Sashe 16
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata jira ta ji amsa da zata fito daga bakina ba ta kashe wayar, ni kuwa na tashi zaune ina mamakin karfi hali da karfin duniyar da ya rufe mata ido take fada min magana son ranta, rushewar wani abu na ji kamar gini hakan yasa na tashi da sauri na fito ashe zan iya gudu da tsohon cikin idan wani abu ya same ni, domin a tunanin wani bangare na ginin gidan mu ne ya fadi. Ko da na fito na tararda Mama har ta kai waje gurin kallo ni ma lekowa na yi sai na ga ba mu kadai ba har da makotanmu sun fito kallo, wani kangon gida ne dake kusa facing din gidanmu aka rushe da motar rushe gidaje.
“Abun ba ko sanarwa ni Wallahi na tsorata”
Wata makociyar su Mama ta fada kowa sai ya dora da na shi, ni dai ban ce komai ba na juyo na dawo cikin gidan na zauna tunanin gobena.
ABIEY POV.
Dr na barin gidan ta kira shi ta fada masa hakin da ta samu Zahra.
“Amman ke a fahimtarki me yake damunta?”
“Wallahi ban fahimci komai ba, kuma na yi tambayarta bata fada min ba, sai dai kasan duk abun da zai saka Mamarta ta yi fushi da ita ba karamin abu ba ne”
“Gashi bata da wata kawa ta kusa balle na bincika ko zan sani”
“Abiey ka bi komai a hankali”
“Shikenan, Thank you so much Dr Zainab kin min abun alheri da ba zan manta ba na gode da kila kula min da Zahra”
“Anything for you”
Ta fada fuskarta da murmushi sannan ya kashe wayar, ya mike tsaye ya nufi windows dakinta yana kallon backyard.
“I wish na san minene matsalarki Zahra”
Ya furta yana murza yastun hannunsa. The following day ya tafi gidansu Momy domin yin magana da Yasmin ko da yaje ya samu tana makarantar Islamiya haka ya zauna ya sha hira da Momy kamin ta dawo, abun da ya dade be yi ba ita kanta Momy ta lura da yadda Abiey yake cikin farinciki a yau sai dai bata tambaye shi komai ba, domin aganinta ba huruminta ba ne, har 6pm yana zaman jiranta Yasmin bata dawo ba sai 8pm kasancewar weekend ne ranar assabar da lahadi suna hadda har 8 na dare suke kaiwa wani lokacin.
“Amman dai maganar da zaka yi da Yasmin tana da muhimmanci sosai ko?”
Momy ta tambaya ganin yadda ya bata lokacin tun 2pm yana jiranta har 8pm, da wani abun ne dabam sai dai yace zai je ya dawo ko kuma yayi waya da ita, amman ya tsaya sai yayi magana da ita face to face, shi dai be ce ma Momy komai ba bayan murmushin da yayi. Yana kishingida jikin kujerar falon Yasmin ta shigo da katon hijab dinta hannunta rike da jakarta ta makaranta, tashi yayi zaune yana kallonta suna hada ido sai ya sakar mata murmushinsa mai kyau ita ma murmushin ta yi masa sai dai ganin Momy yasa ta yi saurin gusar da murnushin ta karaso cikin falon da sallama.
[10/6, 8:31 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣1️⃣
“Barka da dare”
“Welcome”
Ya amsa mata a takaice, sannan ta kalli Momy ta gaishe ta.
“Barka dai yan makaranta an dawo, tun dazun Abiey ke jiranki”
“Ni”
Ta nuna kanta, sai Momy ta tashi zaune tana fadin.
“Ke fa”
“Momy bari ta ci abinci tukuna”
“No ai kara dai ta saurareka yanzu daga baya sai ta ci abinci bari na baku guri”
Sai da Momy ta shige dakinta sannan Yasmin ta zauna a inda Momy ta tashi tana kallon Abiey.
“Allah yasa ba laifi na yi ba”
Yayi murmushi domin ya kura tsorone a tare da ita.
“Ba ki yi laifi komai ba, wani taimako nake son ki yi min”
“Taimako kuma na minene?”
“Zaki min idan na fada”
“Zan iya maka abun”
“Zaki iya”
“Ka fadi ko minene babu wani abu da zaka nema daga gareni da zan kasa yi maka shi matukar ina da iko”
Yayi murmushi.
“Thank you, uhm shekaranjiya ne..... ”
Tun da ya soma bata labarin bata ji komai ba har sai da ya kawo gabar da ya ambaci sunanta, sai ta ja wani irin numfashi da karfi shi kansa sai da ya ji.
“No you don't have to worry, kawai na yi haka ne saboda na samu mafita daga gurin Mai Martaba, da kuma Mama Lami idan ban yi haka ba za su iya zaba min wanda bana ra'ayi”
“To miyasa ka ce ni?”
“That's the point, na san Mai Martaba zai aiko a tambaya masa aurena gurinki da su Momy idan ya gama bimciken da zai yi, idan an zo ina son ki amsa musu cewar ke baki so na kina da wanda kike so, already na yi magana da Ammy ta sani na san kuma zata sanarwa Momy shiyasa ban mata maganar ba”
Yawu ta hade a hankali gabanta yayi mugun faduwa, ta kasa dauke ido daga barin kallonsa.
“Yasmin...”
Ya kira sunanta sannan ta sauke idonta kasa tana jin wani zafi na taso mata.
“Can you”
Ta sake kallonsa irin duban da ita kanta bata san tana masa shi ba, sai kuma ta yi saurin maida kanta kasa.
“Yes”
Ta amsa sai ta tashi da sauri ta bar shi a falon zaune, binta yayi da kallon mamaki da shakkun yadda ta yi masa.
“Is she okay?”
Ya tambayi kansa, sai kuma ya ta tabe baki ya mike tsaye yana kiran Momy.
“Ba dai har kun gama ba”
Shi ne abun da Momy ta fito tana fada.
“Eh daman magana ce zan yi da ita ba mai tsawo ba zan wuce sai da safe”
“Toh Allah ya bamu alheri ka gaishe da su Ammy”
“Za su ji”
Ya fice daga falon kuzarinsa, Momy ta bi shi da kallon kamin ta juya zuwa dakin Yasmin.
Bayan ya dawo gida yake fadawa Ammy yadda suka yi, sannan ya kira Sauban ya labarta masa abubuwan da suka faru kusan ya fi kowa farincikin da jin abun da Mai Martaba yayi ma abokinsa.
“Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba in ji hausawa, amman kana ganin Yasmin zata maka haka?”
“To zai hana? Ba abu ne mai wahala ba, ya maganar gidan? Ina son na zauna kusa da Zahra ko dan na rika sanin halin da take ciki”
“Ana nan ana bincikawa yawancin wadanda ake samu bana kusa da gidansu ba ne, amman akwai wani gida da aka fara gini aka bari shi kuma be da girma sosai gaskia”
“Idan zai yiyu a siye na kusa da shi mana sai a hada in ya so sai a ninka musu, idan kuma haka be samu ba sai a siye shi nan ayi gidan sama”
“Amman kai kana ganin zaka iya zama a nan Zahra bata gane ka”
“Ba zan taba bari ka gane, i just want to be close to her”
“Shikenan zan bincika mana, Allah yasa Mai Martaba ya barka ka aureta kar wata matsala ta ta so kuma”
“No no kar ma kasa wannan a ranka, kar zuciyarka ta sake raya maka zan rasa Zahra”
“Ba fata nake ba, kawai ina sasashe ne”
“To ka daina wannan hasashen”
Ya sauke wayarsa cike da rashin jindadin kalamin da Sauban yayi.
ZAHRA POV.
TWO WEEKS LATER...
Wani irin murdawa na ji marata na yi ta saba min haka sai dai ba irin na yau ba yau kan ta tsananta min sosai, kusan jin nake kamar bayana zai balle gabana kuma kamar zai zazzago kasa ya cire gaba daya, a wahala na rarrafo zan fito saboda fitsarin da nake ji sai Mama ta rike ni.
“Ina zaki?”
“Fitsari zan yi”
“Aa ba a hawan shadda (Masai) idan ana nakuda balle gashi har kin fara zubar da jini, ki yi fitsarin a nan zan gyara”
Tana gama fadar hakan ta tashi ta cire ledar tsakar dakin ta maida gefe daya ta dauko wani katon tsohon zane ta shimfida.
“Yi fitsarin ki dawo nan ki zauna”
Na saki fitsarin a nan Mama ta dauko ruwa zata min tsarko na rike da sauri na karba na yi tsarkina ina ta karewa kar Mama ta gan ni, da taimakonta na isa gurin da ta shimfida min zanen na kwanta, sai tace na tashi zaune na bude kafafuwana.
“Aa ni ba zan bude kafafuwan ba haba Mama ai da kunya?”
“Kunya? Ni na haife ki fa? Kuma ranar haihu mace har tana jin kunya ne? Ai sai daga baya dai ko?”
“Ni dai gaskiya ba zan iya ba, ni tafi dakinki zan haihu da kaina”
Murmushi ta yi.
“Ai ko da sauran nakuda bata taso miki gaba daya ba shiyasa har kika da bakin fadin haka”
Haka ne kuwa duk wani rufe kafafuwa da nake ina jin kunyar Mama na farko farko ne ina jin azabar ta asali ban san lokacin da na walgare kafafuwan ba na kwala ihu.
“Mama ciwo nake ji na shiga uku”
Na fada ina jin wani irin azaba da ban san yadda zan kwatanta ba, a take na ji fitsarin sun kara taruwa a marata.
“fitsari nake ji”
“Ki yi su a nan, kuma ki rika ambaton Allah”
Na yi yunkurin fitsarin sai na ji sun ki fitowa ashe ba fitsari ba ne tsabar azabar ciwo ne, na kai hannu na cire dankwalin kaina saboda wani zafi da nake jin ya baibaiye jikina, na kai hannu na fara tsife kitson dake kaina can kuma na mari cinyata.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Mama mutuwa zan yi, mama ku cire min abun nan Mama ki kira likita Mama ki kira shi ki fada masa ina nan ina shan azaba wayyo Allah”
“Ki bari sai idan kin haihu sai a kira shi”
“Ba zan bari ba ba zan bari ba, ai ba jikinki ba ne baki san yadda nake ji ba, cikina fashewa zai yi marata ciwo take kasana ma barkewa zai yi, wayyo Allah marata”
Murmushi kawai Mama ta yi ta cigaba da tufa min addu'a a kofi bayan ta gama ta ba ni na sha, ta shafa min ragowar a cikina.
“Allah ya sauke ki lafiya, ki yi ta ambaton Allah”
“To wai ba addu'a kika ga ina yi ba, ni dai ki kira likita wayyo Babana”