← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 127

Sashe 19

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Makota da yan'uwa suna ta zuwa yi mana gaisuwa, Mama ta saka dankwali ta daure min cikina daman can ta tanadar min da wasu abubuwan da zan bukata a jego. A aka dora ruwan zafi da sunan na yi wanka Hajiya ta siyo min nama ta dafa min a gidan Mama saboda na ki cin komai, bana aikin komai sai kuka tun ana bani hakuri har aka hakura aka saka min ido.
Ina zaune daki bayan na fito daga wanka Mama ta balla maganin da likita yace a bani ta miko min.

“Karbi ki sha”

“Ni bana son wannan maganin”

“Shi zai taimaka miki ya tsayar miki da zubar nonon”

“Ni bana so ni ki kyale, ba zan sha ba”

“Aiko kara ki sha zai taimaka miki, idan ba haka ba nonon zai dade yana miki ruwa kuma sai ta yi miki ciwo, tun da ba wani zai tsosa miki ba Allah ya riga da yayi ikonsa”

Hajiya ta fada.

“Ni Wallahi mai rai na haifa”

Na fada ina hawaye sai Mama da daka min tsawa da sai da jikina ya dauki rawa.

“Wallahi Zahra idan bakinki ya sake furta magana nan sai na bata miki rai fiye da yadda kike zato, ke kika fi kowa rashin yarda da kaddara ne? Ko kin taba ganin an yi ma Allah haka? Wawuyar banza kawai”

A take na fashe da wani irin kuka da sai da Hajiya ta rika ni ta zaunar.

“Duk yadda kike ji ba ki kai ni Zahra, kin gan ni nan haihuwata goma sha daya amman biyu kawai Allah ya bar min ya karbi sauran, Allah kadai ya san yadda na so ganin ďan Deen ko ba komai zan ji sanyi amman babu yadda zamu yi da ikon Allah, ki yi hakuri kinji”

Hawaye ya sauko mata, sai na kwantar da kaina jikinta ina kuka Mama kuma ta watsar da maganin ta tashi ta fice ta bar mana ďakin.

“Indai ba zata iya hakurin zama da ke ba, sai na maidaki gurina har ki gama wanka abun kadan sai ta rufe ki da fada”

Na kara fashewa da kukan tausayin kaina da kuma ita a lokaci daya. The following day Hajiya ta koma gidanta, aka bar ni daga ni sai Mama sai kuma Yaya Maryam dake zuwa ta wuni ta koma, ita take ta ba ni magana tana kwantar min da hankali amman ina na kasa samu kwanciyar hankali ďana kawai nake gani sai na kara ramewa daman bana wani iya cin abincin kirki, babu ranar da bana kuka haka babu daren da zai zo ya wuce ban yi kewar mijina ba, sai abun ya zame min biyu na rasa inda zan ji sanyi, na koma kamar wanda bata da kowa a duniyar nan.

“Allah kadai ya san wane hali yake ciki, ko sun saka masa sunan ko kuma wani za su saka”

A zatona a cikin raina na yi maganar ashe a fili na yi, sai jin na yi Mama ta amsa min.

“Sunan da suka ga dama mana shi za su saka masa, ki cire ranki a tunanin yaron nan dan Allah Zahra ni kaina ina cikin damuwa kara daga min hankali kike”

“Mama yanzu idan aka ce wata uwa ta dauke miki ni ko Yaya Maryam ya zaki ji?”

Ta dago daga gyara wutar da take ta kalleni sai ta sauke ajiyar zuciya.

“Mutuwa kadai ke iya raba ďa da uwa, kuma abun da kika aikata kamar mutuwa yake, idan baki daina tunani ba za ki iya jawa kanki wata matsala”

“Babu abun da nake so a yanzu Mama sai mutuwa, domin ita ladai ce mafita a gare ni, idan na mutu zan manta da komai ciki har da kuskuren da na aikata”

Tasowa ta yi ta dawo kusa da ni ta zauna.

“Kin ga duk rayuwar nan da kika ganin kina cikin tsanani? Wani na can yafi ki shiga matsala, da za a baki irin kaddararki da sai ji sanyi, ke ma na ki zai zama tarihi kamar ba ayi ba”

“Haka dai kika ganin kamar zai wuce Mama amman ba zai taba wuce ba, na rasa Deen kenan har a bada kuma ga ďana”

Kama kaina ta yi ta kwantar saman kafadarta.

“Zai wuce Zahra komai zai zama labari”

“Mama”

Na kira sunanta a hankali sai ta amsa min.

“Na'am”

“Ina son zan je na yi magana da Dr Hamid”

“Maganar me? Idan zai yiyu na maida masa da kudinsa na karbo babyna”

Dago ni ta yi daga kafadarta ta kalleni.

“Ina zaki samu kudi mai yawa haka?”

Na yi shiru sai kuma na fada mata abun da nake ganin shi ne mafita.

“Wata kila Abiey zai taimaka min ko?”

“Uhmmm yaro man kaza, yar dawowar da yayarsa ta yi tana nuna miki kulawa ta karya har kin fara yarda da ita? Kin manta duk abun sa suka miki suka mana?”

“Mama ni yanzu mafita nake nema”

“Kuma kina da tabbacin Abiey zai sama miki ita? Waya sani ma ko yayi aure wata kila ba baya kasar, ko da ace yana nan ke yanzu har zaki iya tunkararsa da wata magana ta neman taimako? Bayan ya gama watsa miki kasa a ido? Sai ya dauki kudi mai yawa haka ya biya miki bukatarki saboda farincikin da ya kasa sama miki shi a can baya? Ki kaddarar ma ya baki kudin a ganinki ita matar zata yarda ta baki ďanki? Ta cewa mijinta da yan'uwanta me? Ai ba zata kyale ki ba, kuma kin ga bamu san Wacece ita ba, macen da zata bada miliyan bakwai da wani abu a take kuma ta saka miki diyar miliyan ashirin idan kin karya alkawari ai kin san ba karamar mace ba ce, shi kan shi mijinta babban mutun ne shiyasa har take son haihu da shi, sannan idan maganar nan ta fita har ta kaiku kotu to ke da ita duk sai an hukuntaku”

“Toh Mama zan yi magana da shi ya taimaka min na sake ganin yaro ko da sau daya ne”

Ashe na yi sara akan gaba domin kuwa ina rufe baki, kiran Dr Hamid ya shigo wayar Mama da na saka line ne, jiki na rawa na dauka.

“Hello”

“Zahra ya kike”

“Alhamdulillah”

“Ya kamata na kira na tambayi lafiyarki ko na zo, sai dai na daga miki kafa ne saboda ki samu relief kar ganina ya sa ki rika tunani, ya karfin jikin na ki”

“Na gode Allah”

“Maa Shaa Allah akwai abun da kike bukata ne?”

“Eh ina son magana da kai”

“Okay ina saurarenki”

“Ba a waya ba, a fili maganar mai muhimmanci ce”

“Allah yasa ba akan yaron nan ba?”

“Aa akan lafiyata ne, akwai yan matsalolin da nake ji ina son na ganka face to face”

“Ba zai yiyu na zo gidanku a yanzu ba, amman ke zaki iya yin dabara ki same ni a asibiti sai mu yi magana”

“Da yaushe zan same ka?”

“Kin ga ai ga waya sai ki kira ni kamin ki zo”

“Zan iya zuwa yanzu?”

Yayi shiru kamar ba zai amsa ni ba har sai da na dauka kiran ya yanke ne.

“Hello”

“Ke da wa zaki zo?”

“Ni kadai”

“Ki same ni a Favor Hospital, asibitin da kika haihu, idan kin zo sai ki kira ni”

“Toh”

Na amsa da sauri sannan na share hawayena na sauke wayar na mike tsaye da sauri.

“Mama zan je na yi magama da shi zan roke shi ya bar ni na ga ďana”

“Zahra wa kika taba ganin tana jego ta fita? Jegon ma haihuwar fari?”

“Maman zan fita da sunan zuwa asibiti ne, dan Allah karki hana ni ina son na ga little Deen ne, wata kila shi na dama ta karshe da na ke da ita ta ganinsa”

Hawayen da suka sauko min kadai sun isa su saka Mama ta tausayawa min balle kuma har na hada da magiya.

“To bari na tashi mu tafi tare”

“Aa idan ya gan ni da wani ba zai yarda ba, ki bar ni na tafi ni kadai”

Daga bakina da nake magana da shi har jikina rawa yake, kana ganina kasan ina cikin yunwar son ganin ďana.

“Toh Allah ya tsare”

“Ameen”

Na shiga daki da sauri na dauki hijabi na saka na fito rike da yan canji a hannu na hawan napep na nufi kofar fita ina kokarin ficewa ba tare da na ce da Mama na tafi ba, sai ta yi saurin rikoni.

“Zahra kina cikin hayyacinki kuwa? Haka zaki fita kafarki babu talkami? Kuma da wace waya zaki kira shi? ”

Sai a lokacin na kalli kafata ashe ban saka talkami ba, kuma ban dauki wayar kiransa. Mama da kanta ta dauko min talkamin sannan ta mika min wayar, na saka talkamin na karbi wayar na fice ina jin kamar na runtse ido ya bude na gan ni a aibitin gaban Dr Hamid.

ABIEY POV.

“Mai Martaba zai ga rashin kyautawarka fa, ya kamata ka je ka yi masa godiya”

Anty ta fada sai ya dago daga barin kallon agogon hannunsa na miliyan hudu ya kalleta.

“Godiya kuma?”

“Yes ko da ace ya saba yi maka ya kamata ka gode masa balle kuma yayi maka abun da be taba ba, kuma ya tsaya tsayin daka har sai da aka baka Yasmin”

Ya busar da iskar bakinsa.

“Yarinyar ina ganinta kamar Allah ashe tantiriya ce, tun lokacin da abun nan ya faru ta ki yarda mu yi magana da ita face to face, first day na je gidansu ta ki fitowa, na sake zuwa aka ce tana Islamiya na tafi har islamiyarsu amman yarinyar nan bata fito ba”

Anty ta yi murmushi.

“Yasmin fa sonka take, shiyasa ta amsa a lokacin da aka tambaye ta”

Kamar wanda aka tunawa da wani abu sai ya mike tsaye da sauri.

“Bari na yi tafi gidan Momy”

“Gurin me?”

“I need to talk to her”

“Toh Allah yasa ta baka hadin kai, idan ba haka ba kam zata jefaka a matsala, ka san dai ba zaka fara zuwa ka fadawa Mai Maetaba cewar baka sonta ba, kuma idan ba daga gareta aka ji wata matsalar ba Mai Martaba ba zai taba magana biyu ba”
Chapter 19 · 0% Book details