← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 127

Sashe 53

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fada jikin sanyi jiki har bana son kallon fuskar Mama saboda yadda damuwa ta cita har ta cinye.

“Be zama lallai shi ya aikata ba, domin Abiey yana da hankali da tunani, kuma lokacin da Deen yayi masa sharri ma be yi komai ba balle yanzu da yake ganin ya same ki”

Cewar Yaya Maryam sai Sa'adatu wato matar Kawu ta ce.

“Ko kuma fansa yake dauke? Kin san wasu mazan basa yafiya, wata kila duk kaunar da yake nuna miki a yanzu yana neman wanke kanshi ne da kuma son rama abun da kika mashi wasu mazan fa ba su da kyau”

Yaya Maryam ta girgiza kai.

“Da dai ace Zahra yar wani hamshakin mai kudi ce, ko kuma yar sarautar zan iya yarda da haka, amman idan har Abiey zai rama ba sai ya tsaya bata lokacin shi ba, kuma ban ga abun da aka yi mashi da zai ce sai ya rama, burin shi a kullum Zahra ta fahimce kuma ta fahimta, tsakani da Allah abun da Baba yake yi a yanzu ko ni nake da ikon da yake da shi abun da zan aikata kenan”

Mama ta ce.

“Tunaninku karami ne, komai Malam yayi muku yayi muku alherinsa fiye da haka, shi ya aurar da ku, kuma tun bayan mutuwar Babanku waya ke kula da mu idan ba shi ba? Ko da a munafurce yayi ni ya biya ni, yanzu ma saboda abun da Zahra ta yi ne akan Deen ya fusatashi da kuma wasu abubuwan da Hajiya ta fada masa, kuma da ace an bi abun ta siga mai kyau zamu iya daidaita komai amman wannan abun da Abiey yayi ya kara bata abin ne kawai, kuma idan mijinku ko masu neman auren Zahra suka wulakanta Malam kamar ni suka wulakanta saboda ni yake aure, kuma abokin mahaifinku ne, ya isa ya ce ayi ko ya hana”

Mama Sa'adatu tace.

“Ni fa abun da nake ganin yafi ki shirya ki tafi gidan Hajiyar ki bincika ko an dawo da shi”

“Wallahi nauyin zuwa nake ita kanta Hajiya ta dauki zafi a lokacin kamin Malam, yanzu kuma na san zata kara fusata ne ni ban san ma me zan ce musu a yanzu ba”

“Mama ko ki siyo sabuwar waya ki saka line ki?”

Na fada domin na matsu na ji daga bakin Abiey, muna saka da tattauna wanda zai je siyen wayar sai ga Kawu ya shigo, sai aka dawo da labari kasa a nan yake labarta mana cewar yaje gidan ya samu guri ya zama fili daga can kuma ya tafi gidan Hajiya ya samu Baba a can an dawo da shi daga chemist fuskarshi ko'ina a kumbure, ba karamin tashi hankalin Mama yayi ba lokacin da ta ji halin da Baba yake ciki sai ya tashi da sauri ita da Yaya Maryam da matar Kawu suka saka mayafai suka nufi gidan Hajiya domin duba Baba, ni kuma Kawu ya saka ni a gaba yayi ta yi min masifa kamar ni na umarci Abiey ya aikata abun da ya aikata, ni dai ban ce Uffan ba daman can na san ni za a dorawa laifi domin ta dalilina komai ya faru, Kawu sai kumfar baki yake har da fadar na hakura da Abiey domin ko an yi aure matsaloli za su yi ta biyo baya kuma zai zaman babu shiri ko ganin mutunci juna a tsakanin shi da Baba, wata kila ma Baba yace ba zan aureshi ba kuma idan ya fadi haka yana da hujja be kamata na musa mishi ba.

Ni dai kaina na kasa har ya ci ya shude ban ce eh ba balle aa, sai da ya fita sannan ya shiga bangaren surukarshi na ari wayarta na saka line Mama kamar jira ake ina sakawa kiran Hajiya Jamila ya shigo wayata mamaki ne ya kamani ta kira ta tabbatar da abun da yake faruwa a media ko kuma dai nata kiran na dabam ba, da fari kamar ba zan dauka ba, sai kuma wata zuciyar tace na daga na ji uzurinta.

“Hello”

“Hello Zahra ina wuni”

Ta amsa min ta dayan bangaren muryarta masa kasa har da wata uwar gaisuwa kamar ta Allah.

“Lafiya Kalau”

Na mayar mata ina jiran tace min na ga abun da yake ta yawo a media da gaske ne, sai na ji wata maganar ta dabam tsabanin abun da zuciyata take raya min.

“Zahra ke kadai kike? Magana nake son mu yi akan Amir”

Har an rada mashi suna kenan tun da har na ji tana mashi alkunya da Amir.

“Ina saurarenki”

“Ina son na zo na yi magana da ke face to face inda hali”

“Aa wayar ma ta isa ai, zamu iya yin magana”

“Da fari dai zan fara da baki hakuri akan abun da na yi miki Wallahi ba halina ba ne ban san abun da ya zo kaina ba, ban san abun da ya same ni ba a lokacin har na aikata abun da na aikata”

“Babu komai ya wuce, daman ance ido waye ka raina yace wanda nake gani kullum”

“Ba haka ba ne, Zahra taimakonki nake nema, na san kin taimaka min da farko, kuma na gode a yanzu ma ina kara neman taimakonki?”

“Ashe ina da rana da har Hajiya Jamila zata nemi taimakona ikon Allah”

“Dan Allah Zahra ki bar komai ya wuce mana, yaron nan Zahra ke ma naki ne idan kika taimaka ni da ke kamar mun ceci rayuwarshi ne”

“Ni ban gane abun da kike magana a kai ba”

“Zahra ki taimaka min dan Allah kar na rasa ďa na ki dawo gidan nan ki zauna zan ware miki ďaki daya ki rika kula da ďanki kina ba shi nono dan Allah”

Shiru na yi duk kuwa da irin tashin hankali da nake ji a tare da ni na fada min cewar ni da ita kamar mun ceto ďan mu ne hakan na nufin rayuwarshi tana cikin mawuyacin hali kenan?

“Ba ni da ni wani abu da zan yi iya yi ma ďanki a yanzu, na siyar kuma kin siya ya fita daga hakkina”

“Na sani amman duk da haka ina son ki cigaba rainonshi ne ki cigaba da ba shi nono dan Allah ki taimaka min Zahra, idan ma biyanki zan yi Wallahi zan iya”

“Sai na yi tunani akai kuma zan yi shawara da mahaifiyata”

“To na gode sai na jiki ki badi ko nawa saki shayar da shi zan biya ki”

Ban sake ce mata komai ba na yanke wayar. Hajiya Jamila da hawaye suka samu girbi a idonta ta saka hannunta ta share hawayen idonta tana wani sabon tashin hankali daya tunkaro ta a yanzu wanda ya saka ta neman mafita a gurin Zahra ido rufe, a ganinta idan ba ta yi haka asirin ta zai iya tonuwa, idan dan'uwanta ya bata hadin kai ba zama lallau sauran likitocin da bata sani ba su rufa mata asiri amman idan Zahra ta dawo ta cigaba da bawa yaron nono asirinta zai rufu. Tana dora hannun a ta fara murda key din kofar bathroom din ta fito ta ji kamar an taba kofar dakinta, da sauri ta karasa budewar ta fito ta nufi kofar gabanta na faduwa ta bude ta leka bata ga kowa ba, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo cikin dakin ta aikawa Dr Hamid kira, cikin matukar damuwa irin ta neman mafita take labarta mishi abun da ya faru.

ABIEY POV.

Tsakanin apartment din Anty Amarya da na Mai Martaba babu nisa ba musamman idan ka bi ta cikin falon ba kamar na sauran matanshi domin ya gina shi ne saboda Ammy a wacan lokacin kamin ya maye gurbinta da Anty Amarya. Tafiya ce da idan ka so sauri cikin dakiku ma zaka yi ta ka iso bangaren Anty ko na shiga bangaren Mai Martaba, amman a yau corridor yayi ma Abiey tsawo da ya dauke shi kusan minti talatin be iso part din Anty ba, idan ya cira kafa daga kamin ya daga yar uwarta wani yaki ne na duniya saboda tarin gumurzun dawakain tashin hankalin dake ranshi, idanuwanshi sun kada sun yi ja sai ka rantse da Allah baya iya gani da su, saboda yadda tashin hankali ya canja masa halitta a take. Bayan umarnin da Mai Martaba yayi mashi na rabuwa da Zahra, maganar karshe da mai Martaba yayi masa ta matukar daga mashi hankali daman ya dade zuciyarshi na raya mashi ba magani ne kadai abun da ya saka Mai Martaba ya tsare shi ba, me yake nufi da cewar Ammy ta bata mashi zuri'a? Daman ta taba tambayar Ammy ta nuna mashi bata son tambayar kuma ta fada mishi daga ita sai Zahra suka san dalili, ya san ba za a kalleshi ace ba Mai Martaba ne mahaifinshi ba, domin duk a cikin yayan Mai Martaba babu wanda ya fi biyo shi kamar Abiey. Idan zuciyarshi ta aika mashi tambaya sai ruhin dake can tare da Zahra ya jefo mashi ta shi tambayar ta ya zai rayu babu Zahra? Haka ya shigo cikin falon be ko san ya iso ba har sai da Anty ta dafa kafadarshi sai ya kalleta yana kokarin dawowa hayyacinshi.

“Abiey... Ka kwantar da hankalinka zN yi magana da Mai Martaba idan mun keba”

Ya kasa ce mata to ya kasa ce mata aa kuma ya kasa daga mata kai, kallonta kawai yake irin kallon dake nuna tunaninshi da hankalinshi ba akanta suke ba.

“Abiey....”

Ta sake girgiza shi sai ya kalleta a nan ma be ce komai ba ya nufi kofa, ita kima ta bishi da ido har ya fice, da sauri ya shiga motarshi yadda ya juya motar ma wani abun kallo ne domin wasa yake da rayuwarsa kamar an fada mashi bayan wannan ran akwai kyautar wasu da za a yi mashi, yadda yake gudu da mota kadai ya isar ya nuna yadda ba shi tsoron rasa rayuwarshi. Kamar zai tashi gidan haka ya rika danna horn masu bude gate din suka bude jiki na rawa, kamar mai gasar tsere haka ya faka motar ya fito ya nufi entrance din falon Ammy, yana murda kofar ya ji ta a rufe sai ya kwankwasa kuma ya danna door bell da mugun karfi.

“Aliyu...”
Chapter 53 · 0% Book details