Sashe 122
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama Lami ce zaune a gaban Mai Martaba yana kallon video da aka turowa Mai Martaba na wasu yan jarida gudu uku sai dai dayan cikin ruwan sanyi ya bada amsar wadanda suka saka shi, sauran kuwa sai da suka sha wahala sannan suka fadi cewar Rilwan ne ya fada musu komai kuma ya bada umarnin su je su dauki rahoton har ya hada musu da tukuicin kudi. Mama Lami dake rike da baki ta girgiza kai jikinta sai tsuma yake idonta sun yi kwayan irin na marasa gaskiya domin tonuwar asirin ďanta kamar nata ne, domin ita ta saka shi yin komai da saninta aka aikata.
“Wannan sheri ne kawai”
A take Hajiya Kilishi ta karba mata.
“Yauwa ni ma ai na fadi haka, domin mutane babu sherin da ba a iya ba ko dan a haka shi da Mai Martaba”
Anty Amarya ta tabe ki domin ta san borin kunya suke kuma bakinsu a hade yake.
“Wallahi wannan sheri ne aka yi masa Mai Martaba ka fahimci haka, akwai wanda ke son ya hada ka da shi ne, shi kanshi Abiey ai zai iya haka saboda kar sunansa ya bace shi kadai”
Mai Martaba ya mika hannu ya karbi wayarsa rai a bace.
“Na tara ku a nan na nuna muku wannan saboda na gargade ku, ku cire idonku da hannunku akan ďana, saboda ina fushi da shi, hakan ba yana nufin bana sonsa ba ne, kamin na nuna miki video ne saida na yi magana da Rilwanu kuma ya karbi laifinsa, kuma ya fada min gaskiyar abun da ya faru daman can na saka ran wannan abun a tsakaninku ya fito, domin idan ba nan ba babu ta inda labarin nan zai fita, Abiey ya fada min cewar ba shi ya rusa gidan nan ba, yanzu ma na kara yarda hakan domin Rilwan ya fada min cewar ke kika saka shi, kuma be kara min komai ba sai son Abiey da godiya ga Allah da ya ba ni ďa irin Abiey, ina son na ja kunnenku ne gaba dayanku kar na sake ji ko ganin wani abu makamancin wannan akan kowa balle kuma akan Abiey, inda hakan ta sake faruwa na bincika na gano gaskiya to zan dauki tsastsauran mataki akan haka”
“Amman Mai Martaba wannan ba adalci ba ne, daga mutane sun fadi sunan Rilwan sai ka dauka da gaske ne, kuma har ka tara mu kana mana irin wannan gargadi akan wani ďana kamar su sauran ba haihuwar ka yi ba?”
Cewar Hajiya Kilishi a kokarinta na tarewa yar'uwarta laifin da dukansu sun san gaskiya ne, har Rilwan dake zaune a can gefe sai gumi yake, ya kasa dago kai ya kalli kowa.
“Bana kwai sai da zakara, ba iya wannan abun suka fada ba, har shaida sai da suka nuna ta kudin da ya tura musu da kuma maganar da yayi da su, shi ma ai be amsa min laifinsa kai tsaye ba sai da ya ga hujojin da ba zai iya wanke kanshi da su ba, saboda haka ina gargadinku dukanku ku cire Idonku akan Abiey, ba shi kadai ba har da sauran yayana, idan wani abu ya sake faruwa ko wacce ku ta shiryawa zaman yayanta, domin zan iya zabar yayana akan matana, idan baku taimaka min na hada kan iyalina ba, be kamata a same hannunku a cikin ruguzasu ba”
A take Mama Lami ta saka kuka, Hajiya Kilishi na bata hakuri.
“Ki yi hakuri, wannan abun duk sherin makiya ne, shi kansa Rilwan din da wahala idan a hayyacinsa ya amsa cewar ya aikata wannan abun ,domin ba halinsa ba ne kuma babu yadda ba a iya ba, shiga tsakanin uba da ďa ko uwa da uba duk ana yi”
“Kilishi ki yi zaman yayanki, Zuwaira tashi ki koma bangarenki”
Mai Martaba ya fada cikin bacin ran musun da Hajiya Kilishi ke masa, gaba daya kamar bakar kaza yake ganinta a yau.
Anty Amarya ya rufe baki da sauri, jin Mai Martaba yayi furucin da bata taba sa ran zai iya ba ga matan da take ganin sune yan lelensa kuma yan gaban goshin da sai abun da suka fada ake yi. Wani irin zabura Hajiya Kilishi ta yi ta daki kirjinta.
“Ni kuma? Ni Mai Martaba? Daga bada hakuri sai abu ya dawo kaina, aa ba dai ni ba Wallahi, haba Mai Martaba ni miye nawa a ciki daga ba da hakuri, dan Allah ka yi hakuri, abun da ba ayi da kurciya ba yanzu bayan an yi yaya da jikoki za a ce a rabu ka dubi girman Allah ka yi hakuri”
Ta kai kasa tana kuka tana rikon kakafuwansa mikewa yayi tsaye yana kokarin shi na janye kafafuwan na sa yayi ma Anty Amarya alama da ta tashi ta tafi domin mamaki abun da ya faru ya saka ta manta da umarninsa.
“To Wallahi ba ki isa ba, Lami idan ma wani kullin ne kika shirya min to wutar ba zata ci ni kadai ba, daman ai kishiya ba yar'uwa ba ce, ba ki yin min da kurciya da zan iya aurowa ba sai yanzu da tsufa ya kama, wato ki zauna ki mulke gida yadda kike so?”
Lami ta fara yi mata alama da ido cewar ta yi shiru, amman ina son a yau Hajiya Kilishi bata sauraren maganar Lami saboda an yi mata abun da ba a taba ba, kuma akan abun da ba ita ta aikata ba.
“Ba zan yi shiru ba, ai babu kalar shirinki da ban sani ba, haka kika yi sai da kika fitar da Umaima a gidan nan, ke da bakinki kika fada min indai kina raye ita da duk zuri'arta ba za su taba samun muhalli a zucutyar Mai Martaba ba, shi ne a yau ni zaki dawo kaina? To Wallahi sai dai niyarki ta biki, kuma Wallahi ke kika saka aka rusa gidansu Zahra, saboda ki kulla masa sheri kika aika ďanki Rilwan ya saka yan Jarida su kitsa wannan abun saboda ki bata tsakanin ďa da uba”
Lami dake tsaye kamar karan dawa ta girgiza kai cikin kwarewa ta iya makirci na mata.
“Lallai kin hauka a yau Kilishi ni kike kullawa wannan sheri saboda abincinki ya kare a gidan nan? Kamar ni nace Mai Martaba ya sake ki? Ina kika kai hankali ne? Idan ma kishi ne ai an yi can da da kurciya amman yanzu girma ya kama an watsar da komai, kuma idan magana kike ta asiri ai tare muka aikata domin munduwa daya bata amo, har kara ni na yi na iya wanda mijina zai kauna ce ni ne, ke fa ke da bakinki kika fada min cewar Umaima har ta mutu ba zata sake aure ba, kin riga kin jefeta da mugun kullin, wannan haukar da kike ma amanarta ce ta kamaki Wallahi shiyasa kike fadar abun da kika aikata kina dangantasu da ni, amman ni ban san wannan sherin na ki a ina ya zamo asali ba”
Kilishi ta yi cikinta kamar za su daki juna sai ka rantse da Allah ba manya yaya ne da su ba.
“Karya kika yi, Wallahi ke kika shirya komai ai daman kin fada cewar babu macen da zata yi mulki bayan ke, Zuwaira ma da aka kawo daga bayan nan mallake kika yi kika saka mata tsoronki kin mallake kowa a gida, ni ma ai banza kika bar ni kuma Wallahi Allah ya isa”
Mai Martaba ya nade hannayensa baya yana kallon dramar da ake a gidansa, abun da be taba tsammanin faruwarsa ba, kuma be yi zaton da sa hannun matansa a lamarin Ammy ba. Anty Amarya ta mike tsaye idonta cike da kwalla na tausayin Ammy ta fice daga falon ba tare da tace komai ba tun da Mai Martaba ya tarasu har rikicin ya faru. Da gangan Hajiya Kilishi ke fadar abun da Mama Lami ta yi saboda Mai Martaba ya ji komai domin a tunanin Mama Lami ta shirya mata wani abun ne ta fitar da ita a gidan ta wargaza mata yaya, daman can ana zaune ne kawai amman babu aminci da yarda da juna, ko wace tana yi ma yar'uwarta asiri. Uffan Mai Martaba be sake cewa ba ya fara takawa cikin takun kasaita irin na manya sarakuna ba tare da ya san yana yi ba.
Dakinsa na bachi ya shiga sai da ya kai karshen dakin sannan ya daga kansa sama yana jin zuciyarsa babu dadi, be taba jin bakinciki rayuwa da Ammy ba irin yau, ya dade yana tambayar kansa dalilin kauracewa matarsa da yayi wanda hakan ya jefata ga halaka, i duk lokacin da zai waiga ya duba sai ya tarar babu wani laifi da ta yi masa kawai ya kasa zama da ita ne, har abun da ya faru ya saka shi sakinta.
ANTY AMARYA POV.
shiga bangarenta ke da wuya ta dauki wayarta ta kira Ammy, bugu daya ta yi Ammy ta amsa kiran.
“Assalamu Alaikum”
Amsa sallamar ma bata Anty bata samu yi ba, ta fara zayyana mata abun da ya faru cikin kuka.
“Ki gode, a yanzu komai ya zo karshe, kara ke an sake ki da kurciya ita kuma yanzu da tsufanta ya haramtawa kansa ita domin yace ta yi zaman yayanta kuma na tabbatar bakin ciki ba zai bari ta iya zama a cikin gidan nan ba”
“Wani abun a nesa yake na yarda, na sha wahala, na rayu a cikin bakinciki tun bayan fitowa a gidan nan, kuma Allah yayi musu yadda suke so sun raba auren kuma sun yi nasarar yin min aikin kar na auru, tabbas tun bayan fitowa ko kare be sake zuwa yace yana so na ba, amman hakan be dame ni ganin ina da Yaya sai na maida hankali gurin rainon yayana”
“Allah ya saka miki Ammy, Allah ya isar miki”
Ammy ta share hawayen da suke mata zuba mata ta ce.