Sashe 81
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana rufe baki na nufi inda na jefar da uniform dina na dauka na saka su haka domin dawowar da na yi jiya ban wanke su ba ban ma wuni a gidan ba balle na wanke, da sauri na saka tufafin na dauki jakata ta makaranta na nufi inda talkamina suke na saka, sai da na kai bakin kofa na juyo ina fada mata cewar ban ci komai ba.
“Ita Hajiyar bata baki abincin ba?”
“Ta ba ni amman ban tsaya na ci ba saboda ina tsoron kar na zo ki dake ni”
“To ba zaki tsaya cin abinci ba ki yi latti, wuce ki tafi a haka, tun safe Hafsat ta biyo ki amman kina can gurin shashancinki”
Na san idan na kara wata maganar zata iya cewa zata dakeni, ba dan haka ba ba ba zan tafi makarantar ba sai na ci abinci ko kuma ta ba ni kudin makaranta, haka na fito cikin gidan fuska a narke kamar na yi kuka, na san idan na ce zan tafi makaranta a yanzu zan sha doka ne kawai a makarantar wata kila ma a hana ni shiga domin na yi latti sosai.
Hakan ya saka na nufi gidan Makotanmu daman na saba idan bana son zuwa makaranta ko kuma na yi ma Mama wani laifin gidan na ke guduwa na boya ba tare da Mama ta sani ba, babban gida ne da nake kyautata zaton masu shi ba su san darajar nera ba, domin an kawata ko'ina na gidan masu gadi har mutum biyu duk wani kayan alatu dake akwai a duniya akwai shi a gidan, ba abun da nake ji ma dadi kamar kasancewar matar gidan ta dauke ni kamar yarta, na kan zauna na yi hira da ita tana ba ni kyauta abubuwa sosai musamman idan zan tafi makaranta idan na leka gidan ta kan hada min tsarabar tafiya makaranta. Ammy mace ce mai far'a da son mutane ba kamar wasu masu arzikin da zaka tarar suna da izza da daukar kai ba. Ba wuce kwana biyu da tarewa a unguwar ba na leka gidan na gaishe tun daga lokacin sai na zama kamar yar gidan, sai dai ita bata taba zuwa na mu gidan ba Mama ma bata taba zuwa na su ba, a unguwar kam bana jin akwai mai shisshigin shiga gidan kamar ni, ni ma kuma ba wai ina zuwa saboda Allah ne ba, sai dan abubuwan dadin da nake tararwa a gidan da kuma alherin da take min.
Gate din na fara kwankwasawa dayan mai gadin ya bude min karamar kofar yana ganin ni ce ya fara tsokata irin yadda ya saba.
“Sarkin latti kullum sai ta yi lattin zuwa makaranta”
“Eh na ji kai kana zuwa makarantar ma, ai kara ni”
Na rama ina dan hararashi na nusa kai cikin gidan ba tare da fargabar komai ba, na bar shi yana dariya yana cigaba da tsokana ta. Karo na farko na tararda kofar falon a bude domin ba al'adar Ammy ba ce barin kofar falonta a bude, bakin kofar falon na tsaya ina cire talkamina ina kallon Ammy dake zaune a kan center carpet din falon wani katon namiji na kwance a cinyarta.
“Ni fa bana son yarinyar nan Ammy matse ni take idan ina magana da ita tun kamin na tafi yanzu kuma waya san yadda ta zama”
“Ita kuma Raliya fa?”
“Raliya ma Wallahi tattaba ni take idan muna hira Ammy lalata ni za su yi fa ni bana sonsu duka gaskiya”
Shi ne abun da namijin da nake kyautata zaton akwai alaka mai karfi a tsakaninsu yake fada a shagwabe gwaninn ban haushi, shiga na yi cikin falon ina gwalo ido da mamakin yadda mace zata lalata namiji. Motsin shigowata ce ya saka Ammy ta dago kai cike da far'a tana kallona hannunta na jikin fuskar namijin da ban san waye ba domin ban ga fuskarsa ba.
“Zahra”
Sai a lokacin na tuna ban yi sallama ba, komawa na yi na sake shigowa da sallama, sai ta saka dariya namijin ma tashi yayi zaune yana kallona, ina yin arba da fuskarshi gabana ya fadi mutumen da na tashi yi ma sata a super market, amman miya kawo shi nan? Kamar ya san zance sa na ke a zuciyata sai ya sakar min wani tattausan murmushi.
“Na hadu da yarinyar nan jiya”
Ammy ta kalleshi.
“A ina?”
“Na fito siya ma yaran Dr Zainab alawa, kin tuna?”
Ya karasa yana daga min gira kamar yana magana da wanda suka saba fuskarshi da murmushi, ni ma dan murmushi na yi na haye kujera na zauna daman can bana jiran ace min na zauna idan na zo gidan.
“Ammy good morning”
Na gaishe ta ina tunanin alakarta da wannan katon saurayi, ko tace min ďan ta ne ba zan yarda ba domin ban taba ganinshi ba kuma be yi kama da ita ba, bayan Dr Zainab ban san Ammy na wani ďa ko ya ba, ko da yake ban taba zauna na yi hirar iyalinta da ita ba.
“How are you Zahra ba ki tafi makaranta ba?”
Na cinno baki gaba domin ta tabo min gun da bana so.
“To Ammy ba na yi latti ba, kuma Mama tace sai na je saboda kawai na je na kwana a gidan Hajiya”
“Wacece Hajiya?”
“Kishiryar Mama ce kuma bachi ne ya sace ni ban samu na dawo gida ba, sai da safe shi ne wai sai na tafi makaranta”
Na shagwabe nake maganar kamar na fashe da kuka.
“Ahh kin yi laifi gaskiya akan me zaki tafi ki kwana a wani gurin ba gida ba?”
“Ammy it wasn't intentionally ai ban saba kwana a wani gurin ba”
“Ko dai baki saba ba ya zama na farko kuma na karshe, duk abun da iyaye basa so idan mutun ya aikata shi ba wata riba zai gani ba sai faduwa da bacin rai, karki sake kin ji? Ba kin fada min Mamaki ku biyu kawai ta haifa ba?”
Na daga mata kai.
“Kuma kin ce yar'uwarki ta yi aure, ke da kika rage kamata yayi ki zama mata sanyin idaniya kin ji? Kuma ki daina wasa da makaranta karatu shi cigaban mutum a yanzu”
“Toh, amman dai ba zanje ba yau na yi latti dukana za su yi, har ma manta kudina na anko a can gidan Hajiya”
“Biki zaku yi?”
“Eh...”
A take na kwashe labarin komai na bata, tun daga kan alakata da amaryar da yadda mahaifinta ya wofintar da mu da kuma ankon da Mama tace ba zata min ba.
“Yanzu dai tashi ki shiga kitchen ki duba idan akwai ragowar abinci ki dauka ki ci”
“Toh”
Na mike tsaye a take na cire Hijab din makarantar na aje akan kujera tare da jakar makarantar na fara nufar dinning domin a nan na san tana girke abincinta, bina yayi da kallo kamin ya juyo gurin ina jin lokacin da yake tambayarta wacece ni, sai ta yi dariya
“Zahra yar makontanmu ce ita ma auta ce kamar kai, sai dai ta fika saukin kai da son mutane, ban san iyayenta ba amman ita na santa kana kallon yadda take mu'amalarta kamar yar gida, ka san ni kuma da son yara sai kuma zama daya”
“She's so pretty Ammy, so friendly”
Har cikin raina na jidadin furucinsa domin ina jin dadin ace min ina da kyau, sai dai ban yarda na juyo ba balle har na nuna jindadin nawa.
“Ammy ba komai a nan kin cinye”
Na fada ina jin kamar na fashe da kuka domin ban samu komai a cikin kulolin ba.
“Kitchen na ce ki duba ai ba dinning ba”
Na nufi kitchen din kai tsaye, a nan na samu kayan karyawa irin na masu alfamar wani hadin ma ban taba ganin Ammy ta yi shi ba sai yau, wata kila bakonta ta shiryawa shi. Tray na dauka na zuba duk wani abun da raina yake son ko wane gefe gefe sannan na hada tea mai kauri na saka a tsakiyar tray na dauko na fito falon na nufi kofar fita.
“Zahra ina zaki je?”
“Waje zan je na ci”
Na amsata ina kallon bakon nata da ya kasa dauke ido a kaina.
“Aliyu tashi ka bata guri zata ci abinci”
“Kunyata take ji?”
Ya nuna kanshi har lokacin idon na kaina kamar zai cinye ni.
“Ta saba zaunawa ta ci abincin ta anan ba dan kunyarka ba zata fita waje ba”
Yayi murmushi ya mike tsaye yana wani irin kamshi ya nufi daya daga cikin dakunan Ammy. Zuwa na yi na zauna kusa da ita na saka tray a gabana.
“Ammy wannan waye wai ya cika kallo”
Murmushi ta yi
“Aiko kin yi sa'a ďana babu ruwanshi da kallon mata ma”
Na yatsina fuska ina kai lomar nama a bakina.
“Danki? Amman ba ke kika haife shi ba ko?”
“Ni na haife shi mana ba ki san shi ba ne, saboda ba mu dade da dawowa unguwar nan ba kuma lokacin da muka dawo yana waje gurin harkokinshi na kwallo shi ma be san wannan gidan ba wacan da ake gyara ya sani”
Na tsude hannu.
“Ammy yanzu wani gida zaku koma kenan?”
“Eh wanda muka baro ba, ana mana gyara ne za a maida shi gidan sama, idan an gama gyara, a can zamu zauna mun dawo nan ne saboda ana gyara can”
“Ammam kuma da gaske wannan ďanki ne?”
“Ban da abinki Zahra zan miki karya ne? Shi yake bin Zainab amman baya zama a nan yana zama kasashen turawa ne”
“Ikon Allah amman baki yi kama ba, Ammy ya fiki kyau”
“Eh mana saboda yana saurayi ai dole ki ce ya fini kyau”
Ta amsa ni data dariya, ashe da biyu ta yi maganar ni kuwa a bakin gaskiya nake fada.
“Ammy kenan shi ne auta?”
“Eh amman yanzu ke ce auta ba shi ba”
Na yi dariya ina kwasar garar da na tabbatar bakina ya dade be hadu da ita ba, haka na zauna na ci na koshi na yi nas na nemi leda na saka sauran sannan na hau kan kujerarta na kwanta.
“Ba a bachi akan kujera, Shiga ďaki ki kwanta”
“Dakinki?”
Na tambayar da mamaki sai ta daga min kai.