Sashe 68
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Yasmin mutane irin mu ba sa rayuwa mai tsawo a duniya, idan har zamu rayuwa mai tsawo to So zai mutu, idan kuma so zai rayu to mu muke saurin mutuwa, ni kuma na tabbatar da so ba zai taba mutuwa a zuciyata ba, ina son na gyara komai before it too late, idan har zan ji kamar na yi hauka akan Ciwon son Zahra to ni na fi kowa cancantar na san yadda wasu suke ji akan So, Yasmin ba zan bari Ciwon so na ya cutar da ke ba, na yafe Zahra ko now amman ke ba zan yafe ki ba”
Ta sauke kanta kasa idonta na cika da hawaye, tausayinshi ta ke ji da kuma tausayin kanta a lokaci daya, shi ya rasa wanda yake so ita kuma ta san ba zai so ta kamar Zahra ba, kawai dai zai so ta ke saboda ya rasa Zahra kuma saboda kar ta shiga wani mugun hali a dalilinshi.
“Juya gefenki na dama kadan ki wata yarinya kyakkyawa mai kama da ke”
Ya fada domin ya lura da hawayen da suke sauko mata, ta dago ta juya a hankali dama da ita inda motarshi take ta kalla.
“Yi kasa da idonki kadan”
Ta yi masa da ido sai ta yi arba da kyakkyawar fuskarta a jikin bakin gilashin motar bata san lokaci da murmushi ya subuce mata ba.
“Kin fi kyau da murmushi ki daina kuka please”
Ta kalleshi ta kai hannu ta share hawayenta.
“Shiga ciki ki aje tray kuma ki gaishe da Momy sannan ki dauki permission ina son ki raka ni wani guri”
“Toh”
Ta amsa still tana murmushi, sannan ta duka ta dauki tray ta ya kauce mata ta wuce. Sai da ta shiga cikin falon sannan ya saka hannunshi aljihu ya ciro wayarshi ya kira Sauban.
“Ya jikin Zahra”
Shi ne abun da ya fara tambaya a lokacin da Sauban ya karba kiran.
“Sun ce ta ji sauki an sallame ta amman ban ganta ba”
“What do you”
“Na shigo asibiti amman ban ganta ba, sun ce likitan ya sallame ta kuma na je can unguwarsu ban same ta ba”
“Dole ne ka binciko inda take mana Sauban, ka sama mata muhallin ka rika kula da ita but make sure ka saka recording idan zaka je gurinta so that i can trust you more”
“Abiey kana son ka jefa ni a matsala Wallahi, ban san yadda zan yi ma na shiga jikin yarinyar nan har ta saba da ni ba”
“Always remember ba saboda kanka kake wannan ba saboda ni, and i know you're willing to do anything for me you can do this Sauban you can help your friend wannan kadai damar da na ke da ta wannan hanyar ne kawai zan iya samun cikar burina”
“Shikenan zan bincika inda take kuma zan yi duk abun da kake so”
“Thank You”
Ya kashe wayar ya dago yana kallon Yasmin da ta fito rike da yar karamar jakarta da wayarta, kara bude mata kofar gaban motar yayi ta shiga ta zauna ya rufe sannan shi kuma ya zagaya ya shiga yayi ma motar key. A gidan Dr Zainab suka fara zuwa sun dade a can ita kanta Dr ta yi mamakin ganinshi da yasmin musamman yadda ya sake kamar daman can yana son ta sosai ta zo ta kebe da shi ta yi magana amman bata samu dama ba domin be yarda ya tashi ya bar Yasmin ba a falon suka tsaya kuma be yarda ya tashi ya barta ba, a gidan suka yi sallah Isha'i sannan ya dauko ta ya dawo da ita gida, a daren ranar Yasmin ji ta yi kamar an biyata hajji domin ta kwana da farincikin da take ganin bata taba yin irin shi ba, ko da a munafunce Abiey ya nuna mata kauna ita dai ya biyata tun da har ya iya danne zuciyarshi ya bata kulawar da ta kamata, kuma tana da tabbacin daga haka zai kamu da tsananin kaunarta ba tare da ta sani ba.
Tun daga lokacin sai Abiey ya sabawa kanshi da kirata da safe ya ji ya ta tashi da rana ma su kan dade suna waya ko da bashi da abun fada mata zai ce ta ba shi labari idan kuma ya samu time zai dauke ta su fita ko kuma ya zo gidan su yi hira, duk abun da yake yi yana yi ne saboda ya sabawa zuciyarshi da ita kuma ya kori zama da ita kamin lokacin da zaman zai kama su domin ya san idan har ya ce zai koyi zama da ita bayan ta zama mata a gidanshi zai cutar da ita ne kuma ya cutar da kanshi, amman idan ya fara tun a waje zata san wa ta aura kuma ta koyi hakuri da zama da shi kamar yadda shi ma zai koyawa zuciyarshi hakurin zama da ita ba dan yana kaunarta.
A iya tsawon kwanakin da ya kwashe yana bawa Yasmin kulawa be taba jin zai iya mantawa da Zahra ba idan ya kare waya da Yasmin sai ya kira Sauban ya tambaye shi lafiyar Zahra wani lokacin kamin ya kira Yasmin sai ya fara kiran Sauban sai ya hada conference duk wata hira da Sauban zai yi da ita Abiey yana saurare. Ba tare da sanin Sauban ba Abiey ya dauki wayarshi ya saka wani code da zai rika yi ma shi forwarding duk kira shi da Sauban zai yi da Zahra, wani time din kuma shi zai turawa Sauban sakon da zai aikawa Zahra tun abun yana damun Sauban har ya fara sabawa. Tun daga lokacin kuma Abiey be sake tambayar Ammy ko neman sanin komai akan silar lalacewar alakarta da Mai Martaba ba ba dan baya bukatar sanin ba sai dai lura da yayi da halin da ta shiga a wacan lokaci da ta soma ba shi labarin wanda ya kai bata ma iya cin abincin ta koshi kuma tana kunyar hada ido da shi ta kasa sakewa ta koma kamar yadda take da shi a can da.
ZAHRA POV.
Ina shiga ďakin na samu Amir a kwance saman gadonta hannu na saka na dauke shi na zauna bakin gadon ina kallon fuskarshi sai wani irin kaunarshi ta kamani na ji kamar ace mallakina ne, kyakkyawa ne sosai kasancewar ni da ubanshi duk ba a baya ba gurin kyau da hasken fata. Hannu na kai na shafa fuskarshi a hankali sai ya motsa ya kalleni idonshi fari kal kamar madara, murmushi na yi na kai bakina na sunbanci goshinsa. Har na saka hannu na ciro nono na bashi sai kuma wata zuciya ta raya min idan akwai camera a dakin fa? Ai za a iya gani domin Dr Hamid ya fada min cewar na yi tsaka tsantsan akwai camera ko'ina a gidan, saurin dauke hannuna na yi ina tuna kalamin da mijin Jamila yayi min dazun cewar yana son wacece uwar ďanshi.
“To ko dai ya ga ina aikata wani abu ne?”
Na tambayi kaina kamin na samu mai ba ni amsa Hajiya Jamila ta shigo dakin ta rufe kofar da makulli.
“Kin ba shi nono?”
“Aa ina jin tsoro ban san ko akwai camera a ďakin ba kar mai gidanki ya gani”
“Babu camera a ďakuna sai dai a wajen gida da kuma ďakin yaron nan amman ďakina da ďakin mijina da falo duk babu camera”
Jin haka yasa na daga hijab dina na saka hannu ya ciro nono na saka mashi a baki, sai ya karba da sauri ya fara tsosa da karfi ya dade yana tsutsa sannan ruwan nonon ya kawo.
“Me Hubby ya tambaye ki?”
Ina tsaka da ba Amir nono ta yi min wannan tambayar, ba tare da na kalleta ba na amsa mata.
“Ya tambaye abun da ke damuna ne sai kuma yayi min ya jiki”
“Okay duk tambayar da zai miki ki san irin amsar da za ki ba shi karki yi subutar baki”
Na daga mata kai. Sai bayan sallah isha'i na fito daga bangarenta na shiga BQ ko da na shiga na samu su Mama sun jera komai sun gyara daki yayi kyau tare da taimakon masu aikin da Hajiya Jamila ta yi ma magana su kama musu gyaran haka ya taimaka abun yayi sauri. Sai tara mijin Yaya Maryam ya zo ya dauke ta bayan ya shigo cikin gidan ya duba gurin har ya saka mana albarka.
Misalin tara da rabi Hajiya Jamila ta aiko mana da abinci da na tabbatar hotel aka siyo shi domin be yi kama da abinci da aka girka ba ya fi yanayi da abincin siya. Na dan ci kadan Mama ba bata wani ci sosai ba domin ba son shimkafa take da dare ba, bayan mum gama zan kwashe kayan Mama tace na bari ta kwashe domin jikin nawa babu karfi sosai har lokaci, kwashe kayan ke da wuya muka ji sallamar Dr Hamid da sauri na tashi na dauki Hijab na saka Mama ta leka waje sai suka gaisa ina jin lokacin da yake tambayar Mama ni sai tace bari ta yi min magana.
“Tashi ki je Dr Hamid ne”
“Me zan ma shi?”
“Ya za'ayi na sani ni? Ki leka wata kila magana yake son yi da ke”
Cikin rashin jidadin zuwanshi na tashi na fita na taka inda yake tsaye yana wasa da keys din hannunshi na tsaya ba tare da na kalleshi ba.
“Zahra ya karfin jiki?”
“Alhamdulillah”
“Kin ci abinci?”
“Eh”
“Zan wuce gida ne na ce bari na sake biyowa na duba lafiyarki maybe ma ba ki sha maganinki ba”
Na yi murmushi domin kuwa yayi sara ne a kan gaba, ban sha maganin ba sam na manta da wani zancen shan magani ma Mama ma ina jin kamar ta manta bata tunatar da ni shan maganin ba, wata kila kuma tana jiran sai zan kwanta ne.
“Zan sha idan zan kwanta”
“Daman ai na sani saboda ba son magani kike ba, je ki dauko ki sha agabana”
Na yi wata yar siririyar dariya marar sauti.
“Zan sha Allah ka yarda”
Ya dade yana kallona da murmushi a fuskarshi sannan ya duba agogon hannunshi.