← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 127

Sashe 105

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da ta share hawayenta ta sake kama hannayena ta rike sannan ta ce.

“Zahra karki taba yarda ki mu'amalanci wani da aurenki, kara ki yi shi a waje ko kuma bayan mutuwar aure ba a aure ba, maza basa yafe irin wannan kuma basa mantawa, kuma wannan abun yana shafar yayan da mace zata haifa, ni da Momy wato abokiyar zamana a gidan mahaifin Zainab mun sake aure bayan rasuwar mijinmu, sai dai ni na rigata auren saboda na fita kurciya da kyau, kuma ni na yi sa'ar aurene saboda tsohon manemina ne na aura, ya nuna min so irin wanda Aliyu yake kokarin nuna miki a yanzu, har ta kai baya iya adalci a tsakanina da sauran matansa, wannan ya haddasa fitina kuma zazzafan kishin da ya saka sai da aka ware ni dabam, domin ni ina yaki da bakina ne da anyi min sai na yi magana bana shiru, amman Wallahi ban san hanyar zuwa gidan ko wane boka ba, a lokacin kuma sai hankalinsu ya kara tashi suna ganin kamar zan kara dauke masa hankali ne, sanadin haka sai suka shiga bin bokaye suna kokarin raba ni da mijina, sai kuma suka yi nasara Mai Martaba ya juya min baya irin Juyowar da idan na rabe shi sai ya rika jin warina, idan ya taba ni sai yace jin yake kamar ya taba itace, har tambayar yake miya samu jikinki haka ni kuma ban san miye ba, da abun ya fara yawa sai ya daina zuwa gidana sai dai aiko min da duk wani abun bukata da kuma sakon gaisuwa, bayan ya kaurace min sai na fahimci ina da cikin Aliyu, wanda yace min idan na haife shi sunan mahaifinsa za a saka masa duk kuwa da kasancewar ya hana ko wace mace saka sunan Abban sa amman ni soyayya ta saka ya karya wannan alkawarin da ya dauka. Wata rana kamar an turo shi sai ya shigo gidan fuska babu annuri ban masa laifin komai ba,a nan na samu damar sanar masa halin da nake cikin ina ganin kamar samun cikin zai kawar da komai a tsakaninmu ya dawo da zaman lafiyarmu, sai dai a lokacin da na sanar da shi ina dauke da cikin sai ya kasa farinciki a aka danna jindadinsa akan cikin ya gagara nuna min murnarsa, sai Allah ya raba lafiya kawai yace min, a ranar na yi kukan na yi bakinciki sosai, a dayan bangaren kuma na yi farinciki da kyautar da Allah yayi mine. Na yi bakinciki na kaurace min da yayi ya saka na shiga damuwa sosai har ta kai kanensa da suke uba daya wato Galadima wanda shi kadai yake so na a familyn ya fahimci haka, maganinsu ba tsaya a iya farraku tsakanina da Mai Martaba ba ni ma ya taba tafiyata ya shafi kwakwalwata ya kai bana iya tsayawa na natsu akan wasu abubuwa, ga ciwon kafafuwan da na yi ta neman magani har india na je na kasa samun lafiya. A cikin Aliyu na wata na biyar zuciya da sheirin shaidan suka debe ni suka na aikata masha'a tare da kanensa da zan iya cewa cilasta ni yayi domin yayi ta lallashina har na amince, ashe ban sani ba wani karin damuwa ce ta fuskanto ni, domin muna a cikin halin da be kamata ba Mai Martaba ya shigo cikin gidan sai dai be shiga inda muke ba sai ya zauna a falo, bayan mun fito muka same shi. Daga ni har kanensa mutuwa ce kawai ba mu yi ba, amman mun sha kuka na fitar hankali. Ya saka muka yi masa alkawarin babu wanda zai ji wannan maganar daga ni sai shi sai Allah, saboda idan maganar ta fita zai zama abun magana kuma abun kunya. Bayan kanenshi ya fita sai ya tambaye ni tsawon yaushe muke tare, na fada masa gaskiya cewar yau ne kawai, amman be yarda ba.

“Cikinki da ke jikinki zai cigaba da zama a matsayin ďana ko da kuwa ba nawa ba ne, domin jinin ďan'uwana jinina ne, kuma babu wanda zai san da wannan maganar, sannan ina son ki sani na sauwake miki ma'ana na sake ki”

Cikin tashin hankali na fara bashi hakuri ina kuka ina fada masa cewar cikin dake jikina nasa ne.

“Idan har zan iya zaman aure da uwar da ta haife ni, to zan sake zaman aure da ke Umaima!”

Furuncin da yayi kenan ya banranta kansa da ni, daga lokacin sai na dawo gida gurin iyeyena na zauna, damuwa ta shiga kaina ga kuma sihirin da suka min har ya zama na ina yin abu kamar marar hankali, ana ta nema min magani ana min addu'a cikin iyawar Allah na samu sauki. Sai Allah ya dauki kaunar Aliyu ya saka min tun yana ciki domin mahaifinsa be taba zuwa duba lafiyata ba bayan ya sake ni, mutane suna ta fadar cewar maganin da suka min ne ya saka ya sake ni kuma ya dauke idona a kaina domin ina fadawa kowa cewar haka nan sidda ya sake ni ba tare da na masa komai ba.
Kamin na haifi Aliyu kanen mahaifinsa yayi hatsarin mota ya rasu, sai ya zamana ni kadai na rayu da wannan bakincikin har zuwa yau. Bayan na haifi Aliyu Mai Martaba be taba ganin fuskarsa ba be taba aiko masa da komai ba, be taba yi masa komai ba ďana ya girma hannuna yayi wayo na yi masa komai da uwa take yi ma ďanta, sai dai kowa ya kalli Aliyu ya san ďan Mai Martaba ne domin babu inda ya rago Mai Martaba a kamanin. A lokacin da Momy ta haifi Yasmin sai muka je barka daga gidanta na dauki ďana na kai shi gidan Mai Martaba, yana kallonsa sai hawaye suka zubo masa, domin be taba saka shi a ido ba sai a ranar. Sai dai haka be canja tsanar da yake masa ba, be saka ya kula da shi ba, ni kuma ban fasa nunawa ďana shi ne ubansa ba saboda shi ne ubansa din na gaskiya, a kokarinsa na mantawa da ni ya auro mahaifiyarsu Aisha da Narjis, ita kuma ta zo sai ta zama mace mai sanyin hali da son gaskiya, tana ta kokarin sada Aliyu da mahaifinsa sanadin haka har aurenta ya taba mutuwa daga baya aka dawo da ita, amman bata fasa abun da take ba har ta yi nasarar samawa Aliyu ďaki a bangarenta ya zamana shi ma zai shiga yayi yadda yake so kamar ďan gidan, tun daga lokacin nake matukar kaunar Aliyu kuma nake tausayinsa domin laifina ne ya shafe shi, wata kila har da maganin da abokan zamana suka yi na shiga tsakakaninshi da mahaifinsa amman wannan abun da na aikata shi ma ya shafe shi, ya shafa masa bakin fenti da idan Mai Martaba ya kalleshi yana tuna abin da ya faru. Da iyayena suka rasu aka raba gidan mu sai na dawo a wannan gidan da tsohon mijina ya bar mine wato na ci gado, na cigaba da kula da kaina da yayana. Kuma Allah ya taimake ni yayana suka samu tarbiya da suka gama karatu na suka samu aiki, Aliyu kuma ya karkara a bangaren kwallon kafa domin abun da ya fi so kenan ni kuma na goya masa baya”
[11/29, 11:47 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣5️⃣

“Rashin samun kula daga mahaifi yana matukar tayarwa Aliyu hankali yana damunsa sosai, har yan'uwansa suke son yi masa gori da haka, wata rana da kaina na aka shi a mota na shiga dashi har cikin fadar na zaunar da shi a gaban matan Mai Martaba da yayansa na ce ya fadawa Aliyu da duniyar cewar ba shi ya haifi Aliyu ba, sai ya girgiza kai yace Aliyu ďansa ne ko be fada ba kowa ya kalli fuskarsa zai san da haka, yace Aliyu jininsa ne, a gaban matansa yace Zainab ma da ba yata ba ina sonta kamar yata Umaima saboda ta fito daga cikinki balle Abiey da yake jinina.
Daga lokacin sai ya samu kwanciyar hankali, nima na dan samu amman na gagara mantawa, sai dai samun ki da Aliyu yayi, na ga farinciki a tare da shi irin wanda ban taba gani ba, kuma kin kawarda tunaninsa kin dauke hankalinsa daga damuwar da mahaifinsa ya saka masa, neman aurenki ma da aka je sai kanensa ne da yan'uwa suka je, amman shi be ce komai ba”

A rayuwata ban taba jin tausayin wani mutun kamar yadda zuciyata take tausayin Ammy a yanzu ba, daker na iya takaita kukana na share hawayena na ce.

“Ammy babu wanda baya kuskure, kuma abun da kika aikata Allah ya kaddara sai kin aikata haka din saboda haka ba ki isa ki tsallake haka din ba, ki saka a ranki komai be faru ba, kuma na miki alkawari ba zan taba gudun Abiey ba”

Rumgume ni ta yi tana dariya tare da kuka a lokaci daya tana saka min albarka. Muna cikin wannan halin Abiey ya shigo dakin ya same mu a lokacin da har mun dauko wata hirar ta duniya, sai dai ina jikin Ammy ne idanuwana da nata sum kumbura.

“Me kuke yi ma kuka”
Chapter 105 · 0% Book details