Sashe 43
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya na sauke Yaya Maryam kuma ta kalleni ta dauke kai ba dan bata da abun fada ba, sai dan na san ita din mai jin maganar Mama ce ba kamar ni ba. Tafiyar Hajiya da kamar awa biyu sai ga Baba ya shigo fuska babu annuri har wani bude hanci yake yana hararata kamar ya dake ni, sannu da zuwa da muka masa ni da Yaya Maryam ma be amsa ba, Mama ta tashi ta karbi yar jakar hannunsa sai ya nufi kofar daki kamar zai shiga sai kuma ya juyo ya kalleni.
“Ke ashe Zahra baki da mutunci?”
A take gabana ya yanke ya fadi, Yaya Maryam ta kalleshi kamar yadda ni ma nake kallonshi.
“Tun da mahaifinku ya fadi ya mutu waya zame muku gata bayan ni, waya kula da ku cikin abokan Aminu bayan ni? Amman yau ace zaki kalli Idon Hajiya Balkisu ki zagi ďanta tass, saboda abun da be taka kara ya karya ba? ďana ba shi a duniya amman ki kalli idon mahaifiyarsa ki ci mutunshi?”
Mama ta fito daga dakin rike da jakar ta tsaya bakin kofar tana kallon yadda Baba ke tayar da jijiyar wuya.
“Babba be taba zama kamar Karami ba Malam da dai ka zauna ka huta sai na koro maka bayanin abun da ya faru”
“Bayanin me zaki koro min? Lokacin da take aibata ďana ya kamata ki saka baki yi magana ba yanzu ba, daman ai duk lalacewar da Zahra ta yi ke ce sanadi yarinyar nan tun tana karama baki san ki mata fada ba ko kuma ki hana ta aikata abu, haka ta tashi bata jin maganar kowa”
Yaya Maryam ta mike tsaye jikinta har rawa yake.
“Baba kai uba ne a garemu, ko da ace ba ka auri mahaifiyarmu ba ka cancanci girmamawa a garemu, saboda ka zauna da mahaifinmu kuma kasan ciki da wajensa, balle kuma ace kana auren Mama, wata kila Hajiya bata fada maka yadda zaka fahimta ba”
Ya nuna Yaya Maryam da yatsanshi hannunshi har rawa yake kamar mazari.
“Ke kama bakinki, yau nake zaune tare da Hajiya da zata fada min karya? A can da bata fada min ba sai yanzu? ”
Yaya Maryam zata sake magana Mama ta daga mata hannu.
“Ban koya miki wannan tarbiyar ba, ko dukana kika ga yana yi ban ce ki saka hannu ki tare ba, saka talkaminki dauki mayafinki ki tafi gidan mijinki ina gaishe da yara”
“Toh Mama”
Ta amsa a ladabce sannan ta nufi dakin Mama ta dauko mayafinta ta saka da jakarta ta saka talkaminta ta nufi kofa, binta na yi da kallo har ta fice sannan na juyo na kalleshi.
“Idan har zaka yi adalci karka ga laifina Baba, idan kuma ta kama dole sai ka gani to ka kalli abun ta fuska biyu ta bangarena da kuma bangaren Deen”
Da hannu ya watsar da ni yana wani yatsina hanci, cikin tsawa yace.
“Rufe min baki wawuyar banza, ko dan irin zaman da Zaharadini yayi da ke ai be cancanci ki bishi da wani kalamin ba saboda son zuciya, da ace ke din kina da hankali da tunina ai da kin gane cewar abun da ya aikata be aikata laifi ba, saboda duk abun da ya aikata ya aikata ne saboda ke, amman ace mutum baya raye kina son a dole sai kin dora mashi laifi? Mahaifiyarshi bata gama warkewa daga zafin ciwon rashinshi yanzu kuma ki kara mata wani, ai ina tunanin ko wani ki ga yana zagin Zaharadini sai inda karfinki ya kare balle kuma har ace kin zage shi da gaske”
“Wallahi zuciyata bata tana raya min cewar da saninka Deen ya aikata abin da ya aikata ba”
“Ai da nasan ke ce da na hana shi, domin duk mutumen da zai zauna bayan idonka ya zage ka, to ba masoyinka ba ne, abun da aka ce mamaci idan ya bar duniya ba a fadin aibunsa idan ma yana da balle kuma ke da kika matarshi, Zaharadin be barawo ba ne, ba ya fashi da makami baya kashe mutane, kuma duk abun da ya aikata ya aikata ne saboda ke, kuma inda mutumci ko da be aikata abun da ya aikata ba idan ya ce yana sonki ya cancanci a bashi ko dan ni, wane irin gata ne Margayi be miki ba? Na tabbatar da ubanki na raye ba zai wuce aura miki Zahraddini ba”
Na mike tsaye zuciyata na bugawa da mugun karfi.
“Da ace Deen ya nemi soyayya ta ruwan sanyi ba zai yi laifi a gurina ba, amman ya aikata abun da be dace ba, kuma ya bar ni cikin duhun rashin sani, miyasa ba zai fada min gaskiya ba, a haka kuma baka ganin laifinsa, da ace ba Abiey ya aikatawa abun da ya aikata ba, wata kila da yanzu yana gidan Yari domin abun da ya aikata babban laifin ne da za a iya daureshi har na tsawon shekaru wata kila ma har karshen rayuwarshi”
Mama ta daka min tsawa ta nuna min ďaki.
“Zahra wuce ki shiga ďaki?”
“Wane ďaki? Ta gama cin mutunci ďana a gaban idona ta ci mutuncinshi a gaban mahaifiyarsa kuma ki ce ta wuce ta shiga ďaki, ta ci abincina ta kwana a muhallin? Ai yau kin nuna min budulci Zahra yau kin ba ni mamaki, Wallahi a lokacin da Hajiya ta fada min maganar nan na yi zaton zata fada min cewar kin tausaya masa, ashe kara da baya raye da yau ya ga bakinciki Allah ya waddaranki Zahra, shi ma wannan na tabbatar da ya aureki da yanzu yana nan yana nadama”
Ina bude baki na sake magana Mama ta sake daka min tsawa a karo na biyu.
“Na ce ki shiga daki ko?”
“Aa barta ta gama, ai daman rashin kunya ne ta iya har ta siyarwa”
Ba karamin jihadi na yi ba na hade maganar da ta taru a baki, domin na san idan na sake cewa tak sai Mama zata iya cewa zata doke ni, a tarihin rayuwarta ban san Mama ta yi sa'in sa da Baba ba, a iya tsawon rayuwar da na yi tare da ita ban san wata rana da ta taba mayar masa da magana ba, ban kuma san wata rana da ya bata umarni ta ki bi ba, tsantsan biyaya Mama ta yi masa, duk da ban san irin zamantakewar da ta yi da mahaifina ba, domin na taso ne ba tare da na taba ganinsa ko sau daya ba, mutumen da nake kira da uba a yanzu shi na sani a matsayin mahaifina. Hawayen da suka cika idona na share na nufi hanyar ďakin shi kuma ya juya ya fice kamar zai balla kafafuwansa ya tashi sama.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Mama ta furta ni dai ban juyo ba har na shige ďakin, tun da na shiga ban fito ba sai abincin dare ma Mama da kan ta shigo ta kawo min, har lokacin kuma bata ce min komai ba. Ana sauka daga sallah Magariba Baba ya shigo gidan ina jin Mama na sama sannu da zuwa ya amsa mata sama sama, ďaki ya fara zama kamin Mama ta yi masa shimfida a waje ya fito ya zauna kasancewar an dauke wutar nepa a lokacin. Ko da na fito na zagaya bandaki ina jin yana murda radio shi, da ada ne zan masa sannu da zuwa ya amsa, yanzu kuma ban ji ina iya mashi ba, be ma zama lallai idan na mashi ya amsa ba. Bayan na fi fitsari na dawo dakin na dauki carbi na hau katifar na kwanta na fara zikiri, sai kuma tunanin đana ya fado min a rai, ko a wane hali yake a yanzu Allah masa ni, wata kila yana can yana fama da ciwon cikin. Na girgiza kai ina kokarin ganin ban saka abun a raina ba, amman na kasa wani irin kaunarsa nake ji tana kara fisgata. Sosai nake son sanin halin da yake ciki tashi na yi na fita dakin zuwa gurin Mama dake zaune kan tabarma tare da Baba kamin na yi magana wayarta ta yi kara.
“Daman wayarki zan ce ki ara min”
“Gata can daki tana ringing”
Na juya ba tare da na ce masa komai ba, sai ya kira ni.
“Zahra yanzu idan mahaifinki ne zaki zo nan ki tsaya baki gaishe shi ba? Wato yanzu isa zaki fara nuna a cikin gidana ko? Ke kuma kina kallo baki ce mata komai ba”
Na juyo tun kamin Mama tace komai na ce.
“Baba barka da dare”
Ban jira ya amsa ba na sake juyawa na shiga dakin ina jin Mama ba ce mashi
“Yaran yanzu ka haife su ne ba ka haifi halinsu ba Malam”
Ni dai ban maida hankali a akan maganar da su ke ba kara inda wayar take na dauka ganin Mama Hanne ce ya saka na kawo ma Mama wayar da sauri na tsaya jiran ta gama wayar ta ara min na kira Dr Hamid na ji halin da ďana yake ciki. Sai ga yaro ya shigo da kuzarinsa.
“Sallamu Alaikum wai Abiey yace ana sallama da Zahra”
Mama dake waya ta dago ta kalleni nima kallonta na yi kamin na kalli yaron sai muka hada baki ni da Baba gurin furta kalmomi mabanbanta.
“Ka ce gata nan zu... ”
“Ka ce bata nan”
Na kalli Baba da sauri.
“Baba magana kawai zan yi da shi dan Allah”
“To ki tafi ki fada masa kar ya sake zuwa kofar gidan nan”
Mama ta sauke wayar da sauri ta kalleshi.
“Malam Aliyu ne fa dan Mai Martaba”
“Ko ďan Sarkin Saudiya ne be dame ni ba, kuma ba shi zaiba shi damar shiga cikin gidana yayi yadda yake so ba, bana son na gan shi kofar gidana, idan ya sake zuwa Zahra ta fita to ta fita kenan ba zata dawo min a gida ba”
“A dai yi hakuri a rika kai zuciya nesa, ban san iya abun da Hajiya ta fada maka da yasa ka hau da wannan zafin ba, amman yana da kyau idan ana sara a rika duba bakin gatari”
Mama ta fada tana kokarin saukar da shi akan hawan da yayi da yawa na fushi, sai ya taso mata kamar yana jiranta.