
ABIEY POV.
Tafiyar minti shabiyar da kai shi gidansu Yasmin wato gidan Momy, ko parking din kirki be yi ba ya fito ya nufi kofar gidan, kamin a bude masa kofar falon yayi knocked ya fi a kirga. Momy ta kanta ta bude masa kofar
“Aliyu”
Ba karamin jihadi yayi ba na danna fushinsa ya dan saki ransa ya gaisa da Momy, sannan ya karaso cikin falon ya zauna ba tare da yace da Momy komai ba.
“Gurin Yasmin ka zo?”
Momy ta tambaya sai ya daga mata kai da sauri.
“Wata yar matsala aka samu Momy...”
“Na san da komai ai Ammy ta yi min bayani, yanzu haka kamin ka zo fada da nake mata kenan”
“Momy zan iya magana da ita”
“Bari na kira maka ita”
Momy ta tashi ta nufi dakin Yasmin, bata dade ba ta fito ta dawo ta zauna.
“Gata nan fitowa”
“Okay”
Ya amsa yana wasa da keys din hannunsa, shiru shiru babu Yasmin babu labarinta, hakan yasa Momy ta aika mata da kira daga inda take zaune.
“Yasmin.... Yasmin....”
Bata amsa ba sai kara rufa kofa suka ji an saka makulli, Momy ta tashi ta nufi kofar tana tabawa ta jita a rufe gam babu.
“Yasmin ki bude kofar nan kar ranki ya bace miye haka?”
Wani gumi ya karyowa Abiey ya mike tsaye ya nufo kofar.
“Yasmin bude kofar magana kawai zan yi da ke kinji”
A hankali yake maganar yana kokarin kwantar mata da hankali, Yasmin dake cikin dakin ta rufe idonta dake zubar da hawaye ta jingina da kofar ta sulala kasa, ita kanta bata san dalilinta na yin haka ba, kawai ta samu kanta da amsa musu da eh ne a lokacin kanen mahaifinta suke tambayarta.
“Momy ko zaki tafi ina son na yi magana da ita”
Momy ta amsa masa da kai ta juya ta nufi kitchen, sai da Abiey ya ga ta shige sannan ya kwankwasa kofar.
“Yasmin... Bude mu yi magana ta fahimta da ke kinji”
Ta girgiza kai kamar ance mata tana ganinsa.
“Yasmin dear please karki jefa ni a matsala, i face a lot of challenge bana son wata damuwa a yanzu i just want to focus on Zahra and her alone, ban san dalilinki na yin haka ba, wani ya cilasta ki ko kuma kuskuren fahimta aka miki ko bakinki ya subuce ce, amman na san kina daga cikin mutanen da suka san halin da nake ciki, ba za ki yi wani abu da zai kara jefa ni a damuwa ba”
Ya sake murda kofar.
“Yasmin bude kofar kin ji”
Haka yayi magana ya gaji da tsayuwa Yasmin ta ki ta bude kofar, har sai da Momy ta dawo gurin.
“Bata bude ba”
“Momy ko dai tana da aljannu?”
Momy ta yi murmushi.
“Yasmin da magana ma be ishe ta ba, babu wani iska sai iskanci irin na yaran zamani”
“To na ga mun yi magana da ita lafiya lafiya sai kuma na ji magana ta canja”
“Karka damu zan yi magana da ita, maybe tana jin kunyar abun da ta yi maka ne a yanzu shiyasa ba zata bude ba, amman ko da ita bata musu magana ba ni zan yi magana da su kanen mahaifin nata Inshallah”
“Okay thanks”
Ya fada sannan ya saki kofar ya juya tana tafiya a hankali har ya fice, sai a lokacin Yasmin taja numfashi ta aje tana jin yadda kamshin turarenta ke kara sa zuciyarta tana bugawa da karfi.
ZAHRA POV.