Sashe 69
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Shikenan bari na tafi, idan akwai abun da kike bukata ki yi magana da Jamila gobe za a kawo muku abinci da gas din girki”
“Har da dawainiya haka mun gode Allah ya saka da alheri”
“Ameen na yi magana da ita ne ta waya dazun sai take fada min cewar mai gidanta yace gobe za a kawo muku”
“Mijinta yana da kirki sosai”
“Yana da kirki gaskiya taimako da jin kai halinshi ne, yana da tausayi”
Haka muka yi ta yar hira har goma ta gota sannan yayi min sallama ya tafi. Ina komawa ciki na sha magani na kwanta kamar na labarta Mama abun da ya faru tsakanina da mijin Jamila sai kuma na ake ganin kamar abun be kai na bada labari ba.
[11/12, 7:44 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣6️⃣
Washe gari aka kawo mana kayan girki da kuma gas kamar yadda Dr Hamid ya fada, Mama ta jidadi sosai mutanen da suke zuwa duba gurin da muka dawo ma suna ta taya mu murna wai mun yi dace da mutanen arziki, a anan na gane ashe mutane da yawa sun san shi babban mutum ne mu dai da ba mu da alaka da shi kuma ba mu da shige shigen bin gidanjen masu arziki yasa ba mu san waye shi ba sai sunanshi, shi ma ta hanyar gidajen radio muke ji, domin ni dai ban taba ganin fuskarshi ba balle na shaidi cewar shi din ne.
Duk wanda ya zo ya ga gurin da muke zaune sai ya ta ya mu murna domin guri da mai kama da gida gashi an kawata gurin ga kuma ac da aka saka a ko wane daki.
Sai da mutane suka watse sannan mana ta dora min ruwan wanka suka tafasa sai ta ba ni tawul na saka na yi wanka da shi domin babu itacen dogon yaro a gidan da zan iya amfani da shi, duk itacen da suke Garden din gidan daga na ayaba sai na lemu sai guava da mangoro da kuma sauran kayan marmari, bayan na yi wankan ta dama min kunun kayan safa safe irin na mai jago da zai karamin ruwan nono sannan ta dora girki. Da yamma can sai ga Dr Hamid wai ya zo mu gaisa ya kara abincikar lafiyata ya auna jinina ya ce yanzu ya zama normal zan iya daina shan maganin saboda kar yayi kasa sosai ya zama wata illar, mun dan taba hira kadan sannan yayi min sallama ya tafi.
A kullum idan zan kwanta sai na bawa Amir nono da safe ma sai na shigo bangarenta na shayar da shi haka ma da rana sai dai ta tabbatar da cewar idan na samu kuzarin Amir din zai koma hannuna ne a matsayin Nanny ina kula da shi sai idan dare ya raba zan kawo shi a gurinta, ni kuma hakan yayi min dadi domin ina son na samu lokaci da yarona ina son na kebe da shi musamman ma da na lura da yana son hannuna domin komai kukan da yake idan na dauke shi zai daina.
Kwana biyu da na yi a gidan ina shayar da yaron sai ya samu lafiya yana walwala, sai dai ni kuma na rasa walwalar ta dalilin tabbatar da rasa masoyina da na yi, ina ta kokarin mantawa da shi amman na kasa each and every minute sai na tuna da Abiey, a yanzu kaunarshi ta fi azalzalata fiye da ko yaushe, wannan na saka bana iya zauna na ci abinci yadda ya kamata bana iya sakewa na yi hira da ko da Mama ne. Ranar da na muka kwana biyar a gidan Dr Hamid ya zo tare da Dr Zainab a lokacin Amir yana hannuna mun gaisa da ita ina ta jin tsoro domin kallon da take min ya wuce ka'ida kamar mai zargi haka take ta kallona, hannu ta kai ta karbi yaron daga hannuna tana mashi wasa.
“Dr yace min ya samu lafiya”
Dr Zainab ta fada tana juya shi a kafadarshi. Hajiya Jamila ta ce.
“Gaskiya ya samu lafiya, daman ko da Hubby yayi miki magana yana kan wani magani da Dr Hamid ya dora shi akai, shiyasa ya roki ki daga mashi kafa kar abun ya zama biyu”
“Na ga alama ai daman Dr ba baya ba gurin kwarewar aiki”
Ta amsa idonta na kaina.
“Sannu Zahra ya lafiyar jiki?”
“Alhamdulillah”
Na amsa kamar munafuka bana son na hada ido da ita, Hajiya Jamila ta kalleni ta kalleta.
“Daman kin santa ne?”
“Eh makotan mu a inda muka taba zama”
Ta amsa mata jikina na ba ni cewar har yanzu ni take kallo, ina dago kai muka hada ido sai na yi saurin sadda kaina kasa.
“Oh Allah sarki”
Cewar Hajiya Jamila sannan ta mika hannu ta karbi yaron. Dr Zainab ta mike tsaye still idonta na kaina.
“Toh ni zan tafi daman dai na ce zan zo na duba yaron ne saboda kar mijinki yace ban sake zuwa ba, daman dai na fada mashi cewar mu bada kwana biyu mu ga idan yaron be samu sauki ba sai a fara mashi wasu gwaje gwaje”
“Aa ya samu sauki sosai Wallahi mun gode”
Hajiya Jamila ta fada da sauri, Dr Zainab ta sake kallona ta ce.
“Kin dawo da zama a nan ne Zahra?”
“Eh muna tare da Mama”
“Okay”
Daga haka bata sake ce min komai ba har ta fice daga gidan, harabar gidan Dr Hamid ya rakata ya dawo falon ya same ni tare da Hajiya Jamila.
“Thank you Zahra”
Ya fada min yana kallona Hajiya Jamila dai bata ce komai ba sai tashi ta yi tare da ďanta ta nufi hanyar dakinta. Sai da ta shige sannan Dr Hamid ya kalleni
“Zahra matar nan yayar Abiey ce right”
“Ka san Abiey ne?”
“Not much, amman labarin abun da ya faru ya karade ko'ina kuma na san cewa Abiey dan'uwan Dr Zainab ne”
“Mutane sun rubuta Labarai marar dadi da yawa akan mu”
“Musamman ke abun zai fi effecting dinki sama da shi, duk dai ban san alakarku ba amman ina kallon kamar ya yaudareki ne ko? Guy nan is very arrogant ya cika jin kanshi and kin san cele din nan ba su da tausayi da damuwa da kowa sai kansu wannan yasa be taba burge ni ba”
Na yi murmushi ina sauke kaina kasa na saka hannu daya cikin dayan.
“Abiey ba haka yake ba, mutum ne mai sauki ga ga wanda ya fahimce shi, kuma be yaudare ni ba kawai dai kaddararmu ce a haka”
“Maybe dai yana kusa da zuciyarki ne sosai shiyasa kike fadar haka ba zaki gane abun da nake nufi ba”
“Ba ka yi karya ba Abiey yana kusa da zuciyata sosai irin kusancin da idan zan numfasa sai na tuna shi ina kwana da shi a raina na tashi da shi”
“Amman Zahra kun yi soyayya a tsakaninku ne a can baya? If i may ask”
A take na ji idona ya cika da hawaye, na mike tsaye da sauri.
“Bari na tafi ko akwai abun da zan rikawa Mama”
“Okay”
Ya nuna min kofa sai muka tako a tare muka fito haka ya rokoni har gurin BQ na shiga sannan ya koma. Ana sukowa daga sallama magariba mai gadin gidan ya sallama mana a BQ wai ana sallama da ni a waje, gabana na fadi sosai Mama ma ta yi mamakin domin ba mu san wani da zai iya zuwa ya sallama min a wannan lokacin ba.
“Toh ko dai Abiey ne?”
Mama ta fada a take na ji zuciyata ta yi wani zillo kamar ta bar jikina ta tafi ta gana da masoyinta.
“Ya fada maka ko waye shi?”
Na tambayi mai gadin gidan.
“Aa be fada ba”
“Dan Allah ya kamaninshi suke?”
“Fari ne haka dogo yana cikin mota, ya ce ya mana kin san da zuwanshi”
“Ka ce ga ni nan zuwa”
Ya juya ya fita ni kuma na cire hijab din jikina na dauki wani na saka na tambayi izninin Mama.
“Tafi wata kila wata maganar zai fada miki”
Na saka talkamina na fito ina jin kafafuwana na min nauyi, ina fitowa sai na same mota harabar gidan an faka, kai tsaye na nufi gurin kamin na isa aka bude motar ga mamaki Sauban ne fuskarshi da murmushi kamar an masa bushara.
“Ki ce gidan na ku haka yake da tsaro sai an bincike mutum tsab sannan ake bari ya shigo cikin gidan, ba dan ina son ganin ki i swear da fasawa zan yi”
Na yi murmushin da ya same min na dole ina mamakin zuwanshi gidan, ko da yake ba abun mamaki ba ne domin Dr Zainab ta zo dazun ta same ni a gidan wata kila ta hanyarta ya samu labarin cewar ina zaune a nan, sai dai kuma me ya kawo shi gurina? Kamar ya san amsar tambayar nake nema sai ya ce.
“Na san zaki yi mamaki abun da ya kawo ni ko? Na zo na kara duba lafiyar ki ne, kin bar asibiti ba tare da kin sanar min ba, i hope ba laifin abokina ya shafe ni ba”
Na girgiza mashi kai.
“Ko kadan mu ma sallmar ta zo mana an a bazata”
“Amman duk da haka ai ya kamata ki sanar min ko a waya ne, na yi ta yawom zuwa asibitin nan kuma kin san dan iskan likitan nan ya hanani ganinki yace be san inda kike ba, number Mama kuma idan an kira bata shiga, ina ta nemanki amman ban samu ba na sha wahala sosai fa, sai dazun Dr Zainab ta fada min inda zan same ki domin ita ma na yi ta bincikar tace min bata san inda kike ba”
“Ba ni da waya yanzu”
“A nan kike zaune?”
Ya bukaci sani yana karewa BQ din kallo.
“Eh tare da Mama”
“Allah sarki ki min magana da ita mu gaisa”
“Da Mama?”
“Eh ko akwai matsala ne?”
Na girgiza kai alamar aa na juya sai ya kira ni.
“Zahra”
Na juyo bude motar yayi ya dauko kwalin sabuwar wayar da sabon line ya dora min saman wayar.